23214 | MAT 1:1 | Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim. |
23215 | MAT 1:2 | Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da 'yan'uwansa. |
23216 | MAT 1:3 | Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram. |
23217 | MAT 1:4 | Aram shine mahaifin Amminadab, Amminadab shine mahaifin Nashon, Nashon shine mahaifin Salmon. |
23218 | MAT 1:5 | Salmon shine mahaifin Bo'aza ta wurin Rahab, Bo'aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse, |
23219 | MAT 1:6 | Yesse shine mahaifin sarki Dauda. Sarki Dauda shine mahaifin Sulaimanu ta wurin matar Uriya. |
23220 | MAT 1:7 | Sulaimanu shine mahaifin Rehobo'am, Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa. |
23221 | MAT 1:8 | Asa shine mahaifin Yehoshafat, Yehoshafat shine mahaifin Yoram, Yoram kuma shine mahaifin Uziya. |
23222 | MAT 1:9 | Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya. |
23223 | MAT 1:10 | Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya. |
23224 | MAT 1:11 | Yosiya shine mahaifin Yekoniya da 'yan'uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila. |
23225 | MAT 1:12 | Bayan kwasar su zuwa kasar Babila, Yekoniya shine mahaifin Sheyaltiyel, Sheyaltiyel shine mahaifin Zarubabel. |
23226 | MAT 1:13 | Zarubabel shine mahaifin Abihudu, Abihudu shine mahaifin Eliyakim, sannan Eliyakim shine mahaifin Azuru. |
23227 | MAT 1:14 | Azuru shine mahaifin Saduku. Saduku shine mahaifin Akimu, sannan Akimu shine mahaifin Aliyudu |
23228 | MAT 1:15 | Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu. |
23229 | MAT 1:16 | Yakubu shine mahaifin Yusufu maigidan Maryamu, wadda ta wurin ta ne aka haifi Yesu, wanda ake ce da shi Almasihu. |
23230 | MAT 1:17 | Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne |
23231 | MAT 1:18 | Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki. |
23232 | MAT 1:19 | Mijinta, Yusufu, adalin mutum ne, amma ba ya so ya kunyatar da ita a sarari. Sai ya yi shawara ya sake ta a asirce. |
23233 | MAT 1:20 | Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. |
23234 | MAT 1:21 | Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.” |
23236 | MAT 1:23 | “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.” |
23237 | MAT 1:24 | Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala'ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa. |
23238 | MAT 1:25 | Amma Yusufu bai sadu da ita ba sai bayan da ta haifi da. Ya kira sunansa Yesu. |
23239 | MAT 2:1 | Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, |
23240 | MAT 2:2 | ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.'' |
23241 | MAT 2:3 | Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu kwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima. |
23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
23243 | MAT 2:5 | Suka ce masa, ''A Baitalami ne ta kasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta, |
23244 | MAT 2:6 | 'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.''' |
23245 | MAT 2:7 | Sai Hirudus ya kira masanan a asirce ya tambaye su aininhin lokacin da tauraron ya bayyana. |
23246 | MAT 2:8 | Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” |
23247 | MAT 2:9 | Bayan sun ji maganar sarkin, sai suka yi tafiyar su, ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gaban su, har ya zo ya tsaya bisa inda dan yaron nan yake. |
23249 | MAT 2:11 | Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur. |
23250 | MAT 2:12 | Allah kuma ya gargade su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma kasarsu ta wata hanya dabam. |
23251 | MAT 2:13 | Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.” |
23252 | MAT 2:14 | A wannan dare fa Yusufu ya tashi ya dauki dan yaron da mahafiyarsa ya tafi Masar. |
23253 | MAT 2:15 | Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.'' |
23254 | MAT 2:16 | Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan. |