23216 | MAT 1:3 | Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram. |
23222 | MAT 1:9 | Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya. |
23223 | MAT 1:10 | Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya. |
23239 | MAT 2:1 | Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, |
23241 | MAT 2:3 | Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu kwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima. |
23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
23245 | MAT 2:7 | Sai Hirudus ya kira masanan a asirce ya tambaye su aininhin lokacin da tauraron ya bayyana. |
23250 | MAT 2:12 | Allah kuma ya gargade su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma kasarsu ta wata hanya dabam. |
23251 | MAT 2:13 | Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.” |
23253 | MAT 2:15 | Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.'' |
23254 | MAT 2:16 | Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan. |
23257 | MAT 2:19 | Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce, |
23260 | MAT 2:22 | Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili |
23367 | MAT 6:16 | Haka kuma, in za ku yi azumi, kada ku zama da fuska kamar masu makoki yadda munafukai ke yi, domin sukan yankwane fuskokinsu, domin su bayyana ga mutane kamar suna azumi. Gaskiya, ina gaya maku, sun sami ladansu ke nan. |
23402 | MAT 7:17 | Haka kowanne itace mai kyau yakan haifi kyawawan 'ya'ya, amma mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. |
23489 | MAT 10:3 | Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus; |
23501 | MAT 10:15 | Hakika, ina gaya maku, a ranar shari'a za a fi rangwanta wa kasar Saduma da ta Gwamrata a kan wannan birni. |
23509 | MAT 10:23 | In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo. |
23536 | MAT 11:8 | Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna. |
23537 | MAT 11:9 | Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi. |
23603 | MAT 12:45 | Sai ya koma ya kawo wadansu ruhohi guda bakwai, wadanda su ka fi shi mugunta, sa'annan dukan su su zo su zauna a nan. Sa'annan yanayin mutumin nan na karshe ya fi na farko muni. Haka zaya kasance ga wannan mugun zamani. |
23625 | MAT 13:17 | Hakika ina gaya muku, annabawa da mutane dayawa masu aldalci sun yi marmarin ganin abin da kuka gani, amma ba su sami ganin su ba. Sun yi marmarin jin abin da kuka ji, ba su kuwa ji su ba. |
23653 | MAT 13:45 | Haka ma za a kwatanta mulkin sama da wani attajiri mai neman Lu'ulu'ai masu daraja. |
23655 | MAT 13:47 | Haka kuma, za a kwatanta mulkin sama da taru da aka jefa cikin teku, ya kuwa tara hallitu iri-iri. |
23657 | MAT 13:49 | Haka zai kasance a karshen duniya. Mala'iku za su zo su ware miyagu daga cikin masu adalci. |
23667 | MAT 14:1 | A lokacin nan ne, Hiridus mai mulki ya ji labarin Yesu. |
23669 | MAT 14:3 | Domin Hiridus ya kama Yahaya, ya daure shi, kuma ya jefa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar dan'uwansa Filibus. |
23671 | MAT 14:5 | Da Hirudus ya kashe shi, amma yana tsoron jama'a, domin sun dauke shi a matsayin annabi. |
23672 | MAT 14:6 | Amma da ranar bikin haihuwar Hirudus ta kewayo, diyar Hirudiya tayi rawa a lokacin har ta burge Hirudus. |
23699 | MAT 14:33 | Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.” |
23780 | MAT 17:11 | Yesu ya amsa ya ce, “Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa. |
23786 | MAT 17:17 | Yesu ya amsa ya ce, “Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.” |
23799 | MAT 18:3 | ya ce, ''Hakika ina gaya maku, idan baku juya kun zama kamar kananan yara ba, babu yadda zaku shiga mulkin sama. |
23810 | MAT 18:14 | Hakanan fa, ba nufin Ubanku dake sama ba ne da ya daga cikin wadannan kananan ya hallaka. |
23814 | MAT 18:18 | Hakika ina gaya maku, duk abin da kuka daure a duniya, a daure yake a sama. Abin da kuka kwance kuma, a kwance yake a sama. |
23817 | MAT 18:21 | Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?'' |
23831 | MAT 18:35 | Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan'uwansa daga zuciya ba.'' |
23854 | MAT 19:23 | Yesu ya ce wa almajiransa, ''Hakika ina gaya maku, zai zama da wuya mai arziki ya shiga mulkin sama. |
23859 | MAT 19:28 | Yesu ya ce masu, ''Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'anta kabilu goma sha biyu na Isra'ila. |
23877 | MAT 20:16 | Haka yake, na karshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na karshe.'' [An kira dayawa, amma kadan ne zababbu]. |
23904 | MAT 21:9 | Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, “Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!” |
23910 | MAT 21:15 | Amma da manyan firistoci da malaman attaura suka ga abubuwan banmamaki da yayi, kuma sa'adda suka ji yara suna tada murya a cikin haikalin suna cewa, “Hossana ga dan Dauda,” sai suka ji haushi. |
23916 | MAT 21:21 | Yesu ya amsa yace masu, “Hakika ina ce maku, in dai kuna da bangaskiya ba ku yi shakka ba, ba abinda aka yi wa bauren nan kadai za kuyi ba har ma za ku cewa tsaunin nan, “Ka ciru ka fada teku,' sai kuwa haka ta kasance. |
23926 | MAT 21:31 | Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?” Suka ce, “na farkon.” Yesu ya ce masu, “Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku. |
23957 | MAT 22:16 | Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, “Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane. |
23961 | MAT 22:20 | Yesu yace masu, “Hoto da sunan wanene wadannan?” |
24003 | MAT 23:16 | Kaiton ku, makafin jagora, kuda kuke cewa, Kowa ya rantse da Haikali, ba komai. Amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, rantsuwarsa ta daure shi.' |
24004 | MAT 23:17 | Ku wawayen makafi! wanene yafi girma, zinariyar ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar? |
24008 | MAT 23:21 | Kuma duk wanda ya rantse da Haikali ya rantse dashi da kuma wanda yake cikin sa. |
24015 | MAT 23:28 | Haka nan kuke a idanun mutane ku adalai ne, amma a ciki sai munafunci da mugun aiki. |
24022 | MAT 23:35 | Sakamakon hakan alhakin jinin dukkan adalai da aka zubar a duniya ya komo a kan ku, tun daga jinin Habila adali har ya zuwa na Zakariya dan Barakiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikali da bagadi. |
24023 | MAT 23:36 | Hakika, Ina gaya maku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani. |
24059 | MAT 24:33 | Haka kuma, idan kun ga dukkan wadannan abubuwa, ya kamata ku sani, Ya yi kusa, ya na bakin kofa. |
24094 | MAT 25:17 | Haka ma wanda ya karbi talanti biyu ya sami ribar wasu biyu. |
24117 | MAT 25:40 | Sa'annan Sarkin zai amsa masu yace, 'Hakika Ina gaya maku, duk abinda kuka yi wa daya mafi kakanta daga cikin 'yan'uwana a nan ni kuka yi wa.' |
24136 | MAT 26:13 | Hakika Ina gaya maku, duk inda za ayi wannan bishara a dukan duniya, abin da matar nan tayi za'a rika ambatar da shi don tunawa da ita.” |
24144 | MAT 26:21 | Sa'adda suke ci, yace, “Hakika ina gaya maku, daya daga cikin ku zai bada ni.” |
24157 | MAT 26:34 | Yesu yace masa, ''Hakika ina gaya maka, a wannan daren kafin carar zakara, za ka yi musun sani na sau uku.” |
24168 | MAT 26:45 | Sai Yesu ya koma wurin almajiran yace masu, “Har yanzu barci kuke kuna hutawa? Duba, lokaci ya kusato, kuma an bada Dan mutum ga hannun masu zunubi. |
24196 | MAT 26:73 | Bayan dan lokaci kadan wadanda suke a tsaye suka zo wurin Bitrus suka ce masa, “Hakika kai daya daga cikin su ne, gama harshen ka ya tonaka.” |
24209 | MAT 27:11 | Sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamna ya kuma tambaye shi, “Kai sarkin Yahudawa ne?” Yesu ya amsa, “Haka ka fada.” |
24242 | MAT 27:44 | Hakan nan ma 'yanfashin guda biyu da aka gicciye su tare suka zage shi. |
24252 | MAT 27:54 | Da hafsan sojan da wadanda suke kallon Yesu suka ga girgizar kasar da abinda ya faru, suka ji tsoro kwarai sukace, “Hakika wannan Dan Allah ne” |
24343 | MRK 2:14 | Sa'adda ya na wucewa, ya ga Levi dan Halfa yana zaune a wurin karbar haraji, sai ya ce masa, “Ka biyo ni.” Ya tashi, ya bi shi. |
24355 | MRK 2:26 | Yadda ya shiga gidan Ubangiji, sa'adda Abiyata ya ke babban firist, ya ci gurasa da ke ta firist wadda bai dace wani ya ci ba sai Firistoci. Har kuma ya ba wadanda ke tare da shi.” |
24363 | MRK 3:6 | Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi. |
24375 | MRK 3:18 | da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye, |
24382 | MRK 3:25 | Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba. |
24385 | MRK 3:28 | Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta, |
24408 | MRK 4:16 | Haka kuma wadanda aka shuka a wuri mai duwatsu, sune wadanda da zarar sun ji Maganar sai su karba da farin ciki. |
24432 | MRK 4:40 | Ya ce masu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu baku da bangaskiya ne?” |
24490 | MRK 6:14 | Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa. |
24491 | MRK 6:15 | Wadansu kuma suna cewa, “Iliya,” Har yanzu wadansu suna cewa daya “daga cikin annabawa ne na da can.” |
24492 | MRK 6:16 | Sa'adda Hirudus ya ji wannan sai ya ce, “Yahaya wanda na fillewa kai shine ya tashi.” |
24493 | MRK 6:17 | Saboda Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku saboda Hirodiya( matar Filibus dan'uwansa), domin ya aure ta. |
24494 | MRK 6:18 | Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba. |
24495 | MRK 6:19 | Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba. |
24496 | MRK 6:20 | Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi. |
24497 | MRK 6:21 | Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili. |
24498 | MRK 6:22 | Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, “ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi”. |
24523 | MRK 6:47 | Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai. |
24581 | MRK 8:12 | Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, “Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar.” |
24584 | MRK 8:15 | Ya gargade su, “ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus.” |
24586 | MRK 8:17 | Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, “Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?” |
24608 | MRK 9:1 | Sai ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.” |
24669 | MRK 10:12 | Haka nan duk matar da ta saki mijinta ta auri wani ta yi zina da shi kenan.” |
24718 | MRK 11:9 | Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji. |
24720 | MRK 11:11 | San nan Yesu ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Sai ya dudduba komai, da magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyu nan. |
24732 | MRK 11:23 | Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun', bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi. |
24742 | MRK 11:33 | Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba” Yesu ya ce masu, “Haka ni kuma ba zan fada muku ko da wanne iko nake yin abubuwan nan ba.” |
24747 | MRK 12:5 | Ya sake aiken wani. Shi kam, suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wadansu da yawa, sun dodoki wadansu, suka kuma kashe wadansu. |
24755 | MRK 12:13 | Suka aika masa da wadansu farisiyawa da Heridiyawa, don su sa masa tarko da kalamai cikin maganarsa. |
24764 | MRK 12:22 | Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar 'ya'ya. A karshe kuma ita matar ta mutu. |