23240 | MAT 2:2 | ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.'' |
23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
23268 | MAT 3:7 | Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa? |
23275 | MAT 3:14 | Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?” |
23316 | MAT 5:13 | Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane. |
23349 | MAT 5:46 | Domin idan kuna kaunar wadanda suke kaunarku, wanne lada kuka samu? Ba haka masu karban haraji ma suke yi ba? |
23350 | MAT 5:47 | Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba? |
23376 | MAT 6:25 | Saboda haka ina gaya maku, kada ku damu a kan rayuwarku, game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha- ko kuwa jikinku, abin da za ku yi tufafi da shi. Ashe rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? |
23377 | MAT 6:26 | Ku dubi tsuntsayen da ke sararin sama. Ai, ba su shuka, balle girbi, ba su kuma tarawa a cikin rumbuna, amma Ubanku na Sama na ciyar da su. Ashe, ba ku fi su martaba ba? |
23378 | MAT 6:27 | Kuma wanene a cikinku, don damuwarsa, zai iya kara ko taki ga tsawon rayuwarsa? |
23379 | MAT 6:28 | To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi furannin jeji, yadda suke girma. Ba su aiki, kuma ba su sakar kaya. |
23381 | MAT 6:30 | Idan Allah yayi wa ciyawar jeji ado, wadda yau tana wanzuwa, gobe kuwa a jefa ta cikin murhu, ina misalin adon da za ya yi maku, ya ku masu karancin bangaskiya? |
23382 | MAT 6:31 | Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?' |
23388 | MAT 7:3 | Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba? |
23389 | MAT 7:4 | Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon? |
23394 | MAT 7:9 | Ko, kuwa wane mutum ne a cikin ku, dan sa zai roke shi gurasa, ya ba shi dutse? |
23395 | MAT 7:10 | Ko kuwa in ya roke shi kifi, zai ba shi maciji? |
23396 | MAT 7:11 | Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa? |
23401 | MAT 7:16 | Za ku gane su ta irin ''ya'yansu. Mutane na cirar inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya? |
23407 | MAT 7:22 | A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?' |
23418 | MAT 8:4 | Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu? |
23440 | MAT 8:26 | Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. |
23441 | MAT 8:27 | Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”. |
23443 | MAT 8:29 | Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” |
23452 | MAT 9:4 | Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, yace, ''Don me kuke mugun tunani a zuciyarku? |
23453 | MAT 9:5 | Wanne ya fi sauki, a ce, 'An gafarta maka zunubanka,' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya'? |
23459 | MAT 9:11 | Da Farisawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, ''Don me malamin ku ya ke ci tare da masu karbar haraji da masu zunubi?'' |
23462 | MAT 9:14 | Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, ''Don me mu da Farisawa mu kan yi azumi a kai a kai, amma naka almajiran ba su yi?'' |
23463 | MAT 9:15 | Sai Yesu ya ce masu, ''Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi.'' |
23476 | MAT 9:28 | Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?'' Sai suka ce masa. ''I, ya Ubangiji.'' |
23515 | MAT 10:29 | Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba. |
23531 | MAT 11:3 | Ya ce masa. “Kai ne mai zuwa”? ko mu sa ido ga wani. |
23535 | MAT 11:7 | Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa? |
23536 | MAT 11:8 | Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna. |
23537 | MAT 11:9 | Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi. |
23544 | MAT 11:16 | Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna |
23551 | MAT 11:23 | Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu. |
23561 | MAT 12:3 | Amma Yesu ya ce masu, “Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi? |
23562 | MAT 12:4 | Yadda ya shiga gidan Allah, ya ci gurasar alfarwa da doka ta hana shi ko mazan da ke tare da shi su ci, sai dai Firistoci ne kawai doka ta basu damar ci? |
23563 | MAT 12:5 | Sa'annan ba ku karanta cikin shari'a cewa, a ranar Asabaci, Firistoci da ke cikin haikali na sabawa ranar Asabaci, amma kamar ba su yi laifi ba? |
23568 | MAT 12:10 | Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, “Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?” Domin su zarge shi a kan zunubi. |
23569 | MAT 12:11 | Yesu ya ce masu, “Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba? |
23581 | MAT 12:23 | Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?” |
23584 | MAT 12:26 | Idan Shaidan ya fitar da Shaidan, ya rabu gaba da kansa. Yaya mulkin sa za ya tsaya? |
23585 | MAT 12:27 | Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku. |
23587 | MAT 12:29 | Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa. |
23592 | MAT 12:34 | Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana. |
23606 | MAT 12:48 | Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, “Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?” |
23618 | MAT 13:10 | Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, “Don me ka ke yi wa taron magana da misali?” |
23635 | MAT 13:27 | Bayin mai gonar kuwa suka zo suka ce masa, maigida, ashe ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? ya ya aka yi ta kasance da ciyayi? |
23636 | MAT 13:28 | Ya ce masu, “Magabci ne ya yi wannan”. Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?' |
23659 | MAT 13:51 | Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, “I”. |
23662 | MAT 13:54 | Sai Yesu ya shiga yankinsa ya koyar da mutane a masujadarsu. Saboda haka suka yi mamaki suna cewa, “Daga ina wannan mutumin ya sami hikimarsa da al'ajibai? |
23663 | MAT 13:55 | Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba? |
23664 | MAT 13:56 | Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa? |
23697 | MAT 14:31 | Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?” |
23704 | MAT 15:2 | “Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.” |
23705 | MAT 15:3 | Yesu ya amsa masu ya ce, “Kuma don me ku ke karya dokar Allah saboda al'adunku? |
23714 | MAT 15:12 | Sai al'majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?” |
23718 | MAT 15:16 | Yesu ya ce, “Ku ma har yanzu ba ku da fahimta? |
23719 | MAT 15:17 | Ko baku gani ba duk abin da ke shiga baki zuwa ciki ta haka yake fita zuwa salga? |
23736 | MAT 15:34 | Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.” |
23749 | MAT 16:8 | Yesu yana sane da wannan sai ya ce, “Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane? |
23750 | MAT 16:9 | Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba? |
23751 | MAT 16:10 | Ko gurasa bakwai ga mutum dubu hudu, da kuma kwanduna nawa kuka dauka ba? |
23752 | MAT 16:11 | Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.” |
23754 | MAT 16:13 | A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, “Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake? |
23756 | MAT 16:15 | Ya ce masu, “Amma ku wa kuke ce da ni?” |
23767 | MAT 16:26 | Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa? |
23779 | MAT 17:10 | Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, “Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?” |
23786 | MAT 17:17 | Yesu ya amsa ya ce, “Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.” |
23788 | MAT 17:19 | Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce, “Me ya sa muka kasa fitar da shi?” |
23793 | MAT 17:24 | Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?” |
23794 | MAT 17:25 | Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?” |
23797 | MAT 18:1 | Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Wanene mafi girma a mulkin sama?'' |
23808 | MAT 18:12 | Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba? |
23817 | MAT 18:21 | Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?'' |
23829 | MAT 18:33 | Ashe, bai kamata kaima ka nuna jinkai ga dan'uwanka bara kamar yadda na nuna maka jinkai ba?' |
23834 | MAT 19:3 | Farisawa suka zo wurinsa, suna gwada shi, suka ce masa, ''Ya hallata bisa ga doka mutum ya saki matarsa don kowanne dalili?'' |
23835 | MAT 19:4 | Yesu ya amsa ya ce, ''Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace? |
23836 | MAT 19:5 | Shi wanda ya yi su kuma ya ce, “Saboda wannan dalilin, mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya hade da matarsa, su biyun su zama jiki daya?” |
23838 | MAT 19:7 | Sai suka ce masa, ''To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?'' |
23847 | MAT 19:16 | Sai wani mutum ya zo wurin Yesu, ya ce, ''Malam, wanne ayyuka nagari ne zan yi domin in sami rai madawwami?'' |
23848 | MAT 19:17 | Yesu ya ce masa, ''Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin.'' |
23849 | MAT 19:18 | Mutumin ya ce masa, ''Wadanne dokokin?'' Yesu ya ce masa, ''Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur, |
23851 | MAT 19:20 | Saurayin nan ya ce masa, ''Ai na kiyaye duk wadannan. Me nake bukata kuma?'' |
23856 | MAT 19:25 | Da almajiran sun ji haka, suka yi mamaki kwarai da gaske, suka ce, ''Wanene zai sami ceto?'' |
23858 | MAT 19:27 | Sai Bitrus ya amsa ya ce masa, ''Duba, mun bar kome da kome mun bi ka. To me za mu samu?'' |
23867 | MAT 20:6 | Ya kuma sake yin haka a sa'a ta sha daya, da ya fita sai ya ga wasu a tsaye da ba sa yin kome. Sai ya ce masu, 'Me yasa kuke tsaye ba ku yin kome dukan yini?' |
23874 | MAT 20:13 | Amma mai gonar ya amsa wa daya daga cikin su, ya ce, 'Aboki na, ban yi maku laifi ba. Ai mun shirya zan biya ku yadda ake biya a yini, ko ba haka ba? |
23876 | MAT 20:15 | Ashe, ba daidai bane a gare ni, in yi abin da na ga dama da mallaka ta? Ko kishi ne kuke yi saboda kirki na?' |
23882 | MAT 20:21 | Yesu ya ce mata, Me kike so in yi maki?'' Sai ta ce masa, ''Ina so ka ba 'ya'yana izinin zama a mulkinka, daya a hannun damanka, daya kuma a hannun hagunka. |
23883 | MAT 20:22 | Amma Yesu ya amsa, ya ce, ''Baku san abin da kuke roko ba. Ko zaku iya sha daga cikin kokon da zan sha bada dadewa ba?'' Sai suka ce masa, ''Zamu iya.'' |
23893 | MAT 20:32 | Sai Yesu ya tsaya cik, ya sa aka kira su, sai ya ce masu, ''Me kuke so in yi maku?'' |
23905 | MAT 21:10 | Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, “Wanene wannan?” |
23911 | MAT 21:16 | Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?'' Yesu ya ce masu, “I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?” |
23915 | MAT 21:20 | Da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suka ce, “Kaka bishiyar bauren ta bushe nan da nan?” |
23918 | MAT 21:23 | Sa'adda Yesu ya shiga haikalin, sai manyan fristocin da shugabannin jama'a suka zo suka same shi yayin da yake koyarwa, suka ce, “Da wane iko kake yin wadannan abubuwa?” |
23920 | MAT 21:25 | Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?” Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, “In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?' |
23923 | MAT 21:28 | Amma me kuke tunani? Wani mutum yana da 'ya'ya biyu. Ya je wurin na farkon yace, 'Da, je ka kayi aiki yau a cikin gona.' |