Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   z    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23215  MAT 1:2  Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da 'yan'uwansa.
23216  MAT 1:3  Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram.
23218  MAT 1:5  Salmon shine mahaifin Bo'aza ta wurin Rahab, Bo'aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse,
23221  MAT 1:8  Asa shine mahaifin Yehoshafat, Yehoshafat shine mahaifin Yoram, Yoram kuma shine mahaifin Uziya.
23222  MAT 1:9  Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya.
23223  MAT 1:10  Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya.
23224  MAT 1:11  Yosiya shine mahaifin Yekoniya da 'yan'uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila.
23225  MAT 1:12  Bayan kwasar su zuwa kasar Babila, Yekoniya shine mahaifin Sheyaltiyel, Sheyaltiyel shine mahaifin Zarubabel.
23226  MAT 1:13  Zarubabel shine mahaifin Abihudu, Abihudu shine mahaifin Eliyakim, sannan Eliyakim shine mahaifin Azuru.
23227  MAT 1:14  Azuru shine mahaifin Saduku. Saduku shine mahaifin Akimu, sannan Akimu shine mahaifin Aliyudu
23228  MAT 1:15  Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu.
23230  MAT 1:17  Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne
23234  MAT 1:21  Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.”
23236  MAT 1:23  “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.”
23239  MAT 2:1  Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,
23240  MAT 2:2  ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.''
23242  MAT 2:4  Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?”
23244  MAT 2:6  'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.'''
23247  MAT 2:9  Bayan sun ji maganar sarkin, sai suka yi tafiyar su, ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gaban su, har ya zo ya tsaya bisa inda dan yaron nan yake.
23249  MAT 2:11  Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur.
23251  MAT 2:13  Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.”
23253  MAT 2:15  Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.''
23254  MAT 2:16  Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan.
23256  MAT 2:18  ''An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su.
23259  MAT 2:21  Yusufu ya tashi, ya dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ya zo kasar Isra'ila.
23260  MAT 2:22  Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili
23261  MAT 2:23  sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat. Wannan ya cika abin da aka fada ta bakin annabawa, cewa, za a kira shi Banazare.
23262  MAT 3:1  A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa,
23265  MAT 3:4  Yahaya kuwa yana sanye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma daure da damarar fata, abincinsa kuwa fara ne da zuman jeji.
23266  MAT 3:5  Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa.
23267  MAT 3:6  Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu.
23268  MAT 3:7  Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa?
23269  MAT 3:8  Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tubanku.
23271  MAT 3:10  Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.
23272  MAT 3:11  Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.
23273  MAT 3:12  Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.”
23274  MAT 3:13  Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma.
23275  MAT 3:14  Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?”
23276  MAT 3:15  Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci.” Sai Yahaya ya yarje masa.
23279  MAT 4:1  Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi.
23280  MAT 4:2  Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi.
23281  MAT 4:3  Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”
23282  MAT 4:4  Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.'''
23287  MAT 4:9  Ya ce masa, “Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada.''
23288  MAT 4:10  Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.'''
23289  MAT 4:11  Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima.
23290  MAT 4:12  To, da Yesu ya ji an kama Yahaya, sai ya tashi zuwa kasar Galili.
23291  MAT 4:13  Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali.
23294  MAT 4:16  Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.”
23295  MAT 4:17  Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.”
23297  MAT 4:19  Yesu ya ce masu, “Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane.”
23301  MAT 4:23  Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane.
23302  MAT 4:24  Labarinsa ya bazu a cikin dukan kasar Suriya, kuma mutanen suka kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farfadiya, da shanyayyu. Yesu ya warkar da su.
23304  MAT 5:1  Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa.
23307  MAT 5:4  Albarka ta tabbata ga masu makoki, domin za a ta'azantar da su.
23308  MAT 5:5  Albarka ta tabbata ga masu tawali'u, domin za su gaji duniya.
23309  MAT 5:6  Albarka ta tabbata ga masu yunwa da kishin adalci, domin za a kosar da su.
23310  MAT 5:7  Albarka ta tabbata ga masu jinkai, domin za su samu jinkai.
23311  MAT 5:8  Albarka ta tabbata ga masu tsabtar zuciya, domin za su ga Allah.
23312  MAT 5:9  Albarka ta tabbata ga masu kawo salama, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.
23314  MAT 5:11  Masu albarka ne ku sa'adda mutane suka zage ku, suka kuma tsananta maku, ko kuwa suka zarge ku da dukan miyagun abubuwa iri iri na karya, saboda ni.
23316  MAT 5:13  Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane.
23318  MAT 5:15  Mutane ba za su kunna fitila su sa ta karkashin kwando ba, sai ko a dora ta a mazaunin ta, domin ta ba da haske ga kowa da ke gidan.
23319  MAT 5:16  Bari hasken ku ya haskaka gaban mutane yadda za su ga kyawawan ayyukanku su kuma yabi Ubanku da ke cikin sama.
23320  MAT 5:17  Kada ku yi tsammanin na zo ne domin in rushe shari'a ko annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, amma domin in cika su.
23321  MAT 5:18  Domin gaskiya ina gaya maku, har sama da kasa su shude, amma digo ko wasali daya ba za ya shude ba a cikin shari'ar, sai an cika dukan al'amura.
23322  MAT 5:19  Saboda haka duk wanda ya karya mafi kankanta daga cikin dokokin nan ko kuwa ya koya wa wasu su yi haka, za a kira shi mafi kankanta a cikin mulkin sama. Amma dukan wanda ya kiyaye su ko kuwa ya koyar da su, za a kira shi mafi girma a cikin mulkin sama.
23323  MAT 5:20  Gama ina gaya maku cewa idan adalcin ku bai zarce adalcin marubuta da Farisawa ba, babu yadda za ku shiga mulkin sama.
23325  MAT 5:22  Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama.
23326  MAT 5:23  Saboda haka idan za ka yi baiko a bagadi sai ka tuna cewa dan'uwanka yana da damuwa da kai,
23327  MAT 5:24  ka bar baikon ka a gaban bagadin, ka yi tafiyarka. Da farko dai, ka sasanta da dan'uwanka kafin ka zo ka mika baikon.