Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   W    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23253  MAT 2:15  Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.''
23261  MAT 2:23  sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat. Wannan ya cika abin da aka fada ta bakin annabawa, cewa, za a kira shi Banazare.
23264  MAT 3:3  Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.''
23278  MAT 3:17  Duba, wata murya daga sammai tana cewa, ''Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.''
23292  MAT 4:14  Wannan ya faru domin a cika fadar annabi Ishaya cewa,
23382  MAT 6:31  Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?'
23435  MAT 8:21  Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.”
23441  MAT 8:27  Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce,Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”.
23451  MAT 9:3  Sai wadansu marubuta suka ce a tsakaninsu, ''Wannan mutum sabo yake yi.''
23453  MAT 9:5  Wanne ya fi sauki, a ce, 'An gafarta maka zunubanka,' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya'?
23523  MAT 10:37  Dukan wanda ya fi son mahaifinsa ko mahaifayarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.
23524  MAT 10:38  Wanda kuma bai dauki gicciyensa ya biyo ni ba, bai cancanci zama nawa ba.
23526  MAT 10:40  ''Wanda ya marabce ku, ya marabce ni ke nan.
23527  MAT 10:41  Wanda ya marabce ni kuwa, ya marabci wanda ya aiko ni. Wanda ya marabci annabi domin shi annabi ne, zai karbi lada kamar na annabi. Wanda kuma ya marabci mai adalci saboda shi mai adalci ne, zai sami lada kamar na mai adalci.
23538  MAT 11:10  Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, 'Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi'.
23543  MAT 11:15  Wanda ke da kunnuwan ji, ya ji.
23569  MAT 12:11  Yesu ya ce masu,Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba?
23588  MAT 12:30  Wanda baya tare da ni yana gaba da ni ke nan, wanda kuma baya tarawa tare da ni, yana watsarwa ne.
23606  MAT 12:48  Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa,Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?”
23611  MAT 13:3  Sai Yesu ya fada masu abubuwa da yawa cikin misalai. Ya ce,Wani mai shuka, ya tafi yayi shuka.
23613  MAT 13:5  Wadansu irin kuwa suka fadi a kan duwatsu, wurin da babu kasa. Nan da nan sai suka tsira, domin kasar babu zurfi.
23615  MAT 13:7  Wasu irin kuwa suka fada a cikin kayayuwa. Kayayuwan kuwa suka shake su.
23616  MAT 13:8  Wasu irin kuwa suka fada a wuri mai kyau suka ba da tsaba, wani ya ba da dari, wasu sitin, wasu kuma talatin.
23627  MAT 13:19  Idan wani ya ji maganar mulkin sama amma bai fahimce ta ba, sai mugun nan ya zo ya kwace abinda aka shuka a zuciyarsa. Wannan shine irin da aka shuka a kan hanya.
23631  MAT 13:23  Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin.”
23640  MAT 13:32  Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa.”
23643  MAT 13:35  Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, “Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya.”
23663  MAT 13:55  Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba?
23668  MAT 14:2  Ya ce wa barorinsa,Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa”.
23681  MAT 14:15  Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa,Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci.”
23687  MAT 14:21  Wadanda su ka ci kuwa kimanin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara.
23710  MAT 15:8  Wadannan mutane girmama ni da baki kawai suke yi, amma zukatansu nesa suke da ni.
23722  MAT 15:20  Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum.”
23740  MAT 15:38  Wadanda suka ci su dubu hudu ne maza, banda mata da yara.
23754  MAT 16:13  A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake?
23755  MAT 16:14  Suka ce,Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.”
23763  MAT 16:22  Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.”
23774  MAT 17:5  Sa'adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi.”
23795  MAT 17:26  Sai Bitrus ya ce, “Daga wurin baki,” Yesu ya ce masa,Wato an dauke wa talakawansu biya kenan.
23797  MAT 18:1  Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Wanene mafi girma a mulkin sama?''
23816  MAT 18:20  Wurin da mutum biyu ko uku suka taru a cikin sunana, zan kasance tare da su.''
23840  MAT 19:9  Ina gaya maku, duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, yana zina kenan. Wanda kuma ya auri macen da aka saka, yana aikata zina.''
23849  MAT 19:18  Mutumin ya ce masa, ''Wadanne dokokin?'' Yesu ya ce masa, ''Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur,
23856  MAT 19:25  Da almajiran sun ji haka, suka yi mamaki kwarai da gaske, suka ce, ''Wanene zai sami ceto?''
23873  MAT 20:12  Suka ce, 'Wadannan da suka zo a karshe, sa'a guda ce kadai suka yi aiki, amma ka ba su daidai da mu, mu da muka yi fama da aiki cikin zafin rana.'
23888  MAT 20:27  Wanda kuma ke da marmari ya zama na farko a cikin ku, ya zama baran ku.
23905  MAT 21:10  Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, Wanene wannan?”
23906  MAT 21:11  Sai jama'a suka amsa,Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili.”
23913  MAT 21:18  Washegari da safe yayin da yake komawa birnin, sai yaji yunwa.
23923  MAT 21:28  Amma me kuke tunani? Wani mutum yana da 'ya'ya biyu. Ya je wurin na farkon yace, 'Da, je ka kayi aiki yau a cikin gona.'
23925  MAT 21:30  Sai mutumin ya je wurin da na biyun ya fada masa abu guda. Wannan dan ya amsa ya ce, 'zanje, baba,' amma bai je ba.
23926  MAT 21:31  Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?” Suka ce, “na farkon.” Yesu ya ce masu, “Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku.
23937  MAT 21:42  Yesu yace masu, “Baku taba karantawa a nassi ba,'' 'Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani. Wannan daga Ubangijine, kuma abin mamaki ne a idanunmu?'
23946  MAT 22:5  Amma mutanen ba su dauki sakon da mahimmanci ba kuma suka yi tafiyarsu. Wani ga gonarsa, wani ga kasuwancinsa.
23979  MAT 22:38  Wannan itace babbar doka ta farko.
24006  MAT 23:19  Ku makafi! Wanene yafi girma, baikon ko kuwa bagadin da yake kebe baikon ga Allah?
24010  MAT 23:23  Kaiton ku Farisawa da marubuta, munafukai! Kukan fitar da zakkar doddoya, da karkashi, da lamsur, amma kun yar da al'amuran attaura mafi nauyi-, wato, hukunci, da jinkai da bangaskiya. Wadannan ne ya kamata kuyi, ba tare da kunyi watsi da sauran ba.
24085  MAT 25:8  Wawayen su ka ce da masu hikimar, 'Ku sammana kadan daga manku gama fitilunmu su na mutuwa.'
24123  MAT 25:46  Wadannan kuwa zasu tafi cikin madawwamiyar azaba amma adalai zuwa rai madawwami.”
24146  MAT 26:23  Sai ya amsa,Wanda ke sa hannu tare da ni cikin kwano daya shi ne zai bada ni.
24180  MAT 26:57  Wadanda suka kama Yesu, suka kai shi wurin Kayafa babban firist, inda marubuta da duttawan jama'a suka taru.
24184  MAT 26:61  sukace ''Wannan mutum yace zan iya rushe haikalin Allah, in kuma gina shi cikin kwana uku.'''
24185  MAT 26:62  Babban Firist din ya tashi tsaye yace masa, “Ba zaka ce komai ba? Wace irin shaida ce ake yi akanka?”
24191  MAT 26:68  sukace, ''Ka yi mana anabci, kai Almasihu. Wanene wanda ya dokeka.
24194  MAT 26:71  Da ya fita zuwa bakin kofa, nan ma wata yarinyar baiwa ta gan shi tace wa wadanda suke wurin, Wannan mutumin ma yana tare da Yesu Banazare.”
24215  MAT 27:17  To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu,Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?”
24219  MAT 27:21  Sai gwamna ya tambayesu,Wa kuke so a sakar maku?” Sukace, “Barabbas.”
24231  MAT 27:33  Suka iso wani wuri da ake kira Golgotta, wanda ke nufin,”Wurin kwalluwa.”
24235  MAT 27:37  A sama da kansa suka sa abinda ake tuhumarsa da ita a rubuce,Wannan shine sarkin Yahudawa.”
24237  MAT 27:39  Wadanda suke wucewa suna zaginsa, suna girgiza kai,
24244  MAT 27:46  Wajen karfe uku, Yesu ya tada murya mai karfi yace, “Eli, Eli lama sabaktani?” wanda ke nufin, “Allahna, Allahna, don me ka yashe ni?”
24260  MAT 27:62  Washegari, wato bayan ranar Shiri, Sai manyan firistoci da Farisawa suka taru tare da Bilatus.
24279  MAT 28:15  Sai sojojin suka karbi kudin suka yi abinda aka umarcesu. Wannan rahoto ya bazu a tsakanin Yahudawa, ya ci gaba har zuwa yau.
24285  MRK 1:1  Wannan itace farkon bisharar Yesu Almasihu, Dan Allah.
24322  MRK 1:38  Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa'azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan''.
24324  MRK 1:40  Wani kuturu ya zo wurinsa. Yana rokonsa, ya durkusa. Ya ce masa, “in ka yarda kana iya warkar da ni.
24359  MRK 3:2  Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi.
24371  MRK 3:14  Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi,
24397  MRK 4:5  Wadansu kuma suka fadi a kan dutse inda ba kasa dayawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin kasa.
24399  MRK 4:7  Wadansu kuma suka fadi cikin kayayuwa su ka yi girma sai kayayuwan suka shake su, ba su yi tsaba ba.
24400  MRK 4:8  Wadansu kuma suka fadi a kasa mai kyau, suka yi yabanya, suka yi tsaba, suka yi girma, wadansu ribi talattin wadansu sittin, wadansu kuma dari”.
24407  MRK 4:15  Wadanda suka fadi a hanyar kuwa, su ne kwatancin wadanda. a aka shuka mganar a zuciyarsu, Da suka ji, nan da nan sai shaidan ya zo ya dauke Maganar da aka shuka a zuciyarsu.
24410  MRK 4:18  Wadansu kuma su ne kwatacin wadanda suka fadi cikin kayayuwa, sune wadanda suka ji Maganar,
24412  MRK 4:20  Wadanda aka shuka a kasa mai kyau kuwa, sune kwatancin wadanda suke jin Maganar, su karba, su kuma yin amfani da ita wadansu ribi talatin, wadansu sittin, wadansu dari.”
24449  MRK 5:16  Wadanda suka zo su ka ga abin da ya faru da mutumin mai aljanun, suka je suka fada wa mutane abin da suka gani game da aladun.
24478  MRK 6:2  Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa?
24479  MRK 6:3  Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu.
24490  MRK 6:14  Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa.
24491  MRK 6:15  Wadansu kuma suna cewa, “Iliya,” Har yanzu wadansu suna cewa daya “daga cikin annabawa ne na da can.”
24524  MRK 6:48  Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su.
24545  MRK 7:13  Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi.”
24597  MRK 8:28  Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, “Iliya”. wadansu kuma, 'Daya daga cikin anabawa”.
24614  MRK 9:7  Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga gajimaren, “ta ce Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi.
24623  MRK 9:16  Ya tambayi almajiransa, “ Wacce muhawara ce kuke yi da su?”
24659  MRK 10:2  Sai Farisawa su ka zo wurinsa, su ka ce, '' dai dai ne mutum ya saki matarsa?'' Wannan tambaya sun yi ta ne domin su gwada shi.
24718  MRK 11:9  Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji.
24743  MRK 12:1  Sai Yesu ya fara koyar da su da misalai.Wani mutum ne ya yi gonar inabi ya shingen ta, ya haka ramin matse inabin, ya kuwa gina hasumayar tsaro. Ya ba wandansu manoma jinginar gonar, sa'an nan ya tafi wata kasa mai nisa.
24753  MRK 12:11  Wannan daga Ubangiji ne, kuma ya yi dai dai a idanunmu.”'