23214 | MAT 1:1 | Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim. |
23215 | MAT 1:2 | Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da 'yan'uwansa. |
23230 | MAT 1:17 | Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne |
23236 | MAT 1:23 | “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.” |
23240 | MAT 2:2 | ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.'' |
23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
23244 | MAT 2:6 | 'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.''' |
23246 | MAT 2:8 | Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” |
23255 | MAT 2:17 | A lokacin ne aka cika fadar Annabi Irmiya, |
23258 | MAT 2:20 | ''Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu.'' |
23259 | MAT 2:21 | Yusufu ya tashi, ya dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ya zo kasar Isra'ila. |
23264 | MAT 3:3 | Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.'' |
23270 | MAT 3:9 | Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. |
23279 | MAT 4:1 | Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi. |
23281 | MAT 4:3 | Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” |
23283 | MAT 4:5 | Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali, |
23284 | MAT 4:6 | ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.''' |
23286 | MAT 4:8 | Kuma, sai Ibilis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo kwarai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. |
23289 | MAT 4:11 | Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima. |
23292 | MAT 4:14 | Wannan ya faru domin a cika fadar annabi Ishaya cewa, |
23332 | MAT 5:29 | Idan idonka na dama zai sa ka tuntube, kwakule shi ka jefar daga gareka. Don gara daya daga cikin gabobinka ya halaka, da a jefa dukan jikin ka a jahannama. |
23340 | MAT 5:37 | Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. |
23341 | MAT 5:38 | Kun dai ji an ce, “Ido a maimakon ido, hakori kuma a maimakon hakori.' |
23343 | MAT 5:40 | Idan wani yana da niyyar kai kararku gaban shari'a saboda ya karbi rigarku, ku ba wannan mutumin mayafinku ma. |
23358 | MAT 6:7 | Idan za ku yi addu'a, kada ku yi ta maimaici marar anfani, kamar yadda al'ummai suke yi, domin a tunanin su za a saurare su saboda yawan maganganunsu. |
23366 | MAT 6:15 | In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku laifuffukanku ba.” |
23373 | MAT 6:22 | Ido shi ne fitilar jiki. Saboda haka, idan idonka na da kyau, dukan jiki na cike da haske. |
23381 | MAT 6:30 | Idan Allah yayi wa ciyawar jeji ado, wadda yau tana wanzuwa, gobe kuwa a jefa ta cikin murhu, ina misalin adon da za ya yi maku, ya ku masu karancin bangaskiya? |
23391 | MAT 7:6 | Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa aladu, lu'u lu'anku. Idan ba haka ba za su tattake su a karkashin sawunsu, su kuma juyo su kekketa ku. |
23425 | MAT 8:11 | Na gaya maku, da yawa za su zo daga gabas da yamma, su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Ishaku, da Yakubu a cikin mulkin sama. |
23431 | MAT 8:17 | Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.” |
23443 | MAT 8:29 | Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” |
23445 | MAT 8:31 | Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” |
23465 | MAT 9:17 | Mutane kuma ba su dura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Idan sun yi haka, sai salkunan kuma su fashe inabin ya tsiyaye, sai salkunan su lalace. A maimakon haka, ana sa sabon inabi cikin sababbin salkuna, ta haka an tsirar da duka biyun kenan.'' |
23476 | MAT 9:28 | Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?'' Sai suka ce masa. ''I, ya Ubangiji.'' |
23481 | MAT 9:33 | Bayan da an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, su ka ce, ''Kai, ba a taba ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba!'' |
23490 | MAT 10:4 | Saminu Bakairawane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi. |
23492 | MAT 10:6 | Sai dai ku je wurin batattun tumaki na gidan Isra'ila. |
23498 | MAT 10:12 | In za ku shiga gida ku ce, salama a gareku. |
23499 | MAT 10:13 | Idan gidan akwai dan salama, salamarku za ta ta tabbata a gare shi. Idan kuwa babu, salamarku za ta komo maku. |
23505 | MAT 10:19 | Idan har sun bada ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku fada, domin za a ba ku abin da za ku fada a lokacin. |
23509 | MAT 10:23 | In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo. |
23511 | MAT 10:25 | Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa! |
23528 | MAT 10:42 | Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba.'' |
23539 | MAT 11:11 | Ina gaya maku gaskiya, cikin wadanda mata suka haifa, babu mai girma kamar Yahaya mai baftisma. Amma mafi kankanta a mulkin sama ya fi shi girma. |
23542 | MAT 11:14 | kuma in zaku karba, wannan shine Iliya wanda za ya zo. |
23549 | MAT 11:21 | “Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka. |
23553 | MAT 11:25 | A wannan lokaci Yesu ya ce, “Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara. |
23554 | MAT 11:26 | I, ya Uba gama wannan shine ya yi daidai a gare ka. |
23565 | MAT 12:7 | In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba. |
23575 | MAT 12:17 | domin ya zama gaskiyar abin da aka fada ta wurin annabi Ishaya, cewa, |
23584 | MAT 12:26 | Idan Shaidan ya fitar da Shaidan, ya rabu gaba da kansa. Yaya mulkin sa za ya tsaya? |
23585 | MAT 12:27 | Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku. |
23601 | MAT 12:43 | Idan kazamin ruhu ya rabu da mutum, ya kan wuce ya nemi wuraren da ruwa yake domin ya huta, amma bai samu ba. |
23622 | MAT 13:14 | A gare su ne annabcin Ishaya ya cika, wanda yake cewa, “Game da sauraro zaku saurara, amma ba za ku fahimta ba. Game da gani kuma za ku kalla, amma ba za ku gane ba. |
23627 | MAT 13:19 | Idan wani ya ji maganar mulkin sama amma bai fahimce ta ba, sai mugun nan ya zo ya kwace abinda aka shuka a zuciyarsa. Wannan shine irin da aka shuka a kan hanya. |
23643 | MAT 13:35 | Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, “Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya.” |
23659 | MAT 13:51 | Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, “I”. |
23709 | MAT 15:7 | Ku munafukai, daidai ne Ishaya ya yi annabci akan ku da ya ce, |
23716 | MAT 15:14 | Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami.” |
23726 | MAT 15:24 | Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila.” |
23729 | MAT 15:27 | Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.” |
23733 | MAT 15:31 | Don haka mutane da yawa suka yi mamaki a lokacin da suka ga bebaye suna magana, nakasassu sun warke, guragu suna tafiya, makafi suna gani. Sai suka daukaka Allah na Isra'ila. |
23734 | MAT 15:32 | Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.” |
23755 | MAT 16:14 | Suka ce, “Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.” |
23759 | MAT 16:18 | Ina kuma gaya maka cewa kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikilisiya ta. Kofofin hades ba za su yi nasara da ita ba. |
23772 | MAT 17:3 | Sai ga Musa da Iliya sun bayyana garesu suna magana da shi. |
23773 | MAT 17:4 | Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.” |
23779 | MAT 17:10 | Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, “Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?” |
23780 | MAT 17:11 | Yesu ya amsa ya ce, “Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa. |
23781 | MAT 17:12 | Amma ina gaya maku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. A maimakon haka, suka yi masa abin da suka ga dama. Ta irin wanan hanya, Dan Mutum kuma zai sha wuya a hannunsu. |
23790 | MAT 17:21 | [Irin wannan aljanin bashi fita sai tare da addu'a da azumi]. |
23794 | MAT 17:25 | Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?” |
23796 | MAT 17:27 | Amma don kada mu sa masu karbar harajin su yi zunubi, ka je teku, ka jefa kugiya, ka cire kifin da ya fara zuwa. Idan ka bude bakinsa, za ka sami shekel. Ka dauke shi ka ba masu karbar harajin nawa da naka. |
23804 | MAT 18:8 | Idan hannunka ko kafarka ce za ta sa ka tuntube, ka yanke ta, ka yar daga gare ka. Zai fi maka kyau ka shiga rai da nakasa ko gurguntaka, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta tare da hannayenka ko kafafunka. |
23805 | MAT 18:9 | Idan idonka zai sa ka tuntube, ka kwakule shi, ka yar. Zai fi maka kyau ka shiga rai da ido daya, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta da idanu biyu. |
23808 | MAT 18:12 | Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba? |
23809 | MAT 18:13 | In ya same ta, hakika ina gaya maku, farin cikinsa na samun dayan nan da ta bace, zai fi na tassa'in da taran nan da basu bata ba. |
23811 | MAT 18:15 | Idan dan'uwanka yayi maka laifi, fada masa tsakaninku, kai da shi kadai. Idan ya saurare ka, ka maido da dan'uwanka kenan. |
23813 | MAT 18:17 | In kuma ya ki ya saurare su, ka kai lamarin ga ikklisiya. Idan ya ki ya saurari ikklisiya, ka maishe shi ba'al'umme da mai karbar haraji. |
23840 | MAT 19:9 | Ina gaya maku, duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, yana zina kenan. Wanda kuma ya auri macen da aka saka, yana aikata zina.'' |
23841 | MAT 19:10 | Almajiran suka ce wa Yesu, ''Idan haka yake game da mutum da matarsa, ba kyau ayi aure ba.'' |
23852 | MAT 19:21 | Yesu ya ce masa, ''Idan kana so ka zama cikakke, ka tafi ka sayar da mallakarka, ka kuma ba matalauta, zaka sami dukiya a sama. Sa'annan ka zo ka biyo ni.'' |
23855 | MAT 19:24 | Ina sake gaya maku, zai fi wa rakumi sauki ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.'' |
23859 | MAT 19:28 | Yesu ya ce masu, ''Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'anta kabilu goma sha biyu na Isra'ila. |
23882 | MAT 20:21 | Yesu ya ce mata, Me kike so in yi maki?'' Sai ta ce masa, ''Ina so ka ba 'ya'yana izinin zama a mulkinka, daya a hannun damanka, daya kuma a hannun hagunka. |
23884 | MAT 20:23 | Sai ya ce masu, ''In dai kokon nan da zan sha ne, lallai zaku sha. Amma, zama a hannun dama na da kuma hannun hagu na, ba ni ne mai bayarwa ba, amma na wadanda Uba na ya shirya domin su ne.'' |
23898 | MAT 21:3 | Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan.” |
23911 | MAT 21:16 | Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?'' Yesu ya ce masu, “I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?” |
23919 | MAT 21:24 | Yesu ya amsa yace masu, “Ni ma zan yi maku tambaya daya. In kun fada mani, ni ma zan fada maku ko da wane iko nake yin wadannan abubuwa. |
23920 | MAT 21:25 | Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?” Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, “In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?' |
23965 | MAT 22:24 | cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. |
23973 | MAT 22:32 | 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.” |