Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   L    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23214  MAT 1:1  Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim.
23302  MAT 4:24  Labarinsa ya bazu a cikin dukan kasar Suriya, kuma mutanen suka kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farfadiya, da shanyayyu. Yesu ya warkar da su.
23474  MAT 9:26  Labarin kuwa ya bazu a duk yankin.
23653  MAT 13:45  Haka ma za a kwatanta mulkin sama da wani attajiri mai neman Lu'ulu'ai masu daraja.
23743  MAT 16:2  Amma ya amsa ya ce masu,Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,'
23803  MAT 18:7  Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo!
24299  MRK 1:15  Yana cewa,Lokaci ya yi, gama mulkin Allah ya kusato. Ku tuba ku bada gaskiya ga bishara”.
24333  MRK 2:4  Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai.
24343  MRK 2:14  Sa'adda ya na wucewa, ya ga Levi dan Halfa yana zaune a wurin karbar haraji, sai ya ce masa, “Ka biyo ni.” Ya tashi, ya bi shi.
24344  MRK 2:15  Sa'adda Yesu ya shiga gidan Levi yana cin abinci, masu karbar haraji da masu zunubi da yawa su ka zo wurinsa da almajiransa, jama'a masu yawan gaske suka ka bi shi.
24667  MRK 10:10  Lokacin da suke cikin gida, sai almajiransa suka sake tambayarsa akan wannan magana.
24674  MRK 10:17  Lokacin da ya fara tafiya, sai wani mutum ya rugo wurinsa, ya durkusa a gabansa. Ya tambaye shi, yace ya ''Malam managarci, me zan yi domin in sami rai na har abada?''
24845  MRK 14:22  Lokacin da suke cin abincin, Yesu ya dauki gurasa ya sa albarka, ya gutsuttsura ta, sai ya basu yana cewa “Wannan jikinana ne”.
24861  MRK 14:38  Ku zauna a fadake, kuyi addu'a kada ku fada cikin jaraba. Lalle ruhu na da niyya amma jiki raunana ne.
24864  MRK 14:41  Ya sake komowa karo na uku yace masu “har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi”.
24872  MRK 14:49  Lokacin da nake koyarwa a Haikali, kowace rana da ku, baku kama ni ba. Amma anyi haka ne domin a cika abinda Nassi ya fada.”
24893  MRK 14:70  Amma ya sake musawa, jim kadan sai na tsaitsayen suka ce wa BitrusLalle kai ma dayansu ne don ba Galile ne kai”.
25095  LUK 3:1  A cikin shekara ta goma sha biyar da Tibariyus Kaisar ke mulki, Bilatus Babunti kuma ke jagorar Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, dan'uwansa Filibus yana sarautar yankin Ituriya da Tirakonitis, Lisaniyas kuma na sarautar yankin Abiliya,
25115  LUK 3:21  Ana nan, lokacin da ake yiwa dukan mutane baftisma, aka yiwa Yesu mai baftisma. Lokacin da yake yin addu'a, sai sama ta bude,
25118  LUK 3:24  dan Matat, dan Lawi, dan Malki, dan Yanna, dan Yusufu,
25123  LUK 3:29  dan Yosi, dan Aliyeza, dan Yorima, dan Matat, dan Lawi,
25130  LUK 3:36  dan Kainana, dan Arfakshada, dan Shem, dan Nuhu, dan Lamek,
25155  LUK 4:23  Yesu ya ce masu,Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'”
25203  LUK 5:27  Bayan wadannan abubuwa sun faru, Yesu ya fito daga can sai ya ga wani mai karban haraji mai suna Lawi yana zama a wurin karban haraji. Ya ce masa, “Ka biyo ni.”
25204  LUK 5:28  Sai Lawi ya bar komai, ya tashi, ya bi shi.
25205  LUK 5:29  Lawi kuma ya shirya gagarumar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karban haraji da yawa a nan, da wasu mutane da ke zama a gaban teburin liyafar suna cin abinci tare da su.
25348  LUK 8:34  Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen.
25503  LUK 11:29  Lokacin da mutane suke kara taruwa, sai ya fara cewa, “Wannan tsara, muguwar tsara ce. Ta na neman alama, Ko da yake ba wata alamar da za a bata sai irin ta Yunusa.
25691  LUK 16:2  Sai mai arziki ya kira shi ya ce masa, 'Labarin me nake ji game da kai? Kawo lissafin wakilcin ka, don ba za ka sake zama wakili na ba.'
25712  LUK 16:23  yana cikin hades yana shan azaba, sai ya daga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a kirjinsa.
25713  LUK 16:24  Sai ya yi kira ya ce, 'Baba Ibrahim, ka ji tausayi na, ka aiko Li'azaru ya tsoma dan yatsansa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.'
25714  LUK 16:25  Amma Ibrahim ya ce, 'Yaro, ka tuna fa a zamanka na duniya ka sha duniyarka, ka kuma karba abubuwa masu kyau, amma Li'azaru kuma sai wahala. Amma yanzu dadi ake bashi a nan, kai kuwa kana shan azaba.
25748  LUK 17:28  Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine.
25749  LUK 17:29  Amma a ranar da Lutu, ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da kibiritu daga sama, aka hallaka su duka.
25752  LUK 17:32  Ku tuna fa da matar Lutu.
25903  LUK 21:8  Yesu ya amsa, “Ku yi hankali kada a rude ku. Gama dayawa zasu zo a cikin sunana, suna cewa, 'Ni ne shi,' kuma, 'Lokaci ya yi kusa.' Kada ku bi su.
25968  LUK 22:35  Sa'annan Yesu ya ce masu,Lokacin da na aike ku babu jaka, ko burgami ko takalma, ko kun rasa wani abu? Sai suka amsa, “Babu.”
26051  LUK 23:47  Sa'adda jarumin ya ga abin da ya faru, ya daukaka Allah, cewa,Lallai wannan mutumin mai adalci ne.”
26094  LUK 24:34  cewa,Lalle ne Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman.”
26132  JHN 1:19  Wannan ita ce shaidar Yahaya sa'adda Yahudawa suka aika da Firistoci da Lawiyawa zuwa gareshi don su tambaye shi, “Wanene kai?”
26168  JHN 2:4  Yesu yace mata, “Mace, me yasa kika zo wurina? Lokaci na bai yi ba tukuna”.
26593  JHN 11:1  To wani mutum mai suna Li'azaru, yayi rashin lafiya. Shi mutumin Baitanya ne, wato kauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Matta.
26594  JHN 11:2  Wato wannan Maryamu da ta shafe Ubangiji da mur ta kuma share masa kafafunsa da gashin kanta, wadda dan'uwanta Li'azaru ke rashin lafiya.
26597  JHN 11:5  Yesu yana kaunar Matta, da 'yar'uwarta da Li'azaru.
26598  JHN 11:6  Da yaji cewa Li'azaru na rashin lafiya, sai ya tsaya kwana biyu a inda ya ke.
26603  JHN 11:11  Ya fadi wadannan al'amura, kuma bayan wadannan abubuwa, sai ya ce masu, “Abokinmu Li'azaru ya yi barci, amma zan je don In tashe shi daga barci”.
26605  JHN 11:13  Yesu kuwa ya yi maganar mutuwar Li'azaru ne, amma su suna tsammani yana magana akan barci ne na hutu.
26606  JHN 11:14  Sai Yesu ya yi masu bayani cewa,Li'azaru ya mutu.
26609  JHN 11:17  Da Yesu ya iso, sai ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari.
26628  JHN 11:36  Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!”
26631  JHN 11:39  Sai Yesu ya ce, “A kawar da dutsen.” Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, “Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa”.
26635  JHN 11:43  Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce,Li'azaru, ka fito!”
26650  JHN 12:1  Kwana shidda kafin idin ketarewa, Yesu ya zo Baitanya inda Li'azaru yake, wato wannan da Yesu ya tada daga matattu.
26651  JHN 12:2  Sai suka shirya masa abinci a wurin kuma Matta ce ke hidima, Li'azaru kuwa ya kasance cikin wadanda ke kan tebiri tare da Yesu.
26658  JHN 12:9  To babban taron Yahudawa sun ji cewa Yesu yana wurin, sai suka zo, ba don Yesu kawai ba amma domin su ga Li'azaru, wanda Yesu ya tada daga matattu.
26659  JHN 12:10  Sai manyan firistoci suka kulla makirci akan yadda za su kashe Li'azaru shima;
26666  JHN 12:17  Sai taron da ke tare da Yesu a ranar da ya kira Li'azaru daga kabari ya kuma tashe shi daga matattu, suka bada shaida.
26715  JHN 13:16  Lalle hakika ina gaya muku, bawa ba ya fi mai gidansa girma ba; dan aike kuma ba ya fi wanda ya aiko shi girma ba.
26720  JHN 13:21  Bayan Yesu ya fadi haka, ya damu a ruhu, ya yi shaida ya ce,Lalle hakika, ina gaya muku cewa daya daga cikinku zai bashe ni.”
26737  JHN 13:38  Yesu ya amsa ya ce, “ Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku.”
26749  JHN 14:12  Lalle hakika, ina gaya maku, duk wanda ya gaskata ni zai yi ayyukan da nake yi, kuma zai yi ayyuka fiye da wadannan, domin zan tafi wurin Uba.
26840  JHN 17:12  Lokacin da ina tare da su, na adanasu acikin sunanka da ka ba ni. Na kiyaye su, kuma ko daya kuwa daga cikinsu ba ya bace ba, sai dai dan hallakar nan, domin Nassi ya cika.
26993  ACT 1:1  Littafin da na rubuta da farko, Tiyofilos, ya fadi abubuwan da Yesu ya fara yi ya kuma koyar,
27001  ACT 1:9  Lokacin da Ubangiji Yesu ya fadi wadannan abubuwa, yayin da suna kallon sama, sai aka dauke shi zuwa sama, kuma girgije ya boye shi daga idanunsu.
27025  ACT 2:7  Suka yi mamaki matuka; suka ce, ''Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne?
27028  ACT 2:10  cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma,
27029  ACT 2:11  Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.''
27244  ACT 7:59  Lokacin da suke kan jifan Istifanus, ya dinga kira yana cewa, ''Ya Ubangiji Yesu, ka karbi ruhu na.”
27273  ACT 8:28  Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya.
27317  ACT 9:32  Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda.
27320  ACT 9:35  Sai duk mazauna kasar Lidda da kasar Sarona suka ga mutumin, suka kuma juyo ga Ubangiji.
27323  ACT 9:38  Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, ''Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba.''
27378  ACT 11:2  Lokacin da Bitrus ya je Urushalima, wadanda suke na kaciya suka zarge shi;
27398  ACT 11:22  Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya.
27432  ACT 13:1  A cikin iklisiyar da take Antakiya, akwai annabawa da malamai. Sune su Barnabas, Saminu (wadda ake kira Baki) da Lukiya Bakurame da Manayin (wanda aka yi renon su tare da sarki Hiridus mai mulki) da Shawulu.
27489  ACT 14:6  da suka gane haka suka gudu zuwa biranen Likoniya, Listira da Darbe, da garuruwa wadanda ke kewaye da su,
27491  ACT 14:8  A Listira akwai wani wanda ke zaune bai taba tashi da kafafunsa ba, don shi gurgu ne tun daga haihuwa.
27494  ACT 14:11  Da jama'an garin sun ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryarsu suna cewa da Likoniyanci, “Ai alloli sun ziyarce mu daga sama, da kamanin mutane.”
27504  ACT 14:21  Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birnin suka kuma sami almajirai da yawa, suka dawo Listira, da Ikoniya da Antikiya.
27553  ACT 16:1  Bulus ya kuma isa Darbe da Listira, in da akwai wani almajiri mai suna Timoti a wurin, dan wata Bayahudiya wadda ta ba da gaskiya; ubansa kuwa Baheline ne.
27554  ACT 16:2  Ana maganar kirki a kansa ta bakin 'yan'uwa da ke Listira da Ikoniyan.
27566  ACT 16:14  Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi.
27592  ACT 16:40  Da hakanan ne Bulus da Sila suka fita daga kurkuku, sun je gidan Lidiya. Da Bulus da Sila sun ga 'yan'uwa, sun karfafa su, sa'annan suka bar birnin.
27632  ACT 18:6  Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, “Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai.”
27828  ACT 23:26  Gaisuwa zuwa Kuludiyas Lisiyas zuwa ga mai martaba gwamna Filikus.
27839  ACT 24:2  Lokacin da Bulus ya tsaya gaban gwamna, Tartilus ya fara zarginsa yace wa gwamnan, “Saboda kai mun sami zaman lafiya; sa'annan hangen gabanka ya kawo gyara a kasarmu;
27844  ACT 24:7  Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu.
27859  ACT 24:22  Filikus yana da cikakken sanin tafarkin Hanyar, shi yasa ya daga shari'ar. Yace da su, “Duk sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima, zan yanke hukunci.”
27928  ACT 27:5  Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya.
27931  ACT 27:8  Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya.
28055  ROM 2:25  Lallai kuwa kaciya tana da riba a gare ku, idan kuka kiyaye doka, amma idan ku marasa bin doka ne kaciyarku ta zama rashin kaciya.
28224  ROM 9:1  Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki.
28425  ROM 16:21  Timoti abokin aikina, yana gaishe ku, haka Lukiyas da Yason da Susibataras da kuma yan'uwana.
28463  1CO 2:1  Lokacin da na zo wurin ku, yan'uwa, ban zo da gwanintar magana ko hikima ba yayinda na yi shelar boyayyun bayanai game da Allah [ a yayinda na bada shaida game da Allah].
28523  1CO 5:1  Mun ji cewa akwai lalata mai kazanta a cikin ku, irin lalatar ba ba a yarda da ita ba ko a cikin al'ummai. Labarin da na samu shine, wani daga cikin ku yana kwana da matar mahaifinsa.
28526  1CO 5:4  Lokacin da ku ka taru a cikin sunan Ubangijinmu Yesu, ruhuna yana nan tare da ku cikin ikon Ubangiji Yesu, na rigaya na hukunta wannan mutum.
28552  1CO 6:17  Kamar yadda Littafi ya fadi, “Su biyun za su zama nama daya.” Amma wanda yake hade da Ubangiji ya zama ruhu daya da shi kenan.
28602  1CO 8:7  Amma ba kowa ke da wannan ilimi ba. Shi ya sa tun da, wadan su na bauta wa gunki, kuma suna cin wannan abincin kamar abin da aka mika wa gunki. Lamirin su ya kazantu sabo da yana da rauni.