23911 | MAT 21:16 | Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?'' Yesu ya ce masu, “I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?” |
24718 | MRK 11:9 | Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji. |
24924 | MRK 15:29 | suke wucewa suna zaginsa suna kada kai suna cewa, “Aha! kai da zaka rushe haikali ka kuma gina shi cikin kwana uku, |
25602 | LUK 13:15 | Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe kowannenku ba ya kwance Jakinsa ko Sa daga turkensa ya kai shi banruwa ran Asabaci? |
26662 | JHN 12:13 | Sai suka dauki ganyen dabino suka fita gari suka tare shi da kira mai karfi suna cewa, “Hosanna! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila. |
27498 | ACT 14:15 | Suna ta cewa, “Kuji! Ku mutane don me kuke wannan abin? Mu fa mutane ne kamarku. Mun kawo maku labari mai dadi ne, da cewa, ku rabu da abubuwa marar amfani, ku koma ga Allah mai rai, wanda ya hallici sama da kasa da teku da dukan abubuwa da ke cikinsu. |
30890 | REV 7:12 | suna cewa, “Amin! yabo, daukaka, hikima, godiya, girma, iko, da karfi su zama na Allahnmu har abada abadin! Amin!” |
31089 | REV 19:3 | Suka yi magana a karo na biyu: “Halleluya! Hayaki na tasowa daga wurinta har abada abadin.” |
31092 | REV 19:6 | Sai na ji murya kamar na kasaitaccen taron mutane, kamar rurin kogi na ruwaye masu yawa, kuma kamar tsawar aradu, cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji yana mulki, Allah mai iko duka. |
31125 | REV 21:3 | Na ji babbar murya daga kursiyinta na cewa, “Duba! Mazaunin Allah yana tare da 'yan adam, zai zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kuma da kansa zai kasance tare da su ya kuma zama Allahnsu. |
31127 | REV 21:5 | Shi wanda yake zaune a kan kursiyin ya ce, “Duba! Na maida kome ya zama sabo.” Ya ce, “Ka rubuta wannan domin wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya”. |
31156 | REV 22:7 | “Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba! Mai albarka ne wanda ya yi biyayya da kalmomin littafin nan.” |
31161 | REV 22:12 | “Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba. Sakamakona na tare da ni, zan saka wa kowa gwargwadon aikin da ya yi. |
31169 | REV 22:20 | Shi wanda ya shaida wadannan abubuwa ya ce, “I! Ina zuwa ba da dadewa ba.” Amin! Zo, Ubangiji Yesu! |