23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' |
23293 | MAT 4:15 | “Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! |
23325 | MAT 5:22 | Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. |
23374 | MAT 6:23 | Amma in idonka na da lahani, dukan jiki na cike da duhu. Saboda haka, in hasken da yake cikinka duhu ne, ina misalin yawan duhun! |
23390 | MAT 7:5 | Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka. |
23408 | MAT 7:23 | Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!' |
23427 | MAT 8:13 | Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke. |
23439 | MAT 8:25 | Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!” |
23481 | MAT 9:33 | Bayan da an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, su ka ce, ''Kai, ba a taba ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba!'' |
23511 | MAT 10:25 | Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa! |
23547 | MAT 11:19 | Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita. |
23549 | MAT 11:21 | “Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka. |
23570 | MAT 12:12 | Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci.” |
23607 | MAT 12:49 | Sai ya mika hannu ya nuna almajiransa ya ce, “Duba, ga mahaifiyata da 'yan'uwana! |
23693 | MAT 14:27 | Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.” |
23696 | MAT 14:30 | Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!” |
23764 | MAT 16:23 | Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.” |
23803 | MAT 18:7 | Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo! |
23904 | MAT 21:9 | Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, “Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!” |
23911 | MAT 21:16 | Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?'' Yesu ya ce masu, “I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?” |
24000 | MAT 23:13 | Amma kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kun toshewa mutane kofar mulkin sama. Baku shiga ba, kuma ba ku bar wadanda suke so su sami shiga ba. |
24002 | MAT 23:15 | Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kuna tafiya ketaren tekuna da kasashe domin samun almajiri daya tak, in kwa kun samu kukan mai da shi biyunku danwuta. |
24004 | MAT 23:17 | Ku wawayen makafi! wanene yafi girma, zinariyar ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar? |
24006 | MAT 23:19 | Ku makafi! Wanene yafi girma, baikon ko kuwa bagadin da yake kebe baikon ga Allah? |
24010 | MAT 23:23 | Kaiton ku Farisawa da marubuta, munafukai! Kukan fitar da zakkar doddoya, da karkashi, da lamsur, amma kun yar da al'amuran attaura mafi nauyi-, wato, hukunci, da jinkai da bangaskiya. Wadannan ne ya kamata kuyi, ba tare da kunyi watsi da sauran ba. |
24011 | MAT 23:24 | Makafin jagora, ku kan burtsar da kwaro dan mitsil, amma kukan hadiye rakumi! |
24012 | MAT 23:25 | Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! kuna wanke bayan moda da kwano, amma aciki cike suke da zalunci da keta. |
24013 | MAT 23:26 | Kai makahon Bafarise! Sai ka fara tsarkake cikin modar da kwanon domin bayansu ma su tsarkaka. |
24014 | MAT 23:27 | Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar kasa kuke, masu kyaun gani daga waje, daga ciki kuwa sai kasusuwan matattu da kazanta iri iri. |
24016 | MAT 23:29 | Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Ku kan gina kaburburan annabawa, kuna kuma kawata kaburburan adalai. |
24019 | MAT 23:32 | Sai kuma kuka cika ma'aunin ubanninku! |
24024 | MAT 23:37 | Urushalima, Urushalima, keda kika kashe annabawa kika kuma jejjefi wadanda aka turo maki da duwatsu! Sau nawa ne naso in tattaro ki kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fukafukanta, amma kin ki. |
24025 | MAT 23:38 | Ga shi an bar maku gidan ku a yashe! |
24045 | MAT 24:19 | Amma kaito ga wadanda suke dauke da yaro, ko masu shayarwa a wannan kwanakin! |
24049 | MAT 24:23 | Sa'annan idan wani yace maku, duba, “ga Almasihu a nan!” ko, “ga Almasihu a can!” kar ku gaskata. |
24083 | MAT 25:6 | Amma da tsakkar dare sai aka yi shela, 'Ga ango ya iso! Ku fito taryensa. |
24098 | MAT 25:21 | Maigidansa yace masa, 'Madalla, bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abu kadan. Zan sa ka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.' |
24100 | MAT 25:23 | Ubangidansa yace masa, 'Madalla, kai bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abubuwa kadan. Zan saka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.' |
24147 | MAT 26:24 | Dan mutum zai tafi, kamar yadda aka rubuta akan sa. Amma kaiton mutumin da ta wurin sa za'a bada Dan mutum! Gwamma da ba'a haifi mutumin nan ba.” |
24172 | MAT 26:49 | Nan da nan ya kaiga Yesu ya ce, “Gaisuwa, Mallam!” sai ya sumbace shi. |
24188 | MAT 26:65 | Sai babban firist din ya yayyaga rigarsa, yana cewa, “Yayi sabo! don me ku ke neman wata shaida kuma? Duba, yanzu kun ji sabon. |
24227 | MAT 27:29 | Sai suka yi masa rawanin kaya suka sa a kansa, suka kuma bashi sanda a hannunsa na dama. Suka rusuna a gabansa suna masa ba'a, suna cewa, “Ranka ya dade, Sarkin Yahudawa!” |
24238 | MAT 27:40 | suna kuma cewa, “Kai da kace zaka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, ka ceci kanka mana! In dai kai Dan Allah ne, ka sauko daga gicciyen!” |
24311 | MRK 1:27 | Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!” |
24336 | MRK 2:7 | Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi “sai Allah kadai?” |
24391 | MRK 3:34 | Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, “Ga uwa-ta da yan-uwana anan! |
24395 | MRK 4:3 | “ku saurara! wani mai shuka ya tafi shuka. |
24415 | MRK 4:23 | Bari mai kunnen ji, ya ji!'' |
24431 | MRK 4:39 | Sai ya farka, ya tsawata wa Iskar. Ya kuma ce wa ruwan tekun, “Ka natsu! ka yi shiru!” Sai Iskar ta kwanta, wurin duk ya yi shiru. |
24526 | MRK 6:50 | gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, “Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!'' |
24566 | MRK 7:34 | Ya dubi sama, ya ja numfashi ya ce masa, “Ifatha”, wato, “bude!” |
24680 | MRK 10:23 | Yesu ya dubi almajiransa ya ce. ''Yana da wuya masu arziki su shiga mulkin Allah!'' |
24705 | MRK 10:48 | Mutane da yawa suka kwabe shi, cewa yayi shiru. Sai ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, Ya Dan Dauda ka yi mani jinkai, ka ji tausayina!” |
24706 | MRK 10:49 | Yesu ya tsaya ya ce, ku kirawo shi. Su kuwa suka kirawo makahon suka ce masa. ''Albishrinka, ta so! Yana kiranka.'' |
24718 | MRK 11:9 | Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji. |
24719 | MRK 11:10 | Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na Ubanmu Dawuda! Dukaka a cikin sama!” |
24723 | MRK 11:14 | Sai ya ce wa bauren, “Kada kowa ya kara cin ''ya'yanka har abada!” Almajiransa kuwa sun ji maganar. |
24730 | MRK 11:21 | Bitrus kuwa ya tuna ya ce “Malam, dubi! Baurenan da ka la'anta ya bushe.” |
24787 | MRK 13:1 | da Yesu ke fita daga Haikalin, sai daya daga cikin almajirnsa ya ce masa “malam, dubi kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan!” |
24807 | MRK 13:21 | To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata. |
24823 | MRK 13:37 | Abinda na gaya maku, ina gaya wa kowa, shine ku zauna a fadake!” |
24844 | MRK 14:21 | Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! “zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba”. |
24864 | MRK 14:41 | Ya sake komowa karo na uku yace masu “har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi”. |
24868 | MRK 14:45 | Da isowarsa kuwa, sai ya zo wurin Yesu ya ce “Ya malam!”. Sai ya sumbace shi. |
24887 | MRK 14:64 | Kun dai ji sabon da yayi! Me kuka gani? Duk suka yanke masa hukunci akan ya cancanci kisa. |
24908 | MRK 15:13 | sai suka amsa da kuwwa” a “giciye shi!” |
24913 | MRK 15:18 | Suna masa kirari na ba'a suna cewa, “A gaida sarkin Yahudawa!” |
24924 | MRK 15:29 | suke wucewa suna zaginsa suna kada kai suna cewa, “Aha! kai da zaka rushe haikali ka kuma gina shi cikin kwana uku, |
24925 | MRK 15:30 | ka ceci kanka mana, ka sauka daga giciye!” |
24948 | MRK 16:6 | Sai ya ce masu, “Kada ku ji tsoro. Kuna neman Yesu banazare, wanda aka giciye. Ya tashi! Baya nan. Ku duba wurin da aka kwantar dashi. |
24990 | LUK 1:28 | Ya zo wurin ta ya ce, “A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke. |
25053 | LUK 2:11 | Yau an haifi maku mai ceto a cikin birnin Dauda! Shine Almasihu Ubangiji! |
25098 | LUK 3:4 | Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, “Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa! |
25166 | LUK 4:34 | “Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!” |
25167 | LUK 4:35 | Yesu ya tsauta wa aljanin yana cewa, “Yi shiru ka fita daga cikinsa!” Da aljanin ya jefar da mutumin kasa a tsakiyarsu, ya fita daga cikinsa ba tare da yi masa rauni ba. |
25173 | LUK 4:41 | Aljanu kuma sun fita daga wadasunsu da dama, suna kuka cewa, “Kai ne Dan Allah!” Yesu ya tsauta wa aljannun ya kuma hana su magana, domin sun sani cewa shine Almasihu. |
25239 | LUK 6:24 | Amma kaitonku mawadata! Domin kun rigaya kun samu ta'aziyar ku. |
25240 | LUK 6:25 | Kaitonku kosassu a yanzu! Domin za ku ji yunwa nan gaba. Kaitonku masu dariya yanzu! Domin za ku yi makoki kuna kuka nan gaba. |
25241 | LUK 6:26 | Kaiton ku idan kowadanne mutane suna yabon ku! Domin haka kakannin-kakanninsu suka yi wa annabawan karya. |
25257 | LUK 6:42 | Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka. |
25298 | LUK 7:34 | Dan Mutum, ya zo, yana ci, yana sha, amma, kuka ki shi, kuna cewa dubi mutum mai hadama, mai shan ruwan inabi da yawa, abokin masu karbar haraji da masu zunubi! |
25304 | LUK 7:40 | Yesu ya amsa ya ce masa, “Siman, ina so in gaya maka wani abu.” Ya ce, “malam sai ka fadi!” |
25338 | LUK 8:24 | Sai almajiran Yesu su ka zo su ka tashe shi daga barci. Suka ce da shi, “Ya Shugaba! Ya Shugaba! Za mu mutu!” Sai ya tashi ya umarci iskar, sai iskar mai hauka da tumbatsar ruwan sun tsaya tsit. |
25342 | LUK 8:28 | Sa'adda ya ga Yesu, mutumin ya yi ihu da karfi, ya rusuna a gabansa da babban murya ya ce, “Me zan yi da kai, Yesu, Dan Allah Madaukaki? Ina rokonka, kada ka ba ni azaba!” |
25348 | LUK 8:34 | Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen. |
25352 | LUK 8:38 | Mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa, ya roki Yesu cewa, “Ka barni in tafi tare da kai!” Amma Yesu ya sallame shi cewa, |
25366 | LUK 8:52 | Dukan mutane a wurin, suna ta kuka da karfi saboda sun damu da yarinyar ta mutu. Amma Yesu ya ce da su, “Ku dena kuka! Ba mutuwa ta yi ba! Barci ta ke yi kawai!” |
25368 | LUK 8:54 | Amma ya kama hannun ta yayi kira cewa, “Yarinya, na ce ki tashi!” |
25387 | LUK 9:17 | Dukansu suka ci kowa ya koshi. Daga nan almajiran suka tattara sauran abin da ya rage, har kwanduna goma sha biyu suka cika! |
25410 | LUK 9:40 | Na roki almajiran ka su umurci mugun ruhun ya fita daga cikinsa, amma ba su iya ba!” |
25443 | LUK 10:11 | 'Ko kurar birninku da ta like a kafafunmu, mun karkabe maku ita a matsayin shaida a kanku! Amma ku sani mulkin Allah ya zo kusa da ku.' |
25445 | LUK 10:13 | Kaiton ki, Korasinu! Kaiton ki, Baitsaida! Ayyuka masu girma da aka yi a cikinku, da an yi su a cikin Taya da Sidon, da sun tuba tuntuni a zaune cikin toka da tufafin makoki. |
25488 | LUK 11:14 | Wani lokaci, Yesu yana fitar da wani beben aljani. Sa'adda aljanin ya fita, sai mutumin da yake bebe ya yi magana. Sai taron mutanen suka yi mamaki! |
25520 | LUK 11:46 | Sai Yesu ya ce, “Kaitonku malaman shari'a! Gama kun dora wa mutane kaya mai nauyi wanda ya fi karfinsu dauka. Amma ku, ko da dan yatsa ba ku taba kayan ba. |
25552 | LUK 12:24 | Ku dubi hankaki wadanda ba sa yin shuka, ba sa yin girbi. Ba su da rumbuna ko dakunan ajjiya, amma Allah ya na ciyar da su. Ku fa kun fi tsuntsaye daraja! |
25556 | LUK 12:28 | Idan Allah ya sa wa ciyawa tufafi masu kyau haka, wadda yau tana nan, gobe kuma a sa ta a wuta, ta yaya zai kasa sa maku tufafi, ku masu kankantar bangaskiya! |
25578 | LUK 12:50 | Amma ni, ina da baftisma wadda za a yi mani baftisma da ita, kuma na kagara, da an riga an yi ta! |
25596 | LUK 13:9 | In yayi 'ya'ya shekara mai zuwa to, amma in bai yi 'ya'ya ba sai a sare shi!”' |
25602 | LUK 13:15 | Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe kowannenku ba ya kwance Jakinsa ko Sa daga turkensa ya kai shi banruwa ran Asabaci? |
25614 | LUK 13:27 | Amma zai amsa ya ce, “Ina gaya maku, ban san ko daga ina ku ka fito ba, ku tafi daga wurina, dukanku masu aikata mugunta!' |