Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   ”    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23234  MAT 1:21  Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.
23236  MAT 1:23  “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel-ma'ana, “Allah tare da mu.
23242  MAT 2:4  Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?
23246  MAT 2:8  Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.
23251  MAT 2:13  Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.
23263  MAT 3:2  “Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa.
23273  MAT 3:12  Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.
23275  MAT 3:14  Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?
23276  MAT 3:15  Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci. Sai Yahaya ya yarje masa.
23281  MAT 4:3  Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.
23294  MAT 4:16  Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.
23295  MAT 4:17  Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.
23297  MAT 4:19  Yesu ya ce masu, “Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane.
23366  MAT 6:15  In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku laifuffukanku ba.
23369  MAT 6:18  don kada mutane su gane kuna azumi, sai dai Ubanku da yake a asirce. Kuma Ubanku da ke ganin abinda ke a asirce, zai saka maku.
23385  MAT 6:34  “Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe za ta damu da kanta. Kowace rana ta na cike da wahalarta.
23416  MAT 8:2  Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.
23417  MAT 8:3  Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka. Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa.
23420  MAT 8:6  Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai.
23421  MAT 8:7  Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.
23423  MAT 8:9  Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,
23426  MAT 8:12  Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.
23427  MAT 8:13  Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi, A daidai wannan sa'a bawansa ya warke.
23431  MAT 8:17  Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.
23433  MAT 8:19  Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.
23434  MAT 8:20  Yesu ya ce masa, “Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta.
23435  MAT 8:21  Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.
23436  MAT 8:22  Amma Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne matattunsu.
23439  MAT 8:25  Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!
23440  MAT 8:26  Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya? Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit.
23441  MAT 8:27  Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?.
23443  MAT 8:29  Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?
23445  MAT 8:31  Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.
23446  MAT 8:32  “Yesu ya ce masu, “To, ku je. Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa.
23531  MAT 11:3  Ya ce masa. “Kai ne mai zuwa? ko mu sa ido ga wani.
23546  MAT 11:18  Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, “Yana da aljannu.
23552  MAT 11:24  Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku.
23558  MAT 11:30  Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi.
23560  MAT 12:2  Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. “Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci.
23566  MAT 12:8  Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.
23568  MAT 12:10  Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, “Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci? Domin su zarge shi a kan zunubi.
23570  MAT 12:12  Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci.
23571  MAT 12:13  Sai Yesu ya ce wa mutumin nan “Mika hannun ka. Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa.
23581  MAT 12:23  Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?
23582  MAT 12:24  Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, “Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.
23595  MAT 12:37  Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku.
23596  MAT 12:38  Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, “Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.
23605  MAT 12:47  Sai wani ya ce masa, “Duba, mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.
23606  MAT 12:48  Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, “Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?
23608  MAT 12:50  Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.
23618  MAT 13:10  Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, “Don me ka ke yi wa taron magana da misali?
23631  MAT 13:23  Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin.
23636  MAT 13:28  Ya ce masu, “Magabci ne ya yi wannan. Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?'
23638  MAT 13:30  Bari dukan su su girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin, “Ku tuge ciyayin da farko a daura su dami dami sai a kona su, amma a tara alkamar a kai rumbunana.'
23640  MAT 13:32  Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa.
23641  MAT 13:33  Yesu ya sake fada masu wani misali. “Za a kwatanta mulkin sama da yisti da mace takan dauka ta kwaba gari da shi mudu uku har sai ya yi kumburi.
23643  MAT 13:35  Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, “Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya.
23644  MAT 13:36  Sai Yesu ya bar taron ya shiga cikin gida. Amajiransa suka zo wurin sa suka ce, “Ka fasarta mana misalan nan a kan ciyayin da ke gonar
23659  MAT 13:51  Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, “I.
23660  MAT 13:52  Sai Yesu ya ce masu, “Saboda haka kowane malamin attaura da ya zama almajirin mulkin sama, yana kamar mutum mai gida wanda ya zaro tsoho da sobon abu daga taskarsa.
23668  MAT 14:2  Ya ce wa barorinsa, “Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa.
23670  MAT 14:4  Ya ce masa, “Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba.
23681  MAT 14:15  Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, “Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci.
23682  MAT 14:16  Amma Yesu ya ce masu, “Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci.
23683  MAT 14:17  Suka ce masa, “Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai.
23684  MAT 14:18  Yesu ya ce, “Ku kawo mani su.
23692  MAT 14:26  Da almajiran suka ganshi yana tafiya akan tekun, sai suka firgita suna cewa, “Fatalwa ce, suka yi kururuwa cikin tsoro.
23693  MAT 14:27  Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.
23694  MAT 14:28  Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.
23695  MAT 14:29  Yesu yace, “Zo Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu.
23696  MAT 14:30  Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!
23697  MAT 14:31  Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?
23699  MAT 14:33  Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.
23704  MAT 15:2  “Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.
23707  MAT 15:5  Amma kun ce, “Duk wanda ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, “Kowanne taimako da za ka samu daga gare ni yanzu baiko ne ga Allah,'
23711  MAT 15:9  Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu.
23713  MAT 15:11  ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum.
23714  MAT 15:12  Sai al'majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?
23716  MAT 15:14  Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami.
23717  MAT 15:15  Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ka bayyana wannan misali a garemu,
23722  MAT 15:20  Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum.
23724  MAT 15:22  Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce, Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.
23725  MAT 15:23  Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, “Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu.
23726  MAT 15:24  Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila.
23727  MAT 15:25  Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, “Ubangiji ka taimake ni.
23729  MAT 15:27  Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.
23730  MAT 15:28  Sai Yesu ya amsa ya ce mata, “Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.'Yarta ta warke a lokacin.
23734  MAT 15:32  Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.
23735  MAT 15:33  Almajiran suka ce masa, “A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan.
23736  MAT 15:34  Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita? Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.
23745  MAT 16:4  Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa. Daga nan sai Yesu ya tafi.
23747  MAT 16:6  Yesu ya ce masu, “Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa.
23748  MAT 16:7  Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, “Ko saboda bamu kawo gurasa bane.
23752  MAT 16:11  Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.
23755  MAT 16:14  Suka ce, “Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.
23756  MAT 16:15  Ya ce masu, “Amma ku wa kuke ce da ni?
23757  MAT 16:16  Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai.
23760  MAT 16:19  Zan ba ka mabudan mulkin sama. Duk abin da ka kulla a duniya zai zama abin da an kulla a cikin sama, kuma duk abinda ka warware a duniya a warware yake cikin sama,
23763  MAT 16:22  Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.
23764  MAT 16:23  Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.