Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   U    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23219  MAT 1:6  Yesse shine mahaifin sarki Dauda. Sarki Dauda shine mahaifin Sulaimanu ta wurin matar Uriya.
23221  MAT 1:8  Asa shine mahaifin Yehoshafat, Yehoshafat shine mahaifin Yoram, Yoram kuma shine mahaifin Uziya.
23222  MAT 1:9  Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya.
23233  MAT 1:20  Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi.
23237  MAT 1:24  Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala'ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa.
23239  MAT 2:1  Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,
23241  MAT 2:3  Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu kwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.
23251  MAT 2:13  Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.”
23253  MAT 2:15  Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.''
23257  MAT 2:19  Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce,
23264  MAT 3:3  Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.''
23266  MAT 3:5  Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa.
23267  MAT 3:6  Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu.
23274  MAT 3:13  Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma.
23285  MAT 4:7  Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'''
23288  MAT 4:10  Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.'''
23293  MAT 4:15  “Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai!
23303  MAT 4:25  Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun.
23319  MAT 5:16  Bari hasken ku ya haskaka gaban mutane yadda za su ga kyawawan ayyukanku su kuma yabi Ubanku da ke cikin sama.
23336  MAT 5:33  Kun sake ji an ce wa wadan da suke a zamanin da, 'Kada ku yi rantsuwar karya, amma ku yi rantsuwar ku ga Ubangiji.'
23338  MAT 5:35  ko kuwa da duniya, domin mazaunin kafafunsa ne, ko da Urushalima, domin birnin babban sarki ne.
23348  MAT 5:45  domin ku zama 'ya'yan Ubanku da ke cikin sama. Domin yakan sa rana ta haskaka wa mugu da mutumin kirki, kuma yakan aiko da ruwan sama ga adali da azzalumi.
23351  MAT 5:48  Saboda haka, lalle ne ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama yake cikakke.
23352  MAT 6:1  Ku yi hankali kada ku yi ayyukan adalcinku gaban mutane domin su ganku, idan kun yi haka, ba za ku sami sakamako a wurin Ubanku da yake sama ba.
23355  MAT 6:4  domin sadakarku ta zama a asirce. Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku.
23357  MAT 6:6  Amma ku, idan za ku yi addu'a, sai ku shiga cikin daki. Ku rufe kofa, ku yi addu'a ga Ubanku wanda yake a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku.
23359  MAT 6:8  Domin haka, kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatar ku tun kafin ku roke shi.
23360  MAT 6:9  Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka: 'Ubanmu da ke sama, bari a tsarkake sunanka.
23365  MAT 6:14  Domin in kun yafe wa mutane laifuffukansu, Ubanku na Sama shima zai yafe maku.
23366  MAT 6:15  In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku laifuffukanku ba.”
23369  MAT 6:18  don kada mutane su gane kuna azumi, sai dai Ubanku da yake a asirce. Kuma Ubanku da ke ganin abinda ke a asirce, zai saka maku.”
23377  MAT 6:26  Ku dubi tsuntsayen da ke sararin sama. Ai, ba su shuka, balle girbi, ba su kuma tarawa a cikin rumbuna, amma Ubanku na Sama na ciyar da su. Ashe, ba ku fi su martaba ba?
23383  MAT 6:32  Ai, al'ummai ma suna neman dukan irin wadannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.
23396  MAT 7:11  Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa?
23406  MAT 7:21  Ba duk mai ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ne, zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi nufin Ubana da yake cikin sama.
23407  MAT 7:22  A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?'
23416  MAT 8:2  Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce,Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
23420  MAT 8:6  Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai.”
23422  MAT 8:8  Sai hafsan, ya ce,Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke.
23435  MAT 8:21  Wani cikin almajiran ya ce masa,Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.”
23439  MAT 8:25  Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce,Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”
23476  MAT 9:28  Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?'' Sai suka ce masa. ''I, ya Ubangiji.''
23486  MAT 9:38  Saboda haka sai ku yi sauri ku roki Ubangijin girbin ya turo ma'aikata cikin girbinsa.''
23506  MAT 10:20  Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku.
23515  MAT 10:29  Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba.
23518  MAT 10:32  ''Saboda haka duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, ni ma zan yi shaidar sa a gaban Ubana wanda ya ke cikin Sama.
23519  MAT 10:33  Amma duk wanda ya yi musun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi musun sanin sa a gaban Ubana da yake cikin Sama.''
23553  MAT 11:25  A wannan lokaci Yesu ya ce, “Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara.
23554  MAT 11:26  I, ya Uba gama wannan shine ya yi daidai a gare ka.
23555  MAT 11:27  An mallaka mani dukan abu daga wurin Ubana. Sannan babu wanda ya san Dan, sai Uban, babu kuma wanda ya san Uban, sai Dan, da duk wanda ya so ya bayyana masa.
23566  MAT 12:8  Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.”
23608  MAT 12:50  Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.”
23651  MAT 13:43  Sa'an nan ne mutane masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, ya ji.
23694  MAT 14:28  Bitrus ya amsa masa cewa,Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.”
23696  MAT 14:30  Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce,Ubangiji, ka cece ni!”
23703  MAT 15:1  Sai wadansu Farisawa da malamai suka zo wurin Yesu daga Urushalima. Su ka ce,
23715  MAT 15:13  Yesu ya amsa ya ce, “Kowace shuka wadda ba Ubana na sama ya shuka ba za a tuge ta.
23724  MAT 15:22  Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.”
23727  MAT 15:25  Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa,Ubangiji ka taimake ni.”
23729  MAT 15:27  Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.”
23758  MAT 16:17  Yesu ya amsa ya ce masa, “Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama.
23762  MAT 16:21  Daga lokacin nan Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa dole ne ya tafi Urushalima, ya sha wahala mai yawa a hannun dattawa, da manyan firistoci da malaman attaura, a kashe shi, a tashe shi zuwa rai a rana ta uku.
23763  MAT 16:22  Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.”
23768  MAT 16:27  Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa.
23773  MAT 17:4  Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.”
23784  MAT 17:15  Ubangiji, ka ji tausayin yarona, domin yana da farfadiya, kuma yana shan wuya kwarai, domin sau da yawa yana fadawa cikin wuta ko ruwa.
23806  MAT 18:10  Ku kula fa kada ku rena kananan nan. Domin koyaushe a sama, mala'ikunsu na duban fuskar Ubana da ke sama.
23810  MAT 18:14  Hakanan fa, ba nufin Ubanku dake sama ba ne da ya daga cikin wadannan kananan ya hallaka.
23815  MAT 18:19  Kuma ina gaya maku, idan mutum ku biyu zaku yarda akan duk abin da zaku roka, Ubana wanda ke a sama zai yi maku shi.
23817  MAT 18:21  Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?''
23830  MAT 18:34  Ubangidansa yayi fushi, ya danka shi ga masu azabtarwa, har sai ya gama biyan dukan bashin da ake binsa.
23831  MAT 18:35  Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan'uwansa daga zuciya ba.''
23832  MAT 19:1  Sai ya zama sa'adda Yesu ya gama wadannan maganganu, sai ya bar Galili ya zo kan iyakokin Yahudiya, ketaren kogin Urdun.
23878  MAT 20:17  Da Yesu zai tafi Urushalima, ya dauki sha-biyun nan a gefe, yayin da suke tafiya, sai ya ce masu,
23879  MAT 20:18  “Ku duba fa, zamu tafi Urushalima, kuma za a bada Dan Mutum ga manyan firistoci da marubuta. Za su kuma yanke masa hukuncin kisa,
23884  MAT 20:23  Sai ya ce masu, ''In dai kokon nan da zan sha ne, lallai zaku sha. Amma, zama a hannun dama na da kuma hannun hagu na, ba ni ne mai bayarwa ba, amma na wadanda Uba na ya shirya domin su ne.''
23891  MAT 20:30  Suka kuma ga makafi biyu zaune a bakin hanya. Da makafin suka ji cewa Yesu ne ke wucewa, sai suka tada murya suna cewa, ''Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai.''
23892  MAT 20:31  Amma jama'ar suka tsauta masu, suka ce suyi shiru. Duk da haka, makafin suka kara tada murya fiye da na da, suka ce, ''Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai.''
23894  MAT 20:33  Sai suka ce masa, Ya Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.''
23896  MAT 21:1  Yayinda Yesu da almajiransa suka kusato Urushalima sai suka zo Betafaji wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa guda biyu,
23898  MAT 21:3  Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan.”
23904  MAT 21:9  Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, “Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!”
23905  MAT 21:10  Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, “Wanene wannan?”
23937  MAT 21:42  Yesu yace masu, “Baku taba karantawa a nassi ba,'' 'Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani. Wannan daga Ubangijine, kuma abin mamaki ne a idanunmu?'
23957  MAT 22:16  Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, “Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane.
23978  MAT 22:37  Yesu yace masa, “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.'
23984  MAT 22:43  Yesu yace masu, “To ta yaya kuma Dauda cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji, yana cewa,
23985  MAT 22:44  Ubangiji ya cewa wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na mai da makiyanka matakin sawayenka.”
23986  MAT 22:45  Idan Dauda ya kira Almasihu 'Ubangiji,' ta yaya ya zama dan Dauda?”
23996  MAT 23:9  Kada ku kira kowa 'Ubanku' a duniya, domin Uba daya ne ku ke da shi, kuma yana sama.
24017  MAT 23:30  Kuna cewa, 'Da muna nan a zamanin Ubanninmu, da bamu basu goyon baya ba wajen zubar da jinin annabawa.'
24024  MAT 23:37  Urushalima, Urushalima, keda kika kashe annabawa kika kuma jejjefi wadanda aka turo maki da duwatsu! Sau nawa ne naso in tattaro ki kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fukafukanta, amma kin ki.
24026  MAT 23:39  Ina dai gaya maku, ba za ku kara gani na ba, sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji.”'