Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   Word'Word    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23218  MAT 1:5  Salmon shine mahaifin Bo'aza ta wurin Rahab, Bo'aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse,
23220  MAT 1:7  Sulaimanu shine mahaifin Rehobo'am, Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa.
23228  MAT 1:15  Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu.
23233  MAT 1:20  Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi.
23237  MAT 1:24  Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala'ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa.
23244  MAT 2:6  'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.'''
23249  MAT 2:11  Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur.
23251  MAT 2:13  Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.”
23257  MAT 2:19  Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce,
23262  MAT 3:1  A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa,
23279  MAT 4:1  Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi.
23280  MAT 4:2  Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi.
23283  MAT 4:5  Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali,
23284  MAT 4:6  ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.'''
23289  MAT 4:11  Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima.
23296  MAT 4:18  Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne.
23299  MAT 4:21  Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su.
23304  MAT 5:1  Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa.
23307  MAT 5:4  Albarka ta tabbata ga masu makoki, domin za a ta'azantar da su.
23314  MAT 5:11  Masu albarka ne ku sa'adda mutane suka zage ku, suka kuma tsananta maku, ko kuwa suka zarge ku da dukan miyagun abubuwa iri iri na karya, saboda ni.
23320  MAT 5:17  Kada ku yi tsammanin na zo ne domin in rushe shari'a ko annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, amma domin in cika su.
23325  MAT 5:22  Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama.
23326  MAT 5:23  Saboda haka idan za ka yi baiko a bagadi sai ka tuna cewa dan'uwanka yana da damuwa da kai,
23327  MAT 5:24  ka bar baikon ka a gaban bagadin, ka yi tafiyarka. Da farko dai, ka sasanta da dan'uwanka kafin ka zo ka mika baikon.
23343  MAT 5:40  Idan wani yana da niyyar kai kararku gaban shari'a saboda ya karbi rigarku, ku ba wannan mutumin mayafinku ma.
23347  MAT 5:44  Amma ina gaya maku, ku kaunaci magabtan ku, ku yi addu'a domin masu tsananta maku, ku albarkaci wadanda suka la'ance ku, ku yi alheri ga wadanda suke kin ku,
23350  MAT 5:47  Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba?
23353  MAT 6:2  Saboda haka, in za ku yi sadaka, kada ku busa kaho yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma akan tituna domin mutane su yabesu. Gaskiya ina gaya maku, sun samu ladansu.
23356  MAT 6:5  Sa'adda za ku yi addu'a kuma, kada ku zama kamar munafukai, domin sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'unsu da kuma a gefen tituna, domin mutane su gansu. Gaskiya ina gaya maku, sun sami ladarsu kenan.
23357  MAT 6:6  Amma ku, idan za ku yi addu'a, sai ku shiga cikin daki. Ku rufe kofa, ku yi addu'a ga Ubanku wanda yake a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku.
23358  MAT 6:7  Idan za ku yi addu'a, kada ku yi ta maimaici marar anfani, kamar yadda al'ummai suke yi, domin a tunanin su za a saurare su saboda yawan maganganunsu.
23360  MAT 6:9  Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka: 'Ubanmu da ke sama, bari a tsarkake sunanka.
23383  MAT 6:32  Ai, al'ummai ma suna neman dukan irin wadannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.
23390  MAT 7:5  Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka.
23391  MAT 7:6  Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa aladu, lu'u lu'anku. Idan ba haka ba za su tattake su a karkashin sawunsu, su kuma juyo su kekketa ku.
23397  MAT 7:12  Saboda haka, duk abinda ku ke so mutane su yi maku, ku ma sai ku yi masu, domin wannan shi ne dukan shari'a da koyarwar annabawa.
23408  MAT 7:23  Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!'
23413  MAT 7:28  Ya zama sa'adda Yesu ya gama fadin wadannan maganganu, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa,
23424  MAT 8:10  Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba.
23427  MAT 8:13  Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke.
23432  MAT 8:18  Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili.
23440  MAT 8:26  Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit.
23442  MAT 8:28  Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya.
23445  MAT 8:31  Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”
23448  MAT 8:34  Sai duk jama'ar gari suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, suka roke shi ya bar kasarsu.
23458  MAT 9:10  Sa'adda kuma Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karbar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa.
23461  MAT 9:13  Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, 'Ni kam, ina bukatar jinkai ba hadaya ba.' Ba domin in kira masu adalci su tuba na zo ba, sai dai masu zunubi.
23463  MAT 9:15  Sai Yesu ya ce masu, ''Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi.''
23466  MAT 9:18  Yesu kuwa yana cikin yi masu magana sai ga wani shugaban jama'a ya zo ya yi masa sujada, ya ce, ''Yanzun nan 'yata ta rasu, amma ka zo ka dora mata hannu, za ta rayu.''
23473  MAT 9:25  Sa'adda aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta shi.
23481  MAT 9:33  Bayan da an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, su ka ce, ''Kai, ba a taba ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba!''
23485  MAT 9:37  Sai ya ce wa almajiransa, ''Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan kadan ne.
23486  MAT 9:38  Saboda haka sai ku yi sauri ku roki Ubangijin girbin ya turo ma'aikata cikin girbinsa.''
23488  MAT 10:2  To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya;
23493  MAT 10:7  Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'.
23496  MAT 10:10  Kada kuma ku dauki zabira a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci abincin sa.
23501  MAT 10:15  Hakika, ina gaya maku, a ranar shari'a za a fi rangwanta wa kasar Saduma da ta Gwamrata a kan wannan birni.
23507  MAT 10:21  Dan'uwa zai ba da dan'uwansa a kashe shi, uba kuwa dansa. 'Ya'ya kuma za su tayarwa iyayensu, har su sa a kashe su.
23535  MAT 11:7  Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa?
23541  MAT 11:13  Gama dukan annabawa da shari'a sun yi annabci har zuwa lokacin Yahaya.
23550  MAT 11:22  Amma zai zama da sauki a kan Taya da Sidon a ranar shari'a fiye da ku.
23551  MAT 11:23  Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu.
23552  MAT 11:24  Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku.”
23557  MAT 11:29  Ku dauki karkiya ta ku koya daga gare ni, gama ni mai tawali'u ne da saukin hali a zuciya, sannan zaku sami hutawa ga rayukanku.
23563  MAT 12:5  Sa'annan ba ku karanta cikin shari'a cewa, a ranar Asabaci, Firistoci da ke cikin haikali na sabawa ranar Asabaci, amma kamar ba su yi laifi ba?
23565  MAT 12:7  In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba.
23567  MAT 12:9  Sa'annan Yesu ya bar wannan wuri, ya shiga majami'ar su.
23569  MAT 12:11  Yesu ya ce masu, “Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba?
23579  MAT 12:21  Sa'annan al'ummai za su dogara a ga sunansa.
23580  MAT 12:22  Sa'annan wani mutum, makaho ne, kurma kuma, aljannu kuma na cikinsa, an kawo shi wurin Yesu. Ya warkar da shi, ya sami ganin gari ya kuma yi magana.
23581  MAT 12:23  Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?”
23585  MAT 12:27  Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku.
23587  MAT 12:29  Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa.
23594  MAT 12:36  Sa'annan ina ce maku a ranar shari'a, mutane za su bada lissafin abubuwan banza da su ka fadi.
23596  MAT 12:38  Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, “Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”
23599  MAT 12:41  Mutanen Nineba za su tsaya a ranar shari'a da wannan zamani sannan su kashe su. Domin sun tuba da suka ji wa'azin Yunusa, amma duba wanda ya fi Yunusa yana nan.
23603  MAT 12:45  Sai ya koma ya kawo wadansu ruhohi guda bakwai, wadanda su ka fi shi mugunta, sa'annan dukan su su zo su zauna a nan. Sa'annan yanayin mutumin nan na karshe ya fi na farko muni. Haka zaya kasance ga wannan mugun zamani.
23604  MAT 12:46  Sa'adda Yesu ya ke yi wa Jama'a jawabi, sai mahaifiyarsa da 'yan'uwansa su ka zo su ka tsaya a waje, suna neman su yi magana da shi.
23634  MAT 13:26  Sa'adda suka yi toho suka kuma ba da tsaba, sai ciyayin suka bayyana.
23651  MAT 13:43  Sa'an nan ne mutane masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, ya ji.
23657  MAT 13:49  Haka zai kasance a karshen duniya. Mala'iku za su zo su ware miyagu daga cikin masu adalci.
23661  MAT 13:53  Daga nan, sa'adda Yesu ya kammala ba da wadanan misalai, sai ya tafi ya bar wurin.
23666  MAT 13:58  Kuma bai yi al'ajibai dayawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.
23669  MAT 14:3  Domin Hiridus ya kama Yahaya, ya daure shi, kuma ya jefa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar dan'uwansa Filibus.
23679  MAT 14:13  Sa'adda da Yesu ya ji haka, ya fita daga cikin kwale-kwale zuwa wani kebabben wuri. Da taron suka ji haka, suka bi shi da kafa daga biranen.
23704  MAT 15:2  “Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.”
23714  MAT 15:12  Sai al'majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?”
23724  MAT 15:22  Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.”
23739  MAT 15:37  Jama'a duka suka ci suka koshi. Suka tattara gutsattsarin abincin da ya rage, kwando bakwai cike.
23753  MAT 16:12  Sa'annan suka fahimta cewa ba yana gaya masu su yi hankali da yistin da ke cikin gurasa ba ne, amma sai dai su yi lura da koyarwar Farisawa da Sadukiyawa.
23765  MAT 16:24  Sa'annan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk wanda yake so ya bi ni, lallai ne ya ki kansa, ya dauki gicciyensa, ya bi ni.
23768  MAT 16:27  Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa.
23774  MAT 17:5  Sa'adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, “Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi.”
23782  MAT 17:13  Sa'annan almajiransa suka fahimci cewa yana yi masu magana a kan Yahaya mai Baftisma ne.
23790  MAT 17:21  [Irin wannan aljanin bashi fita sai tare da addu'a da azumi].
23806  MAT 18:10  Ku kula fa kada ku rena kananan nan. Domin koyaushe a sama, mala'ikunsu na duban fuskar Ubana da ke sama.
23808  MAT 18:12  Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba?
23809  MAT 18:13  In ya same ta, hakika ina gaya maku, farin cikinsa na samun dayan nan da ta bace, zai fi na tassa'in da taran nan da basu bata ba.
23811  MAT 18:15  Idan dan'uwanka yayi maka laifi, fada masa tsakaninku, kai da shi kadai. Idan ya saurare ka, ka maido da dan'uwanka kenan.
23817  MAT 18:21  Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?''