23233 | MAT 1:20 | Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. |
23234 | MAT 1:21 | Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.” |
23236 | MAT 1:23 | “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.” |
23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
23246 | MAT 2:8 | Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” |
23251 | MAT 2:13 | Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.” |
23263 | MAT 3:2 | “Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa.” |
23264 | MAT 3:3 | Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.'' |
23268 | MAT 3:7 | Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa? |
23273 | MAT 3:12 | Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.” |
23275 | MAT 3:14 | Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?” |
23276 | MAT 3:15 | Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci.” Sai Yahaya ya yarje masa. |
23281 | MAT 4:3 | Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” |
23282 | MAT 4:4 | Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.''' |
23284 | MAT 4:6 | ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.''' |
23285 | MAT 4:7 | Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.''' |
23287 | MAT 4:9 | Ya ce masa, “Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada.'' |
23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' |
23293 | MAT 4:15 | “Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! |
23294 | MAT 4:16 | Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.” |
23295 | MAT 4:17 | Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.” |
23297 | MAT 4:19 | Yesu ya ce masu, “Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane.” |
23306 | MAT 5:3 | “Albarka ta tabbata ga masu talauci a ruhu, domin mulkin sama nasu ne. |
23341 | MAT 5:38 | Kun dai ji an ce, “Ido a maimakon ido, hakori kuma a maimakon hakori.' |
23366 | MAT 6:15 | In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku laifuffukanku ba.” |
23369 | MAT 6:18 | don kada mutane su gane kuna azumi, sai dai Ubanku da yake a asirce. Kuma Ubanku da ke ganin abinda ke a asirce, zai saka maku.” |
23370 | MAT 6:19 | “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke batawa, inda barayi kuma ke fasawa su yi sata. |
23385 | MAT 6:34 | “Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe za ta damu da kanta. Kowace rana ta na cike da wahalarta”. |
23416 | MAT 8:2 | Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.” |
23417 | MAT 8:3 | Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa. |
23420 | MAT 8:6 | Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai.” |
23421 | MAT 8:7 | Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.” |
23422 | MAT 8:8 | Sai hafsan, ya ce, “Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke. |
23423 | MAT 8:9 | Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,” |
23424 | MAT 8:10 | Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba. |
23426 | MAT 8:12 | Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.” |
23427 | MAT 8:13 | Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke. |
23431 | MAT 8:17 | Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.” |
23433 | MAT 8:19 | Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.” |
23434 | MAT 8:20 | Yesu ya ce masa, “Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta.” |
23435 | MAT 8:21 | Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.” |
23436 | MAT 8:22 | Amma Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne matattunsu.” |
23439 | MAT 8:25 | Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!” |
23440 | MAT 8:26 | Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. |
23441 | MAT 8:27 | Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”. |
23443 | MAT 8:29 | Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” |
23445 | MAT 8:31 | Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” |
23446 | MAT 8:32 | “Yesu ya ce masu, “To, ku je.” Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa. |
23476 | MAT 9:28 | Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?'' Sai suka ce masa. ''I, ya Ubangiji.'' |
23531 | MAT 11:3 | Ya ce masa. “Kai ne mai zuwa”? ko mu sa ido ga wani. |
23532 | MAT 11:4 | Yesu ya amsa ya ce masu, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da ku ka gani da abin da ku ka ji. |
23535 | MAT 11:7 | Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa? |
23546 | MAT 11:18 | Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, “Yana da aljannu”. |
23549 | MAT 11:21 | “Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka. |
23552 | MAT 11:24 | Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku.” |
23553 | MAT 11:25 | A wannan lokaci Yesu ya ce, “Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara. |
23558 | MAT 11:30 | Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi.” |
23560 | MAT 12:2 | Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. “Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci.” |
23561 | MAT 12:3 | Amma Yesu ya ce masu, “Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi? |
23566 | MAT 12:8 | Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.” |
23568 | MAT 12:10 | Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, “Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?” Domin su zarge shi a kan zunubi. |
23569 | MAT 12:11 | Yesu ya ce masu, “Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba? |
23570 | MAT 12:12 | Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci.” |
23571 | MAT 12:13 | Sai Yesu ya ce wa mutumin nan “Mika hannun ka.” Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa. |
23576 | MAT 12:18 | “Dubi, bawa na zababbe; kaunatacce na, wanda ya ke faranta mani raina sosai. Zan sa Ruhu na bisan sa, za ya furta hukunci zuwa al'ummai. |
23581 | MAT 12:23 | Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?” |
23582 | MAT 12:24 | Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, “Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.” |
23583 | MAT 12:25 | Amma Yesu ya san tunanin su, sai ya ce. “Duk mulkin da ya rabu gaba da kan sa, ba zaya tsaya ba, duk wani birni da ya rabu ba zai tsaya ba, ko gida da ya tsage, za ya rushe. |
23595 | MAT 12:37 | Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku.” |
23596 | MAT 12:38 | Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, “Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.” |
23597 | MAT 12:39 | Amma Yesu ya amsa ya ce masu, “Mugun zamani da mazinaciyar tsara, su na bukutar alama. Amma babu alamar da za a ba su, sai dai alamar annabi Yunusa. |
23605 | MAT 12:47 | Sai wani ya ce masa, “Duba, mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai”. |
23606 | MAT 12:48 | Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, “Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?” |
23607 | MAT 12:49 | Sai ya mika hannu ya nuna almajiransa ya ce, “Duba, ga mahaifiyata da 'yan'uwana! |
23608 | MAT 12:50 | Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.” |
23611 | MAT 13:3 | Sai Yesu ya fada masu abubuwa da yawa cikin misalai. Ya ce, “Wani mai shuka, ya tafi yayi shuka. |
23618 | MAT 13:10 | Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, “Don me ka ke yi wa taron magana da misali?” |
23619 | MAT 13:11 | Yesu ya amsa ya ce masu, “An baku 'yanci ku fahimci asiran mulkin sama, amma gare su ba a bayar ba. |
23622 | MAT 13:14 | A gare su ne annabcin Ishaya ya cika, wanda yake cewa, “Game da sauraro zaku saurara, amma ba za ku fahimta ba. Game da gani kuma za ku kalla, amma ba za ku gane ba. |
23631 | MAT 13:23 | Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin.” |
23632 | MAT 13:24 | Yesu ya sake ba su wani misali, yana cewa “Za a kwatanta mulkin sama da wani mutum wanda ya shuka iri mai kyau a gona. |
23636 | MAT 13:28 | Ya ce masu, “Magabci ne ya yi wannan”. Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?' |
23638 | MAT 13:30 | Bari dukan su su girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin, “Ku tuge ciyayin da farko a daura su dami dami sai a kona su, amma a tara alkamar a kai rumbunana.'” |
23639 | MAT 13:31 | Sai Yesu ya sake yin magana da su cikin misalai, yana cewa “Za a kwatanta mulkin sama da kwayar mustad, wanda wani mutum ya shuka a lambunsa. |
23640 | MAT 13:32 | Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa.” |
23641 | MAT 13:33 | Yesu ya sake fada masu wani misali. “Za a kwatanta mulkin sama da yisti da mace takan dauka ta kwaba gari da shi mudu uku har sai ya yi kumburi.” |
23643 | MAT 13:35 | Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, “Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya.” |
23644 | MAT 13:36 | Sai Yesu ya bar taron ya shiga cikin gida. Amajiransa suka zo wurin sa suka ce, “Ka fasarta mana misalan nan a kan ciyayin da ke gonar” |
23645 | MAT 13:37 | Yesu ya amsa kuma ya ce, “Shi wanda ya shuka iri mai kyau Dan Mutum ne. |
23659 | MAT 13:51 | Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, “I”. |
23660 | MAT 13:52 | Sai Yesu ya ce masu, “Saboda haka kowane malamin attaura da ya zama almajirin mulkin sama, yana kamar mutum mai gida wanda ya zaro tsoho da sobon abu daga taskarsa.” |
23662 | MAT 13:54 | Sai Yesu ya shiga yankinsa ya koyar da mutane a masujadarsu. Saboda haka suka yi mamaki suna cewa, “Daga ina wannan mutumin ya sami hikimarsa da al'ajibai? |
23665 | MAT 13:57 | Suka bata rai saboda shi. Amma Yesu ya ce masu, “Ai annabi bai rasa daraja sai dai ko a garinsa da kuma cikin iyalinsa. |
23668 | MAT 14:2 | Ya ce wa barorinsa, “Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa”. |
23670 | MAT 14:4 | Ya ce masa, “Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba.” |
23674 | MAT 14:8 | Bayan ta amshi umurni daga wurin mahaifiyarta, ta ce, “Ka bani kan Yahaya mai baptisma a kan tire. |
23681 | MAT 14:15 | Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, “Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci.” |
23682 | MAT 14:16 | Amma Yesu ya ce masu, “Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci.” |
23683 | MAT 14:17 | Suka ce masa, “Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai.” |
23684 | MAT 14:18 | Yesu ya ce, “Ku kawo mani su.” |
23692 | MAT 14:26 | Da almajiran suka ganshi yana tafiya akan tekun, sai suka firgita suna cewa, “Fatalwa ce,” suka yi kururuwa cikin tsoro. |
23693 | MAT 14:27 | Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.” |
23694 | MAT 14:28 | Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.” |
23695 | MAT 14:29 | Yesu yace, “Zo” Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu. |
23696 | MAT 14:30 | Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!” |
23697 | MAT 14:31 | Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?” |
23699 | MAT 14:33 | Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.” |
23704 | MAT 15:2 | “Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.” |
23705 | MAT 15:3 | Yesu ya amsa masu ya ce, “Kuma don me ku ke karya dokar Allah saboda al'adunku? |
23707 | MAT 15:5 | Amma kun ce, “Duk wanda ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, “Kowanne taimako da za ka samu daga gare ni yanzu baiko ne ga Allah,'” |
23710 | MAT 15:8 | “ Wadannan mutane girmama ni da baki kawai suke yi, amma zukatansu nesa suke da ni. |
23711 | MAT 15:9 | Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu.” |
23712 | MAT 15:10 | Sai ya kira taron mutane zuwa gare shi ya ce masu, “Ku saurara ku fahimta, |
23713 | MAT 15:11 | ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum.” |
23714 | MAT 15:12 | Sai al'majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?” |
23715 | MAT 15:13 | Yesu ya amsa ya ce, “Kowace shuka wadda ba Ubana na sama ya shuka ba za a tuge ta. |
23716 | MAT 15:14 | Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami.” |
23717 | MAT 15:15 | Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ka bayyana wannan misali a garemu,” |
23718 | MAT 15:16 | Yesu ya ce, “Ku ma har yanzu ba ku da fahimta? |
23722 | MAT 15:20 | Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum.” |
23724 | MAT 15:22 | Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.” |
23725 | MAT 15:23 | Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, “Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu.” |
23726 | MAT 15:24 | Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila.” |
23727 | MAT 15:25 | Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, “Ubangiji ka taimake ni.” |
23728 | MAT 15:26 | Ya amsa ya ce, “Ba daidai bane a dauki gurasar yara a jefa wa kananan karnuka. |
23729 | MAT 15:27 | Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.” |
23730 | MAT 15:28 | Sai Yesu ya amsa ya ce mata, “Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.”'Yarta ta warke a lokacin. |
23734 | MAT 15:32 | Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.” |
23735 | MAT 15:33 | Almajiran suka ce masa, “A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan.” |
23736 | MAT 15:34 | Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.” |
23743 | MAT 16:2 | Amma ya amsa ya ce masu, “Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,' |
23745 | MAT 16:4 | Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa.” Daga nan sai Yesu ya tafi. |
23747 | MAT 16:6 | Yesu ya ce masu, “Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa.” |
23748 | MAT 16:7 | Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, “Ko saboda bamu kawo gurasa bane.” |
23749 | MAT 16:8 | Yesu yana sane da wannan sai ya ce, “Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane? |
23752 | MAT 16:11 | Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.” |
23754 | MAT 16:13 | A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, “Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake? |
23755 | MAT 16:14 | Suka ce, “Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.” |
23756 | MAT 16:15 | Ya ce masu, “Amma ku wa kuke ce da ni?” |
23757 | MAT 16:16 | Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai.” |
23758 | MAT 16:17 | Yesu ya amsa ya ce masa, “Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama. |
23760 | MAT 16:19 | Zan ba ka mabudan mulkin sama. Duk abin da ka kulla a duniya zai zama abin da an kulla a cikin sama, kuma duk abinda ka warware a duniya a warware yake cikin sama,” |
23763 | MAT 16:22 | Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.” |
23764 | MAT 16:23 | Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.” |
23765 | MAT 16:24 | Sa'annan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk wanda yake so ya bi ni, lallai ne ya ki kansa, ya dauki gicciyensa, ya bi ni. |
23769 | MAT 16:28 | Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa.” |
23773 | MAT 17:4 | Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.” |
23774 | MAT 17:5 | Sa'adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, “Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi.” |
23776 | MAT 17:7 | Sai Yesu ya zo ya taba su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” |
23778 | MAT 17:9 | Yayin da suke saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su, ya ce, “Kada ku fadawa kowa wannan wahayin, sai Dan Mutum ya tashi daga matattu.” |
23779 | MAT 17:10 | Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, “Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?” |
23780 | MAT 17:11 | Yesu ya amsa ya ce, “Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa. |
23784 | MAT 17:15 | “Ubangiji, ka ji tausayin yarona, domin yana da farfadiya, kuma yana shan wuya kwarai, domin sau da yawa yana fadawa cikin wuta ko ruwa. |
23785 | MAT 17:16 | Na kawo shi wurin almajiran ka, amma ba su iya su warkar da shi ba.” |
23786 | MAT 17:17 | Yesu ya amsa ya ce, “Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.” |
23788 | MAT 17:19 | Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce, “Me ya sa muka kasa fitar da shi?” |
23789 | MAT 17:20 | Yesu ya ce masu, “Saboda karancin bangaskiyarku. Domin hakika, ina gaya maku, in kuna da bangaskiya ko da kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan dutse, 'Matsa daga nan ka koma can,' zai kuwa matsa kuma ba abin da zai gagare ku. |
23791 | MAT 17:22 | Suna zaune a Galili, Yesu ya ce wa almajiransa, “Za a bada Dan Mutum ga hannun mutane. |
23792 | MAT 17:23 | Kuma za su kashe shi, a rana ta uku zai tashi.” Sai almajiransa suka yi bakin ciki kwarai. |
23793 | MAT 17:24 | Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?” |
23794 | MAT 17:25 | Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?” |
23795 | MAT 17:26 | Sai Bitrus ya ce, “Daga wurin baki,” Yesu ya ce masa, “Wato an dauke wa talakawansu biya kenan. |
23822 | MAT 18:26 | Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, “Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba.” |
23836 | MAT 19:5 | Shi wanda ya yi su kuma ya ce, “Saboda wannan dalilin, mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya hade da matarsa, su biyun su zama jiki daya?” |
23879 | MAT 20:18 | “Ku duba fa, zamu tafi Urushalima, kuma za a bada Dan Mutum ga manyan firistoci da marubuta. Za su kuma yanke masa hukuncin kisa, |
23897 | MAT 21:2 | yace masu, “Ku shiga kauyen da yake gaban ku zaku iske wata jaka da aholaki tara da ita. Ku kwance su ku kawo mani su. |
23898 | MAT 21:3 | Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan.” |
23900 | MAT 21:5 | “Ku cewa diyar Sihiyona, duba, ga sarkinki na zuwa wurin ki, mai tawali'u ne, kuma akan jaki wanda aholaki ne.” |
23904 | MAT 21:9 | Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, “Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!” |
23905 | MAT 21:10 | Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, “Wanene wannan?” |
23906 | MAT 21:11 | Sai jama'a suka amsa, “Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili.” |
23908 | MAT 21:13 | Ya ce masu, “A rubuce yake, 'Za a kira gidana gidan addu'a,' amma kun mayar dashi kogon 'yan fashi.” |
23910 | MAT 21:15 | Amma da manyan firistoci da malaman attaura suka ga abubuwan banmamaki da yayi, kuma sa'adda suka ji yara suna tada murya a cikin haikalin suna cewa, “Hossana ga dan Dauda,” sai suka ji haushi. |
23911 | MAT 21:16 | Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?'' Yesu ya ce masu, “I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?” |
23914 | MAT 21:19 | Da ya ga bishiyar baure a bakin hanya, sai yaje wurin amma bai sami kome ba sai dai ganye. Sai ya ce mata, “Kada ki kara yin 'ya'ya har abada.” Sai nan take bishiyar bauren ta bushe. |
23915 | MAT 21:20 | Da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suka ce, “Kaka bishiyar bauren ta bushe nan da nan?” |
23916 | MAT 21:21 | Yesu ya amsa yace masu, “Hakika ina ce maku, in dai kuna da bangaskiya ba ku yi shakka ba, ba abinda aka yi wa bauren nan kadai za kuyi ba har ma za ku cewa tsaunin nan, “Ka ciru ka fada teku,' sai kuwa haka ta kasance. |
23917 | MAT 21:22 | Kome kuka roka cikin addu'a, in dai kun gaskanta, za ku samu.” |
23918 | MAT 21:23 | Sa'adda Yesu ya shiga haikalin, sai manyan fristocin da shugabannin jama'a suka zo suka same shi yayin da yake koyarwa, suka ce, “Da wane iko kake yin wadannan abubuwa?” |
23919 | MAT 21:24 | Yesu ya amsa yace masu, “Ni ma zan yi maku tambaya daya. In kun fada mani, ni ma zan fada maku ko da wane iko nake yin wadannan abubuwa. |
23920 | MAT 21:25 | Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?” Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, “In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?' |
23921 | MAT 21:26 | Amma in munce, ' daga mutune,' muna tsoron jama'a, saboda sun san Yahaya annabi ne.” |
23922 | MAT 21:27 | Sai suka amsa ma Yesu suka ce, ''Bamu sani ba.” Shi ma yace masu, “Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba. |
23926 | MAT 21:31 | Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?” Suka ce, “na farkon.” Yesu ya ce masu, “Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku. |
23936 | MAT 21:41 | Suka ce masa, “Zai hallaka mugayen manoman nan ta hanya mai tsanani, zai kuma bada gonar haya ga wadansu manoman, mutanen da za su biya, lokacin da inabin ya nuna.” |
23937 | MAT 21:42 | Yesu yace masu, “Baku taba karantawa a nassi ba,'' 'Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani. Wannan daga Ubangijine, kuma abin mamaki ne a idanunmu?' |
23939 | MAT 21:44 | Duk wanda ya fadi akan dutsen nan zai ragargaje. Amma duk wanda dutsen ya fadawa, zai nike.” |
23943 | MAT 22:2 | “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya wa dansa liyafar aure. |
23945 | MAT 22:4 | Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, “Ku gaya wa wadanda aka gayyata, “Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren.” |
23955 | MAT 22:14 | Gama mutane dayawa aka kira, amma kadan aka zaba.”' |
23957 | MAT 22:16 | Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, “Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane. |
23958 | MAT 22:17 | To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?” |
23959 | MAT 22:18 | Amma Yesu ya gane muguntarsu yace, “Don me kuke gwada ni, ku munafukai? |
23960 | MAT 22:19 | Ku nuna mani sulen harajin.” Sai suka kawo masa sulen. |
23961 | MAT 22:20 | Yesu yace masu, “Hoto da sunan wanene wadannan?” |
23962 | MAT 22:21 | Suka ce masa, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce masu, “To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.” |
23965 | MAT 22:24 | cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. |
23969 | MAT 22:28 | To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta.” |
23970 | MAT 22:29 | Amma Yesu ya amsa yace masu, “Kun bata, domin ba ku san litattafai ko ikon Allah ba. |
23973 | MAT 22:32 | 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.” |