Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   C    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

27  GEN 1:27  Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su.
245  GEN 10:10  Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
1186  GEN 40:13  Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa.
1192  GEN 40:19  Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’ ”
1326  GEN 44:1  Yusuf kuwa ya ba wa mai yin masa hidima a gida, waɗannan umarnai cewa, Cika buhunan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin buhunsa.
2218  EXO 25:22  Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.
2744  EXO 40:36  Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul.
2993  LEV 10:15  Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da ’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
3000  LEV 11:2  “Ku ce wa Isra’ilawa,Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci.
3007  LEV 11:9   ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori.
3073  LEV 13:20  Firist zai bincike shi, in kuma ya zama ya fi fatar jiki zurfi kuma gashinsa ya juya ya zama fari, firist ɗin zai furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu a inda ƙurjin yake.
3959  NUM 8:19  Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da ’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.”
4989  DEU 3:12  Cikin ƙasar da muka kwasa a lokacin, na ba wa mutanen Ruben da mutanen Gad yankin arewa na Arower ta Kwarin Arnon, haɗe da rabin ƙasar tudu ta Gileyad, tare da biranenta.
5301  DEU 14:9  Cikin dukan halittun da suke cikin ruwa, za ku iya cin duk wani da yake da ƙege da ɓamɓaroki.
5709  DEU 29:27  Cikin zafin fushi da babbar hasala Ubangiji ya tumɓuke su daga ƙasarsu, ya watsar da su cikin wata ƙasa dabam, kamar yadda suke a yau.”
5775  DEU 32:15  Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri; cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul. Ya yashe Allahn da ya yi shi, ya ƙi Dutse Cetonsa.
5829  DEU 33:17  Cikin daraja yana yi kamar ɗan fari na bijimi; ƙahoninsa ƙahonin ɓauna ne. Tare da su zai tukwiyi al’ummai, har ma da waɗanda suke ƙarshen duniya. Haka dubu dubban Efraim suke; haka dubban Manasse suke.”
6561  JDG 2:14  Cikin fushinsa a kan Isra’ila Ubangiji ya ba da su ga hannun waɗanda suka kawo musu hari suka washe su. Ya sayar da su ga abokan gābansu da suke kewaye da su, waɗanda ba za su iya yin tsayayya da su ba.
6646  JDG 5:21  Kogin Kishon ya kwashe su, tsohon kogi, kogin Kishon. Ci gaba raina; ka ƙarfafa!
6781  JDG 9:25  Cikin hamayya da shi waɗannan ’yan ƙasar Shekem suka sa mutane a kan tuddai don su yi kwanton ɓauna a kan su yi fashi ga duk wanda ya wuce a can, wannan fa ya kai kunnen Abimelek.
6930  JDG 14:19  Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko masa da iko. Sai ya fita ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutanensu talatin, ya kwashe kayansu ya kuma ba da rigunarsu ga waɗanda suka bayyana kacici-kacicin. Cike da fushi, ya haura zuwa gidan mahaifinsa.
7072  JDG 20:16  Cikin dukan mayaƙan nan akwai zaɓaɓɓu mutane ɗari bakwai waɗanda su bahagwai ne, kowanne yana iya harbin gashin guda na kai da majajjawa ba kuskure.
7517  1SA 14:7  Mai ɗaukan makaman ya ce, “Ka yi duk abin da yake zuciyarka. Ci gaba, ina tare da kai gaba da baya.”
8652  2SA 22:47  “Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena! Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona!
8680  2SA 23:24  Cikin talatin ɗin kuwa akwai, Asahel, ɗan’uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,
9337  1KI 17:17  Ana nan sai ɗan matan, wato, gwauruwan nan ya fara ciwo. Ciwon ya ƙara muni, daga ƙarshe sai ya daina numfashi.
9454  1KI 20:43  Cike da fushi, sarkin Isra’ila ya tafi fadarsa a Samariya.
9463  1KI 21:9  Cikin waɗannan wasiƙu ta rubuta, “Ku yi shelar ranar azumi, ku zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane.
9783  2KI 9:23  Yoram ya juya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya,Cin amana, Ahaziya!”
10128  2KI 21:5  Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari.
10860  1CH 16:35  Ku yi kuka, ku ce, Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”
10992  1CH 23:4  Dawuda ya ce, Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai.
11153  1CH 28:5  Cikin dukan ’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila.
11244  2CH 3:10  Cikin Wuri Mafi Tsarki ya yi kerubobi biyu, ya kuma shafe su da zinariya.
11591  2CH 19:10  Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba.
11648  2CH 21:19  Cikin lokaci, a ƙarshen shekara ta biyu, sai hanjin cikinsa suka fito saboda cutar, ya kuma mutu cikin tsananin zafi. Mutanensa suka hura wuta don girmama shi, kamar yadda suka yi wa kakanninsa.
11674  2CH 23:13  Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!”
11791  2CH 28:22  Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji.
11880  2CH 31:21  Cikin kome da ya yi cikin hidimar haikalin Allah, cikin biyayya kuma ga doka da umarnai, ya nemi Allahnsa, ya kuma yi aiki gabagadi. Ta haka kuwa ya yi nasara.
11918  2CH 33:5  Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari.
11920  2CH 33:7  Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon,Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.
11925  2CH 33:12  Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.
12280  EZR 10:23  Cikin Lawiyawa, akwai Yozabad, Shimeyi, Kelaya (wato, Kelita), Fetahahiya, Yahuda, Eliyezer.
12355  NEH 3:23  Can gaba da su, Benyamin da Hasshub ne suka yi gyare-gyaren a gaban gidansu, biye da su kuwa, Azariya ɗan Ma’asehiya, ɗan Ananiya ne ya yi gyare-gyaren kusa da gidansa.
12421  NEH 6:15  Cikin kwana hamsin da biyu aka gama gina katangar, a ranar ashirin da biyar ga watan Elul.
12530  NEH 9:15  Cikin yunwansu ka ba su burodi daga sama, cikin ƙishirwansu kuma ka fitar musu ruwa daga dutse. Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka rantse ta wurin ɗaga hannu cewa za ka ba su.
12544  NEH 9:29  “Ka gargaɗe su su dawo ga dokarka, amma suka yi fariya, suka bijire wa umarnanka. Suka yi zunubi game da farillanka waɗanda ta wurinsu ne mutum zai rayu in ya yi biyayya da su. Cikin taurinkai suka juye bayansu daga gare ka, suka zama masu taurinkai, suka kuma ƙi su saurara.
12548  NEH 9:33  Cikin dukan abubuwan da suka faru da mu, ka kasance mai adalci; ka yi aminci, yayinda mu kuwa muka aikata mugu.
12895  JOB 1:22  Cikin wannan duka Ayuba bai yi wa Allah zunubi ta wurin ba shi laifi ba.
12947  JOB 4:13  Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan.
13456  JOB 24:16  Cikin duhu mutane suna fasa gidaje, amma da rana sukan kulle kansu; ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.
13513  JOB 28:5  Cikin ƙasa inda ake samun abinci, a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta;
13922  JOB 41:22  Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi, tana kabtar ƙasa in tana tafiya.
13975  PSA 4:5  Cikin fushinku kada ku yi zunubi; sa’ad da kuke kan gadajenku, ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela
14054  PSA 10:2  Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi, waɗanda yake kama cikin makircin da ya shirya.
14056  PSA 10:4  Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah.
14137  PSA 18:7  Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
14216  PSA 21:10  A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su.
14355  PSA 31:6  Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.
14370  PSA 31:21  Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su daga makircin mutane; a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya daga harsuna masu zagi.
14372  PSA 31:23  Cikin tsorona na ce, “An yanke ni daga gabanka!” Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai sa’ad da na kira gare ka don taimako.
14510  PSA 37:39  Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala.
14534  PSA 38:23  Zo da sauri ka taimake ni, Ya Ubangiji Mai Cetona.
14579  PSA 41:13  Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada.
14586  PSA 42:6  Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.
14592  PSA 42:12  Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.
14597  PSA 43:5  Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da Allahna.
14629  PSA 45:5  Cikin darajarka ka hau zuwa nasara a madadin gaskiya, tawali’u da adalci; bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki.
14639  PSA 45:15  Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka.
14674  PSA 48:10  Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.
14691  PSA 49:12  Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
14743  PSA 51:20  Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima.
14845  PSA 59:12  Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su.
14882  PSA 62:8  Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
14886  PSA 62:12  Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji,Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,
14916  PSA 65:6  Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa,
14972  PSA 68:20  Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. Sela
15160  PSA 77:10  Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sela
15252  PSA 79:9  Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka.
15284  PSA 81:8  Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. Sela
15338  PSA 85:5  Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
15398  PSA 89:8  Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro; shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi.
15611  PSA 102:24  Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina.
15662  PSA 104:24  Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka.
15817  PSA 108:8  Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki,Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.
15942  PSA 118:5  Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.
16121  PSA 119:155  Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka.
16951  PRO 17:8  Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara.
17121  PRO 23:7  gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka,Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai.
17412  ECC 2:9  Na ƙasaita fiye da kowane mutumin da ya riga ni zama a Urushalima. Cikin dukan wannan, hikimata ba tă rabu da ni ba.
17442  ECC 3:13  Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.
17699  SNG 7:3  Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye.
17860  ISA 7:8  gama kan Aram shi ne Damaskus, kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.
17898  ISA 8:21  Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu.
18053  ISA 16:14  Amma yanzu Ubangiji ya ce, Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta, ’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”
18063  ISA 17:10  Kun manta da Allah Mai Cetonku; ba ku tuna da Dutse, kagararku ba. Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,
18121  ISA 21:16  Ga abin da mai girma ya ce mini,Cikin shekara ɗaya, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, dukan sojojin Kedar za su zo ga ƙarshe.
18280  ISA 29:17  Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi kuma gona mai taƙi za tă zama kamar kurmi?
18302  ISA 30:15  Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa,Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake, cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku, amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.