Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   Word!    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23288  MAT 4:10  Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.'''
23374  MAT 6:23  Amma in idonka na da lahani, dukan jiki na cike da duhu. Saboda haka, in hasken da yake cikinka duhu ne, ina misalin yawan duhun!
23390  MAT 7:5  Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka.
23408  MAT 7:23  Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!'
23427  MAT 8:13  Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke.
23511  MAT 10:25  Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa!
23549  MAT 11:21  “Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka.
23570  MAT 12:12  Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci.”
23693  MAT 14:27  Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.”
23764  MAT 16:23  Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.”
23803  MAT 18:7  Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo!
23904  MAT 21:9  Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, “Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!”
24000  MAT 23:13  Amma kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kun toshewa mutane kofar mulkin sama. Baku shiga ba, kuma ba ku bar wadanda suke so su sami shiga ba.
24002  MAT 23:15  Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kuna tafiya ketaren tekuna da kasashe domin samun almajiri daya tak, in kwa kun samu kukan mai da shi biyunku danwuta.
24004  MAT 23:17  Ku wawayen makafi! wanene yafi girma, zinariyar ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?
24006  MAT 23:19  Ku makafi! Wanene yafi girma, baikon ko kuwa bagadin da yake kebe baikon ga Allah?
24010  MAT 23:23  Kaiton ku Farisawa da marubuta, munafukai! Kukan fitar da zakkar doddoya, da karkashi, da lamsur, amma kun yar da al'amuran attaura mafi nauyi-, wato, hukunci, da jinkai da bangaskiya. Wadannan ne ya kamata kuyi, ba tare da kunyi watsi da sauran ba.
24011  MAT 23:24  Makafin jagora, ku kan burtsar da kwaro dan mitsil, amma kukan hadiye rakumi!
24012  MAT 23:25  Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! kuna wanke bayan moda da kwano, amma aciki cike suke da zalunci da keta.
24013  MAT 23:26  Kai makahon Bafarise! Sai ka fara tsarkake cikin modar da kwanon domin bayansu ma su tsarkaka.
24014  MAT 23:27  Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar kasa kuke, masu kyaun gani daga waje, daga ciki kuwa sai kasusuwan matattu da kazanta iri iri.
24016  MAT 23:29  Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Ku kan gina kaburburan annabawa, kuna kuma kawata kaburburan adalai.
24019  MAT 23:32  Sai kuma kuka cika ma'aunin ubanninku!
24024  MAT 23:37  Urushalima, Urushalima, keda kika kashe annabawa kika kuma jejjefi wadanda aka turo maki da duwatsu! Sau nawa ne naso in tattaro ki kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fukafukanta, amma kin ki.
24025  MAT 23:38  Ga shi an bar maku gidan ku a yashe!
24045  MAT 24:19  Amma kaito ga wadanda suke dauke da yaro, ko masu shayarwa a wannan kwanakin!
24083  MAT 25:6  Amma da tsakkar dare sai aka yi shela, 'Ga ango ya iso! Ku fito taryensa.
24098  MAT 25:21  Maigidansa yace masa, 'Madalla, bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abu kadan. Zan sa ka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.'
24100  MAT 25:23  Ubangidansa yace masa, 'Madalla, kai bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abubuwa kadan. Zan saka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.'
24147  MAT 26:24  Dan mutum zai tafi, kamar yadda aka rubuta akan sa. Amma kaiton mutumin da ta wurin sa za'a bada Dan mutum! Gwamma da ba'a haifi mutumin nan ba.”
24188  MAT 26:65  Sai babban firist din ya yayyaga rigarsa, yana cewa, “Yayi sabo! don me ku ke neman wata shaida kuma? Duba, yanzu kun ji sabon.
24238  MAT 27:40  suna kuma cewa, “Kai da kace zaka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, ka ceci kanka mana! In dai kai Dan Allah ne, ka sauko daga gicciyen!”
24336  MRK 2:7  Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi “sai Allah kadai?”
24391  MRK 3:34  Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, “Ga uwa-ta da yan-uwana anan!
24395  MRK 4:3  “ku saurara! wani mai shuka ya tafi shuka.
24431  MRK 4:39  Sai ya farka, ya tsawata wa Iskar. Ya kuma ce wa ruwan tekun, “Ka natsu! ka yi shiru!” Sai Iskar ta kwanta, wurin duk ya yi shiru.
24526  MRK 6:50  gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, “Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!''
24706  MRK 10:49  Yesu ya tsaya ya ce, ku kirawo shi. Su kuwa suka kirawo makahon suka ce masa. ''Albishrinka, ta so! Yana kiranka.''
24719  MRK 11:10  Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na Ubanmu Dawuda! Dukaka a cikin sama!”
24730  MRK 11:21  Bitrus kuwa ya tuna ya ce “Malam, dubi! Baurenan da ka la'anta ya bushe.”
24844  MRK 14:21  Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! “zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba”.
24864  MRK 14:41  Ya sake komowa karo na uku yace masu “har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi”.
24887  MRK 14:64  Kun dai ji sabon da yayi! Me kuka gani? Duk suka yanke masa hukunci akan ya cancanci kisa.
24948  MRK 16:6  Sai ya ce masu, “Kada ku ji tsoro. Kuna neman Yesu banazare, wanda aka giciye. Ya tashi! Baya nan. Ku duba wurin da aka kwantar dashi.
24990  LUK 1:28  Ya zo wurin ta ya ce, “A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke.
25053  LUK 2:11  Yau an haifi maku mai ceto a cikin birnin Dauda! Shine Almasihu Ubangiji!
25098  LUK 3:4  Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, “Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa!
25166  LUK 4:34  “Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!”
25239  LUK 6:24  Amma kaitonku mawadata! Domin kun rigaya kun samu ta'aziyar ku.
25240  LUK 6:25  Kaitonku kosassu a yanzu! Domin za ku ji yunwa nan gaba. Kaitonku masu dariya yanzu! Domin za ku yi makoki kuna kuka nan gaba.
25241  LUK 6:26  Kaiton ku idan kowadanne mutane suna yabon ku! Domin haka kakannin-kakanninsu suka yi wa annabawan karya.
25257  LUK 6:42  Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka.
25298  LUK 7:34  Dan Mutum, ya zo, yana ci, yana sha, amma, kuka ki shi, kuna cewa dubi mutum mai hadama, mai shan ruwan inabi da yawa, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!
25338  LUK 8:24  Sai almajiran Yesu su ka zo su ka tashe shi daga barci. Suka ce da shi, “Ya Shugaba! Ya Shugaba! Za mu mutu!” Sai ya tashi ya umarci iskar, sai iskar mai hauka da tumbatsar ruwan sun tsaya tsit.
25348  LUK 8:34  Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen.
25366  LUK 8:52  Dukan mutane a wurin, suna ta kuka da karfi saboda sun damu da yarinyar ta mutu. Amma Yesu ya ce da su, “Ku dena kuka! Ba mutuwa ta yi ba! Barci ta ke yi kawai!”
25387  LUK 9:17  Dukansu suka ci kowa ya koshi. Daga nan almajiran suka tattara sauran abin da ya rage, har kwanduna goma sha biyu suka cika!
25443  LUK 10:11  'Ko kurar birninku da ta like a kafafunmu, mun karkabe maku ita a matsayin shaida a kanku! Amma ku sani mulkin Allah ya zo kusa da ku.'
25445  LUK 10:13  Kaiton ki, Korasinu! Kaiton ki, Baitsaida! Ayyuka masu girma da aka yi a cikinku, da an yi su a cikin Taya da Sidon, da sun tuba tuntuni a zaune cikin toka da tufafin makoki.
25488  LUK 11:14  Wani lokaci, Yesu yana fitar da wani beben aljani. Sa'adda aljanin ya fita, sai mutumin da yake bebe ya yi magana. Sai taron mutanen suka yi mamaki!
25552  LUK 12:24  Ku dubi hankaki wadanda ba sa yin shuka, ba sa yin girbi. Ba su da rumbuna ko dakunan ajjiya, amma Allah ya na ciyar da su. Ku fa kun fi tsuntsaye daraja!
25556  LUK 12:28  Idan Allah ya sa wa ciyawa tufafi masu kyau haka, wadda yau tana nan, gobe kuma a sa ta a wuta, ta yaya zai kasa sa maku tufafi, ku masu kankantar bangaskiya!
25578  LUK 12:50  Amma ni, ina da baftisma wadda za a yi mani baftisma da ita, kuma na kagara, da an riga an yi ta!
25674  LUK 15:17  Amma da hankalinsa ya dawo, ya ce, 'Barorin mahaifina su nawa ne da suke da abinci isasshe, amma ina nan a nan, ina mutuwa sabili da yunwa!
25680  LUK 15:23  Sa'annan a kawo kiwataccen marakin nan, a yanka. Mu yi buki!
25721  LUK 17:1  Sai Yesu ya ce wa almajiransa, 'Babu shakka akwai sanadodin tuntube da za su sa mu yin zunubi amma kaiton wanda shine sanadin su!
25743  LUK 17:23  Za su ce maku, 'Duba can! 'Duba nan!' Amma kada ku je kuna dubawa, ko kuwa ku bi su.
25781  LUK 18:24  Yesu kuwa, da ya ga ransa ya baci, sai ya ce, “Yana da wuya masu dukiya su shiga mulkin Allah!
25838  LUK 19:38  cewa, “Albarka ta tabbata ga sarki da ke zuwa cikin sunan Uba! Salama a sama da daraja mafi daukaka kuma!”
25842  LUK 19:42  cewa, “Da kun san wannan rana, ko ku ma, abubuwan da ke kawo maku salama! Amma yanzu an boye su daga idanunku.
25918  LUK 21:23  Kaiton wadanda suke da juna biyu da masu ba da mama a wannan kwanakin! Gama za a sha kunci mai girma a kasan, da fushi kuma zuwa ga mutanen nan.
25971  LUK 22:38  Sai suka ce, “Ubangiji, duba! Ga takuba biyu.” Sai ya ce masu, “Ya isa.”
25997  LUK 22:64  Bayan da suka rufe masa idanu, suka tambaye shi, cewa, “Ka yi annabci! Wa ya buge ka?”
26066  LUK 24:6  Baya nan, amma ya tashi! Ku tuna fa yadda ya yi maku magana tun sa'adda ya ke Galili,
26085  LUK 24:25  Yesu ya ce masu, “Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada!
26142  JHN 1:29  Washegari, Yahaya ya ga Yesu yana zuwa wurinsa ya ce, “Duba, ga Dan Ragon Allah wanda ke dauke zunubin duniya!
26162  JHN 1:49  Natana'ilu ya amsa, “Rabbi, Kai Dan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!”
26346  JHN 6:20  Amma ya ce masu, “Ni ne! kada ku firgita.”
26536  JHN 9:27  Ya amsa, “ Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne?
26824  JHN 16:29  Almajiransa sukace, duba, “Yanzu kake magana a sarari, ba cikin karin magana ba!
26897  JHN 19:3  Suka zo wurin sa sukace, “Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi.
27210  ACT 7:25  zaton Musa 'yan'uwansa za su fahimci taimakon Allah ne ya zo masu amma ina! Basu gane ba.
27354  ACT 10:26  Amma Bitrus ya tashe shi yana cewa, “Tashi tsaye! Ni ma mutum ne.”
28057  ROM 2:27  Sannan idan mutum marar kaciya ta jini zai kiyaye dukkan dokoki, ba zai iya shara'anta ku masu kaciya ta shari'a ba? Haka kuma ya kasance ne domin kuna da shari'a a rubuce da kuma kaciya amma ba kwa bin doka!
28153  ROM 6:17  Amma godiya ta tabbata ga Allah! domin da ku bayin zunubi ne, amma kun yi biyayya daga zuciyarku irin salon koyarwar da aka baku.
28183  ROM 7:24  Ni wahalallen mutum ne! wa zai kubutar dani daga wannan jiki na mutuwa?
28184  ROM 7:25  Amma godiya ga Allah ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Domin haka ni kaina a wannan hannu bisa ga tunani na ina bautawa shari'ar Allah. Duk da haka, ta wani gefen ina bautawa ka'idar zunubi da ke tare da jikina.
28297  ROM 11:20  Wannan gaskiya ne! Saboda rashin bangaskiyarsu ne ya sa aka karye su daga rassan, amma ku tsaya da karfi acikin bangaskiyarku. Kada ku dauki kanku fiye da yadda ya kamata, amma ku ji tsoro.
28310  ROM 11:33  Ina misalin zurfin wadata da kuma hikima da sani na Allah! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban a bincika, hanyoyinsa kuma sun fi gaban ganewa!
28499  1CO 3:21  haka ba sauran fariya akan mutane! Domin kuwa kome naku ne,
28509  1CO 4:8  Kun rigaya kun sami dukkan abubuwan da kuke bukata! Kun rigaya kun zama mawadata! Kun rigaya kun fara mulki- kuma ba tare da mu ba! Hakika, marmarina shine ku yi mulki, domin mu yi mulki tare da ku.
28524  1CO 5:2  Kuma kuna fahariya sosai! Ba bakinciki ya kamata ku yi ba? Shi wanda ya yi haka, dole a fitar da shi daga cikin ku.
28541  1CO 6:6  Amma kamar yadda yake, mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba!
28543  1CO 6:8  Amma kun yi wa wadansu laifi kun kuma cutar su, su kuwa 'yan'uwanku ne!
28550  1CO 6:15  Ba ku sani ba jikunanku gabobi ne na Almasihu? Na dauki gabobin Almasihu in hada su da karuwa? Allah ya sawwake!
28553  1CO 6:18  Ku gujewa fasikanci! Kowane zunubi mutum yake aikatawa a waje da jikinsa yake, amma mutum mai fasikanci yana zunubi gaba da jikinsa.
28688  1CO 11:20  Domin, in kun taru a wuri daya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!
28820  1CO 15:34  “Ku natsu! kuyi zaman adalci! kada ku cigaba da zunubi. Domin wasunku basu da sanin Allah. Ina fadar wannan domin in baku kunya.
28822  1CO 15:36  Ku jahilai ne sosai! Abinda ka shuka ba zaya fara girma ba sai ya mutu.
28837  1CO 15:51  Duba! ina gaya maku asirtacciyar gaskiya: Ba dukanmu zamu mutu ba, amma dukanmu za a canza mu.