23217 | MAT 1:4 | Aram shine mahaifin Amminadab, Amminadab shine mahaifin Nashon, Nashon shine mahaifin Salmon. |
23261 | MAT 2:23 | sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat. Wannan ya cika abin da aka fada ta bakin annabawa, cewa, za a kira shi Banazare. |
23272 | MAT 3:11 | Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. |
23275 | MAT 3:14 | Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?” |
23291 | MAT 4:13 | Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali. |
23293 | MAT 4:15 | “Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! |
23298 | MAT 4:20 | Nan da nan sai suka bar tarunsu, suka bi shi. |
23300 | MAT 4:22 | Nan take suka bar mahaifinsu da jirgin, suka bi shi. |
23392 | MAT 7:7 | Roka, kuma za a ba ku. Nema, kuma za ku samu. Kwankwasa kuma za a bude maku. |
23408 | MAT 7:23 | Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!' |
23417 | MAT 8:3 | Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa. |
23425 | MAT 8:11 | Na gaya maku, da yawa za su zo daga gabas da yamma, su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Ishaku, da Yakubu a cikin mulkin sama. |
23461 | MAT 9:13 | Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, 'Ni kam, ina bukatar jinkai ba hadaya ba.' Ba domin in kira masu adalci su tuba na zo ba, sai dai masu zunubi. |
23470 | MAT 9:22 | Sai Yesu ya juya, ya gan ta ya ce, '''Yata, ki karfafa. Bangaskiyarki ta warkar da ke.'' Nan take matar ta warke. |
23488 | MAT 10:2 | To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya; |
23565 | MAT 12:7 | In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba. |
23599 | MAT 12:41 | Mutanen Nineba za su tsaya a ranar shari'a da wannan zamani sannan su kashe su. Domin sun tuba da suka ji wa'azin Yunusa, amma duba wanda ya fi Yunusa yana nan. |
23613 | MAT 13:5 | Wadansu irin kuwa suka fadi a kan duwatsu, wurin da babu kasa. Nan da nan sai suka tsira, domin kasar babu zurfi. |
23688 | MAT 14:22 | Nan take sai ya sa almajiran suka shiga kwale-kwalen su haye zuwa dayan gefen kafin shi, domin ya sallami taron. |
23693 | MAT 14:27 | Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.” |
23697 | MAT 14:31 | Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?” |
23785 | MAT 17:16 | Na kawo shi wurin almajiran ka, amma ba su iya su warkar da shi ba.” |
23895 | MAT 20:34 | Sai Yesu yayi juyayi a cikin sa, ya taba idanunsu. Nan da nan, suka sami ganin gari, suka kuma bi shi. |
23906 | MAT 21:11 | Sai jama'a suka amsa, “Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili.” |
23919 | MAT 21:24 | Yesu ya amsa yace masu, “Ni ma zan yi maku tambaya daya. In kun fada mani, ni ma zan fada maku ko da wane iko nake yin wadannan abubuwa. |
23922 | MAT 21:27 | Sai suka amsa ma Yesu suka ce, ''Bamu sani ba.” Shi ma yace masu, “Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba. |
23962 | MAT 22:21 | Suka ce masa, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce masu, “To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.” |
23966 | MAT 22:25 | Akwai wasu 'yan'uwa bakwai. Na farkon yayi aure sai ya mutu. Da shike bai bar 'ya'ya ba. Ya bar wa dan'uwansa matarsa. |
23973 | MAT 22:32 | 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.” |
24063 | MAT 24:37 | Kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka zai zama game da zuwan Dan Mutum. |
24064 | MAT 24:38 | A wadannan kwankin kafin zuwan ruwan tsufana suna ci suna sha, suna aure suna aurarwa har ranar da Nuhu ya shiga jirgin, |
24102 | MAT 25:25 | Na ji tsoro, don haka sai na je na boye talantinka a rami. Duba, ga abinda yake naka.' |
24112 | MAT 25:35 | Gama na ji yunwa kuka bani abinci; Na ji kishi kuka bani ruwa; Na yi bakunci kun bani masauki; |
24113 | MAT 25:36 | Na yi huntanci kuka tufasar dani; Na yi ciwo kuka kula dani; Ina kurkuku kuka ziyarceni.' |
24145 | MAT 26:22 | Suka yi bakin ciki, suka fara tambayarsa daya bayan daya, ''Na tabbata ba ni bane ko, Ubangiji?” |
24172 | MAT 26:49 | Nan da nan ya kaiga Yesu ya ce, “Gaisuwa, Mallam!” sai ya sumbace shi. |
24174 | MAT 26:51 | Nan take, daya daga cikin wadanda suke tare da Yesu ya mika hannunsa, ya zare takobinsa, ya sare wa bawan babban firist din kunne. |
24186 | MAT 26:63 | Amma Yesu yayi shiru. Babban Firist ya ce, “Na umarce ka da sunan Allah mai rai, ka gaya mana ko kai Almasihu ne, Dan Allah.'' |
24202 | MAT 27:4 | yace, “Na yi zunubi ta wurin cin amanar mara laifi.” Amma sukace, “Ina ruwan mu? Ka ji da shi da kanka?” |
24241 | MAT 27:43 | Tun da ya yarda da Allah. Bari Allahn ya cece shi mana, saboda yace, “Ni dan Allah ne.” |
24246 | MAT 27:48 | Nan take wani ya ruga da gudu ya dauki soso ya tsoma cikin ruwan inabi mai tsami ya soka kan sandar kara ya mika masa ya sha. |
24292 | MRK 1:8 | Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki''. |
24293 | MRK 1:9 | Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun. |
24302 | MRK 1:18 | Nan da nan suka bar tarun su, suka bi shi. |
24308 | MRK 1:24 | Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah”. |
24312 | MRK 1:28 | Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili. |
24325 | MRK 1:41 | Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa “Na yarda. Ka sarkaka”. |
24326 | MRK 1:42 | Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa. |
24337 | MRK 2:8 | Nan da nan Yesu ya sani a ruhunsa, abinda suke tunani a tsakaninsu. Ya ce masu, “Me ya sa kuke tunanin wannan a zuciyarku? |
24340 | MRK 2:11 | ''Na ce maka, tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidan ka.” |
24397 | MRK 4:5 | Wadansu kuma suka fadi a kan dutse inda ba kasa dayawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin kasa. |
24463 | MRK 5:30 | Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce “wanene ya taba rigata?” |
24475 | MRK 5:42 | Nan da nan yarinyar ta tashi ta yi tafiya [gama shekarun ta sun kai goma sha biyu]. Nan da nan mutanen suka yi mamaki kwarai da gaske. |
24521 | MRK 6:45 | Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen. |
24567 | MRK 7:35 | Nan da nan ya mayar masa da jinsa. abinda ya daure harshensa ya sake shi, sai ya fara magana da kyau. |
24579 | MRK 8:10 | Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta. |
24615 | MRK 9:8 | Nan take da suka duba, ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kadai. |
24631 | MRK 9:24 | Nan da nan mahaifin yaron ya daga murya ya ce, Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata. |
24709 | MRK 10:52 | Yesu ya ce masa. ''Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.'' Nan take idanunsa suka bude, ya bi Yesu, suka tafi tare. |
24758 | MRK 12:16 | Suka kawowa Yesu daya. Ya ce masu, “ Kamar waye da kuma rubutun wanene? suka ce masa, “Na Kaisar ne.” |
24763 | MRK 12:21 | Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba 'ya'ya. Na ukun ma haka. |
24768 | MRK 12:26 | Amma game da mattattun da suka tashi, ashe, ba ku taba karantawa a littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa? “Ni ne Allah na Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu'? |
24809 | MRK 13:23 | Amma ku zauna a fadake, Na dai fada maku wadannan abubuwan kafin lokacin. |
24866 | MRK 14:43 | Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, daya daga cikin sha biyun da taron jama'a rike da takkuba da kulake. Manyan firistoci da malaman attaura da shugabanni suka turo su. |
24872 | MRK 14:49 | Lokacin da nake koyarwa a Haikali, kowace rana da ku, baku kama ni ba. Amma anyi haka ne domin a cika abinda Nassi ya fada.” |
24885 | MRK 14:62 | Yesu ya ce “Nine. Za ku kuwa ga Dan Mutum zaune dama ga mai iko, yana kuma zuwa cikin gajimare”. |
24891 | MRK 14:68 | Amma ya musa ya ce “Ni ban ma san abinda kike fada ba balle in fahimta”. Sai ya fito zaure. Sai zakara yayi cara. |
24895 | MRK 14:72 | Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu, Bitrus kuwa ya tuna da maganar Yesu a gare shi cewa “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sani na sau uku”. Da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka. |
24981 | LUK 1:19 | Mala'ikan ya amsa ya ce masa, “Nine Jibra'ilu, wanda ke tsaye a gaban Allah. An aiko ni in gaya maka wannan labari mai dadi. |
24988 | LUK 1:26 | A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat, |
25026 | LUK 1:64 | Nan take, sai bakinsa ya bude kuma harshensa ya saki. Ya yi magana ya kuma yabi Allah. |
25046 | LUK 2:4 | Yusufu kuma ya tashi ya bar birnin Nazarat zuwa garin Baitalami da ke Yahudiya, wanda ake kuma kira birnin Dauda, domin shi daga zuriyar iyalin Dauda ne. |
25051 | LUK 2:9 | Nan da nan, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare su, daukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, sai suka figita kwarai. |
25055 | LUK 2:13 | Nan take, sai ga babban taro daga sama tare da mala'ikan suna yabon Allah, suna cewa, |
25081 | LUK 2:39 | Da su ka gama komai da aka bukace su suyi bisa ga tafarkin shari'ar Ubangiji, sai suka koma Galili, zuwa birninsu, Nazarat. |
25093 | LUK 2:51 | Sa'annan ya koma gida tare da su zuwa Nazarat yana kuma masu biyayya. Mahaifiayarsa kuma ta ajiye dukan wadannan abubuwa a zuciyarta tana yin tunani akansu. |
25119 | LUK 3:25 | dan Matatiya, dan Amos, dan Nahum, dan Hasli, dan Najjaya, |
25121 | LUK 3:27 | dan Yowana, dan Resa, dan Zarubabila, dan Shiyaltiyel, dan Niri, |
25125 | LUK 3:31 | dan Malaya, dan Mainana, dan Matata, dan Natan, dan Dauda, |
25126 | LUK 3:32 | dan Yesse, dan Obida, dan Bu'aza, dan Salmon, dan Nashon, |
25128 | LUK 3:34 | dan Yakubu, dan Ishaku, dan Ibrahim, dan Tera, dan Nahor, |
25130 | LUK 3:36 | dan Kainana, dan Arfakshada, dan Shem, dan Nuhu, dan Lamek, |
25148 | LUK 4:16 | Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi. |
25153 | LUK 4:21 | Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.” |
25159 | LUK 4:27 | Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai. |
25166 | LUK 4:34 | “Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!” |
25171 | LUK 4:39 | Sai ya tsaya a kanta, ya tsautawa zazzabin, kuma ya rabu da ita. Nan take, ta tashi ta fara yi masu hidima. |
25189 | LUK 5:13 | Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, “Na yarda. Ka tsarkaka.” Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi. |
25201 | LUK 5:25 | Nan take, ya tashi a gabansu ya dauki tabarma da yake kwance; sai ya koma gidansa, yana daukaka Allah. |
25273 | LUK 7:9 | Sa'adda Yesu ya ji haka, ya yi mamakin mutumin, ya juya wajen taron da su ke biye da shi, ya ce, “Na gaya maku, ko a cikin Isra'ila ban sami wani mai bangaskiya irin wannan ba” |
25275 | LUK 7:11 | Wani lokaci bayan wannan, ya zama Yesu yana tafiya wani gari da ake kira Na'im. Almajiransa su na tare da shi, da kuma taron mutane masu yawa. |
25308 | LUK 7:44 | Yesu ya juya wajen matar, ya ce da Siman, “Ka ga matan nan. Na shiga gidanka. Ba ka ba ni ruwa domin kafafuna ba, amma ita ta ba ni, da hawayenta ta wanke kafafuna, ta kuma shafe su da gashin kanta. |
25358 | LUK 8:44 | Sai ta biyo ta bayan Yesu ta taba habar rigarsa. Nan take sai zubar jinin ya tsaya. |
25360 | LUK 8:46 | Amma Yesu ya ce, “Na sani, wani ya taba ni, domin iko ya fita daga wurina.” |
25369 | LUK 8:55 | Nan da nan ruhun ta ya dawo jikin ta sai ta tashi. Ya ce masu su ba ta wani abu ta ci. |