23229 | MAT 1:16 | Yakubu shine mahaifin Yusufu maigidan Maryamu, wadda ta wurin ta ne aka haifi Yesu, wanda ake ce da shi Almasihu. |
23230 | MAT 1:17 | Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne |
23233 | MAT 1:20 | Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. |
23234 | MAT 1:21 | Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.” |
23237 | MAT 1:24 | Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala'ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa. |
23239 | MAT 2:1 | Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, |
23240 | MAT 2:2 | ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.'' |
23244 | MAT 2:6 | 'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.''' |
23247 | MAT 2:9 | Bayan sun ji maganar sarkin, sai suka yi tafiyar su, ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gaban su, har ya zo ya tsaya bisa inda dan yaron nan yake. |
23248 | MAT 2:10 | Da suka ga tauraron, sai suka yi matukar farin ciki. |
23249 | MAT 2:11 | Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur. |
23250 | MAT 2:12 | Allah kuma ya gargade su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma kasarsu ta wata hanya dabam. |
23251 | MAT 2:13 | Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.” |
23253 | MAT 2:15 | Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.'' |
23254 | MAT 2:16 | Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan. |
23257 | MAT 2:19 | Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce, |
23260 | MAT 2:22 | Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili |
23261 | MAT 2:23 | sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat. Wannan ya cika abin da aka fada ta bakin annabawa, cewa, za a kira shi Banazare. |
23264 | MAT 3:3 | Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.'' |
23265 | MAT 3:4 | Yahaya kuwa yana sanye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma daure da damarar fata, abincinsa kuwa fara ne da zuman jeji. |
23266 | MAT 3:5 | Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa. |
23267 | MAT 3:6 | Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu. |
23268 | MAT 3:7 | Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa? |
23270 | MAT 3:9 | Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. |
23271 | MAT 3:10 | Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta. |
23272 | MAT 3:11 | Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. |
23274 | MAT 3:13 | Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma. |
23275 | MAT 3:14 | Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?” |
23277 | MAT 3:16 | Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya fito nan da nan daga cikin ruwan, sai kuma sammai suka bude masa. Ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya, ya sauko a kansa. |
23278 | MAT 3:17 | Duba, wata murya daga sammai tana cewa, ''Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.'' |
23279 | MAT 4:1 | Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi. |
23280 | MAT 4:2 | Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi. |
23281 | MAT 4:3 | Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” |
23282 | MAT 4:4 | Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.''' |
23283 | MAT 4:5 | Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali, |
23284 | MAT 4:6 | ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.''' |
23285 | MAT 4:7 | Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.''' |
23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' |
23293 | MAT 4:15 | “Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! |
23294 | MAT 4:16 | Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.” |
23295 | MAT 4:17 | Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.” |
23296 | MAT 4:18 | Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. |
23299 | MAT 4:21 | Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su. |
23300 | MAT 4:22 | Nan take suka bar mahaifinsu da jirgin, suka bi shi. |
23301 | MAT 4:23 | Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane. |
23303 | MAT 4:25 | Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun. |
23304 | MAT 5:1 | Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa. |
23306 | MAT 5:3 | “Albarka ta tabbata ga masu talauci a ruhu, domin mulkin sama nasu ne. |
23307 | MAT 5:4 | Albarka ta tabbata ga masu makoki, domin za a ta'azantar da su. |
23308 | MAT 5:5 | Albarka ta tabbata ga masu tawali'u, domin za su gaji duniya. |
23309 | MAT 5:6 | Albarka ta tabbata ga masu yunwa da kishin adalci, domin za a kosar da su. |
23310 | MAT 5:7 | Albarka ta tabbata ga masu jinkai, domin za su samu jinkai. |
23311 | MAT 5:8 | Albarka ta tabbata ga masu tsabtar zuciya, domin za su ga Allah. |
23312 | MAT 5:9 | Albarka ta tabbata ga masu kawo salama, domin za a ce da su 'ya'yan Allah. |
23313 | MAT 5:10 | Albarka ta tabbata ga wadanda ake tsananta masu saboda adalci, domin mulkin sama nasu ne. |
23314 | MAT 5:11 | Masu albarka ne ku sa'adda mutane suka zage ku, suka kuma tsananta maku, ko kuwa suka zarge ku da dukan miyagun abubuwa iri iri na karya, saboda ni. |
23315 | MAT 5:12 | Ku yi murna da matukar farin ciki, domin sakamakonku mai yawan gaske ne a sama. Ta haka ne mutane suka tsananta wa annabawa da suka yi rayuwa kafin ku. |
23316 | MAT 5:13 | Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane. |