23220 | MAT 1:7 | Sulaimanu shine mahaifin Rehobo'am, Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa. |
23228 | MAT 1:15 | Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu. |
23233 | MAT 1:20 | Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. |
23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
23256 | MAT 2:18 | ''An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su. |
23258 | MAT 2:20 | ''Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu.'' |
23295 | MAT 4:17 | Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.” |
23301 | MAT 4:23 | Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane. |
23304 | MAT 5:1 | Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa. |
23308 | MAT 5:5 | Albarka ta tabbata ga masu tawali'u, domin za su gaji duniya. |
23321 | MAT 5:18 | Domin gaskiya ina gaya maku, har sama da kasa su shude, amma digo ko wasali daya ba za ya shude ba a cikin shari'ar, sai an cika dukan al'amura. |
23325 | MAT 5:22 | Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. |
23328 | MAT 5:25 | Ka yi sulhu da mai karar ka tun kana hanyar zuwa gaban shari'a, domin kada mai karar ka ya mika ka ga alkali, alkali kuwa ya mika ka ga dogarai, za a kuwa jefa ka a kurkuku. |
23331 | MAT 5:28 | Amma ina gaya maku, duk wanda ya dubi mace, da muguwar sha'awa, ya riga ya yi zina da ita a zuciyarsa. |
23357 | MAT 6:6 | Amma ku, idan za ku yi addu'a, sai ku shiga cikin daki. Ku rufe kofa, ku yi addu'a ga Ubanku wanda yake a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku. |
23358 | MAT 6:7 | Idan za ku yi addu'a, kada ku yi ta maimaici marar anfani, kamar yadda al'ummai suke yi, domin a tunanin su za a saurare su saboda yawan maganganunsu. |
23388 | MAT 7:3 | Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba? |
23389 | MAT 7:4 | Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon? |
23441 | MAT 8:27 | Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”. |
23471 | MAT 9:23 | Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya sosai. |
23483 | MAT 9:35 | Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da kauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. |
23491 | MAT 10:5 | Sha biyun nan su ne Yesu ya aika, ya yi masu umarni ya ce, ''Kada ku shiga wajen al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. |
23493 | MAT 10:7 | Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'. |
23509 | MAT 10:23 | In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo. |
23511 | MAT 10:25 | Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa! |
23582 | MAT 12:24 | Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, “Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.” |
23585 | MAT 12:27 | Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku. |
23594 | MAT 12:36 | Sa'annan ina ce maku a ranar shari'a, mutane za su bada lissafin abubuwan banza da su ka fadi. |
23608 | MAT 12:50 | Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.” |
23649 | MAT 13:41 | Dan Mutum zai aiki mala'ikunsa, kuma su tara dukan abubuwan da ke sa zunubi daga cikin mulkinsa, da kuma wadanda su ka yi aikin mugunta. |
23671 | MAT 14:5 | Da Hirudus ya kashe shi, amma yana tsoron jama'a, domin sun dauke shi a matsayin annabi. |
23770 | MAT 17:1 | Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus da Yakubu, da Yahaya dan'uwansa, ya kai su kan wani dutse mai tsawo su kadai. |
23844 | MAT 19:13 | Sai aka kawo masa yara kanana don ya dibiya hannuwansa akansu, yayi masu addu'a, amma almajiran suka kwabe su. |
23880 | MAT 20:19 | za su kuma bada shi ga al'ummai don suyi masa ba'a, su bulale shi, su kuma gicciye shi. Amma a rana ta uku, za a tada shi.'' |
23917 | MAT 21:22 | Kome kuka roka cikin addu'a, in dai kun gaskanta, za ku samu.” |
23921 | MAT 21:26 | Amma in munce, ' daga mutune,' muna tsoron jama'a, saboda sun san Yahaya annabi ne.” |
23976 | MAT 22:35 | Daya daga cikinsu, masanin shari'a, yayi masa tambaya, yana gwada shi- |
23993 | MAT 23:6 | Su na son mafifitan wuraren zama a gidan biki, da mafifitan wuraren zama a majami'u, |
24033 | MAT 24:7 | Gama al'umma zata tayarwa al'umma, kuma mulki zai tayarwa mulki. Za'a yi yunwa da girgizar kasa a wurare dabam dabam. |
24050 | MAT 24:24 | Gama annabawan karya da almasihan karya za su zo suna nuna alamu da al'ajibai, don su yaudari masu yawa zuwa ga bata, in ya yiwuma har da zababbun. |
24057 | MAT 24:31 | Zai aiki mala'ikunsa, da karar kaho mai karfi, kuma za su tattara dukkan zababbu daga dukkan kusurwoyi hudu, daga karshen sararin sama har zuwa wani karshen. |
24109 | MAT 25:32 | A gabansa za'a tattara dukkan al'ummai, zai rarraba mutanen daya'daya, kamar yadda makiyayi yake rarraba tumaki daga awaki. |
24118 | MAT 25:41 | Sa'annan zai cewa wadanda suke hannunsa na hagu, 'Ku rabu da ni, ku la'anannu, ku tafi cikin wutar jahannama da aka shirya wa Shaidan da aljannunsa, |
24165 | MAT 26:42 | Sai ya koma karo na biyu yayi addu'a, Yace, “Ya Ubana, in wannan kokon ba zai wuce ba sai na sha shi, bari nufinka ya kasance.” |
24197 | MAT 26:74 | Sai ya fara rantsuwa irin ta la'ana, yana cewa, ''Ban san wannan mutumin ba,” nan da nan zakara yayi cara. |
24204 | MAT 27:6 | Sai babban firist ya dauki kwandalolin azurfar ya ce, “Ba daidai bane bisa ga shari'a musa wannan cikin ma'aji, saboda kudin jini ne.” |
24217 | MAT 27:19 | Da yake zaune a kujerar shari'a, matarsa ta aika masa cewa, “Ka fita sha'anin mutumin nan marar laifi. Saboda na sha wahala sosai a yau cikin mafarki saboda shi.” |
24222 | MAT 27:24 | Amma da Bilatus ya ga ba zai iya komai ba don hargitsi zai iya barkewa, ya dauki ruwa ya wanke hannuwansa a gaban jama'a, yace, “Ba ni da laifi ga jinin mutumin nan marar laifi. Ku yi abin da kuka ga dama.” |
24227 | MAT 27:29 | Sai suka yi masa rawanin kaya suka sa a kansa, suka kuma bashi sanda a hannunsa na dama. Suka rusuna a gabansa suna masa ba'a, suna cewa, “Ranka ya dade, Sarkin Yahudawa!” |
24229 | MAT 27:31 | Bayan sun gama masa ba'a, suka cire masa alkyabbar suka sa masa kayansa, suka jagorance shi zuwa wurin da za a gicciye shi. |
24239 | MAT 27:41 | Ta haka ma manyan firistocin suka rika yi masa ba'a, tare da marubuta da shugabannin, suna cewa, |
24276 | MAT 28:12 | Firistocin suka hadu da dattawa suka tattauna al'amarin, sai suka bada kudi masu yawa ga sojojin |
24291 | MRK 1:7 | Yana wa'azi, ya ce “akwai mai zuwa a bayana wanda ya ke da iko fiye da ni. wanda ko maballin takalminsa ban isa in kwance ba. |
24297 | MRK 1:13 | Yana a jeji kwana arba'in, Shaidan yana jarabtar sa. Yana cikin jeji da dabobi, sai malaiku su ka yi masa hidima. |
24304 | MRK 1:20 | Sai ya kira su, su kuwa suka bar mahaifinsu Zabadi a jirgin ruwan da ma'aikatansu, sai su ka bi shi. |
24313 | MRK 1:29 | Bayan da suka bar majami'a, sai su ka shiga gidan Saminu da Andarawus, suna kuma tare da Yakubu da Yahaya. |
24329 | MRK 1:45 | Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko'ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko'ina. |
24333 | MRK 2:4 | Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai. |
24469 | MRK 5:36 | Amma sa'adda Yesu ya ji abin da suka ce, sai ya ce da shugaban majami'ar, “kada ka ji tsoro ka ba da gaskiya kawai.” |
24549 | MRK 7:17 | Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali. |
24554 | MRK 7:22 | zina, kwadayi, mugunta, hai'inci, mugun guri, kishi, zargi, girmankai, wawanci. |
24565 | MRK 7:33 | Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa. |
24640 | MRK 9:33 | Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya? |
24741 | MRK 11:32 | In kuwa muka ce, “ amma in muka ce ta mutum ce zasu jejjefemu domi suna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne. |
24771 | MRK 12:29 | Yesu ya amsa yace, “ mafi girma shine, 'ku saurara ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne. |
24782 | MRK 12:40 | Sun kuma kwace gidajen gwauraye, da yin doguwar addu'a, don mutane su gani. Wadanan mutanen zasu sami hukunci mai tsanani.” |
24788 | MRK 13:2 | Ya ce masa, ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? babu wani dutsen da za a bar shi akan dan'uwansa, da ba za a rushe shi ba.” |
24794 | MRK 13:8 | Al'umma za ta tasarwa al'umma, mulki ya tasarwa mulki. Za a yi girgizar kasa awurare dabam-dabam, da kuma yunwa, amma fa dukkan wadanna abubuwan mafarin azaba ne. |
24862 | MRK 14:39 | Sai ya sake komawa, yayi addu'a, yana maimaita kalmominsa na farko. |
24906 | MRK 15:11 | Sai Firistochi suka zuga jama'a, sai suka yi kuwwa suna cewa, a sakar masu Barrabbas amaimakon Yesu. |
24928 | MRK 15:33 | sa'a ta shida zuwa sa'a ta tara, duhu ya rufe ko'ina, |
24980 | LUK 1:18 | Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa.” |
24981 | LUK 1:19 | Mala'ikan ya amsa ya ce masa, “Nine Jibra'ilu, wanda ke tsaye a gaban Allah. An aiko ni in gaya maka wannan labari mai dadi. |
24996 | LUK 1:34 | Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?” |
25016 | LUK 1:54 | Ya ba da taimako ga bawan sa Isra'ila, domin ya tuna ya kuma nuna jinkai |
25067 | LUK 2:25 | Ga shi akwai wani mutum a Ushalima mai suna Siman. Wannan mutum adali ne kuma mai ibada. Yana jiran mai ta'aziyar Isra'ila, kuma Ruhu Mai-sarki na bisansa. |
25074 | LUK 2:32 | Haske ne na wahayi ga al'ummai, kuma daukakar mutanenka Isra'ila.” |
25076 | LUK 2:34 | Sai Siman ya albarkace su ya ce wa uwatasa Maryamu, “Ki ji da kyau, wannan yaro zai zama sanadiyar faduwa da tashin mutane dayawa a Isra'ila, kuma alama wadda ake kushen ta. |
25113 | LUK 3:19 | Yahaya kuma ya tsauta wa sarki Hirudus domin ya auri matar dan'uwansa, Hiruduya, da kuma sauran abubuwan da Hirudus ya yi. |
25115 | LUK 3:21 | Ana nan, lokacin da ake yiwa dukan mutane baftisma, aka yiwa Yesu mai baftisma. Lokacin da yake yin addu'a, sai sama ta bude, |
25120 | LUK 3:26 | dan Ma'ata, dan Matatiya, dan Shimeya, dan Yuseka, dan Yoda, |
25126 | LUK 3:32 | dan Yesse, dan Obida, dan Bu'aza, dan Salmon, dan Nashon, |
25134 | LUK 4:2 | kwana arba'in, shaidan kuma ya jarabce shi. A kwanakin nan, bai ci abinci ba, kuma yunwa ta kama shi bayan karshen lokacin. |
25147 | LUK 4:15 | Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa. |
25152 | LUK 4:20 | Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa. |
25209 | LUK 5:33 | Sun ce masa, “Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?” |
25229 | LUK 6:14 | Sunayen Manzannin sune Siman (wanda ya kuma kira Bitrus) da dan'uwansa, Andrawus, Yakubu, Yahaya, Filibus, Bartalamawus, |
25252 | LUK 6:37 | Kada ku shari'anta, kuma ba za a shari'anta ku ba. Kada ku kayar, ku ma ba za a kashe ku ba. Ku yafe wa wasu, kuma za a yafe maku. |
25256 | LUK 6:41 | Don me kake duba dan hakin da ke a idon dan'uwanka, amma ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? |
25257 | LUK 6:42 | Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka. |
25327 | LUK 8:13 | Sa'annan, wadanda suka fada kan duwatsu sune mutanen da, da zarar sun ji maganar, sukan karbe ta da murna, amma ba su da sauyu; su kan bada gaskiya na dan lokaci kadan kawai, da zaran gwaji ya same su sai su ridda. |
25355 | LUK 8:41 | Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, daya daga cikin shugabannin majami'a, ya zo kusa da Yesu ya rusuna da kansa a kasa. Ya roke shi domin ya zo gidansa, |
25493 | LUK 11:19 | Idan ni na fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba, ta wurin wa wadanda suke bin ku suke fitar da aljanu? Saboda haka, su ne zasu zama masu yi maku shari'a. |
25539 | LUK 12:11 | Idan suka kawo ku gaban majami'a, ko gaban masu shari'a, ko gaban masu iko, kada ku damu da abin da za ku fada domin ku kare kanku. Ko kuwa abin da za ku ce. |
25579 | LUK 12:51 | Kuna zaton na zo duniya domin in kawo salama? Na ce maku a'a, amma tsattsaguwa. |
25590 | LUK 13:3 | A'a, ina gaya maku. In ba ku tuba ba, dukanku za ku halaka kamarsu. |
25601 | LUK 13:14 | Amma shugaban majami'a yayi fushi domin Yesu yayi warkarwa a ranar Asabaci. Sai shugaban ya amsa yace wa jama'a, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo domin a warkar da ku amma ba ranar Asabaci ba.” |
25651 | LUK 14:29 | Kada ya zama bayan da ya sa harsashin ginin, ya kasa gamawa, har duk wadanda suka gani su fara yi masa ba'a, |
25789 | LUK 18:32 | Gama za a bashe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa miyau. |
25803 | LUK 19:3 | Yana kokarin ya ga ko wanene Yesu, amma bai iya gani ba sabo da yawan jama'a, domin shi gajere ne. |