13278 | JOB 17:14 | In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’ tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’ |
17881 | ISA 8:4 | Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.” |
18325 | ISA 31:5 | Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima; zai kāre ta ya kuma fanshe ta, zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.” |
19090 | JER 3:19 | “Ni kaina na faɗa, “ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza in ba ki ƙasa mai daɗi, gādo mafi kyau da wata al’umma.’ Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’ ba za ki ƙara rabuwa da bina ba. |
22190 | HOS 2:18 | “A waccan rana,” in ji Ubangiji, “za ki ce da ni ‘mijina’; ba za ki ƙara ce ni ‘maigidana’ ba. |
22354 | HOS 14:4 | Assuriya ba za su iya cece mu ba; ba za mu hau dawakan yaƙi ba. Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’ wa abin da hannuwanmu suka yi ba, gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.” |
22682 | MIC 3:5 | Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Game da annabawa masu ɓad da mutanena, in wani ya ciyar da su, sai su ce akwai ‘salama’ amma in bai ciyar da su ba, a shirye suke su kai masa hari. |
23997 | MAT 23:10 | Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi. |
26712 | JHN 13:13 | Kuna ce da ni ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake. |
30593 | 2PE 3:4 | Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.” |