23240 | MAT 2:2 | ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.'' |
23243 | MAT 2:5 | Suka ce masa, ''A Baitalami ne ta kasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta, |
23246 | MAT 2:8 | Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” |
23253 | MAT 2:15 | Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.'' |
23256 | MAT 2:18 | ''An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su. |
23258 | MAT 2:20 | ''Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu.'' |
23278 | MAT 3:17 | Duba, wata murya daga sammai tana cewa, ''Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.'' |
23451 | MAT 9:3 | Sai wadansu marubuta suka ce a tsakaninsu, ''Wannan mutum sabo yake yi.'' |
23452 | MAT 9:4 | Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, yace, ''Don me kuke mugun tunani a zuciyarku? |
23457 | MAT 9:9 | Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karbar haraji. Yace masa, ''Ka biyo ni.'' Ya tashi ya bi shi. |
23459 | MAT 9:11 | Da Farisawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, ''Don me malamin ku ya ke ci tare da masu karbar haraji da masu zunubi?'' |
23462 | MAT 9:14 | Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, ''Don me mu da Farisawa mu kan yi azumi a kai a kai, amma naka almajiran ba su yi?'' |
23463 | MAT 9:15 | Sai Yesu ya ce masu, ''Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi.'' |
23466 | MAT 9:18 | Yesu kuwa yana cikin yi masu magana sai ga wani shugaban jama'a ya zo ya yi masa sujada, ya ce, ''Yanzun nan 'yata ta rasu, amma ka zo ka dora mata hannu, za ta rayu.'' |
23469 | MAT 9:21 | Domin ta ce a ran ta, ''Ko da mayafinsa ma na taba, sai in warke.'' |
23472 | MAT 9:24 | Sai ya ce, ''Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci ta ke yi.'' Sai suka yi masa dariyar raini. |
23475 | MAT 9:27 | Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai wadansu makafi biyu suka bi shi, suna daga murya suna cewa, ''Ya Dan Dauda, ka ji tausayinmu.'' |
23477 | MAT 9:29 | Sai Yesu ya taba idanunsu, ya ce, ''Ya zama maku gwargwadon bangaskiyarku.'' |
23478 | MAT 9:30 | Sai idanunsu suka bude. Amma Yesu ya umarce su kwarai, ya ce, ''Kada fa kowa ya ji labarin nan.'' |
23485 | MAT 9:37 | Sai ya ce wa almajiransa, ''Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan kadan ne. |
23491 | MAT 10:5 | Sha biyun nan su ne Yesu ya aika, ya yi masu umarni ya ce, ''Kada ku shiga wajen al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. |
23518 | MAT 10:32 | ''Saboda haka duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, ni ma zan yi shaidar sa a gaban Ubana wanda ya ke cikin Sama. |
23520 | MAT 10:34 | ''Kada ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. Ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi. |
23526 | MAT 10:40 | ''Wanda ya marabce ku, ya marabce ni ke nan. |
23797 | MAT 18:1 | Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Wanene mafi girma a mulkin sama?'' |
23799 | MAT 18:3 | ya ce, ''Hakika ina gaya maku, idan baku juya kun zama kamar kananan yara ba, babu yadda zaku shiga mulkin sama. |
23818 | MAT 18:22 | Yesu ya amsa ya ce masa, ''Ban gaya maka sau bakwai ba, amma bakwai din ma har sau saba'in. |
23828 | MAT 18:32 | Sai ubangidansa ya kirawo shi, ya ce masa, ''Kai mugun bawa, na gafarta maka bashin nan duka, domin ka roke ni. |
23834 | MAT 19:3 | Farisawa suka zo wurinsa, suna gwada shi, suka ce masa, ''Ya hallata bisa ga doka mutum ya saki matarsa don kowanne dalili?'' |
23835 | MAT 19:4 | Yesu ya amsa ya ce, ''Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace? |
23838 | MAT 19:7 | Sai suka ce masa, ''To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?'' |
23839 | MAT 19:8 | Sai ya ce masu, ''Saboda taurin zuciyarku, shi yasa Musa ya yarda maku ku saki matanku, amma da farko ba haka yake ba. |
23841 | MAT 19:10 | Almajiran suka ce wa Yesu, ''Idan haka yake game da mutum da matarsa, ba kyau ayi aure ba.'' |
23842 | MAT 19:11 | Amma Yesu yace masu, ''Ba kowa ne zai karbi wannan koyarwa ba, amma sai wadanda an yardar masu su karbe ta. |
23845 | MAT 19:14 | Amma Yesu ya ce masu, ''Ku bar yara kanana, kada ku hana su zuwa wuri na, domin mulkin sama na irinsu ne.'' |
23848 | MAT 19:17 | Yesu ya ce masa, ''Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin.'' |
23849 | MAT 19:18 | Mutumin ya ce masa, ''Wadanne dokokin?'' Yesu ya ce masa, ''Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur, |
23851 | MAT 19:20 | Saurayin nan ya ce masa, ''Ai na kiyaye duk wadannan. Me nake bukata kuma?'' |
23852 | MAT 19:21 | Yesu ya ce masa, ''Idan kana so ka zama cikakke, ka tafi ka sayar da mallakarka, ka kuma ba matalauta, zaka sami dukiya a sama. Sa'annan ka zo ka biyo ni.'' |
23854 | MAT 19:23 | Yesu ya ce wa almajiransa, ''Hakika ina gaya maku, zai zama da wuya mai arziki ya shiga mulkin sama. |
23856 | MAT 19:25 | Da almajiran sun ji haka, suka yi mamaki kwarai da gaske, suka ce, ''Wanene zai sami ceto?'' |
23857 | MAT 19:26 | Yesu ya dube su, ya ce, ''A wurin mutane wannan ba zai yiwu ba, amma a wurin Allah, kome mai yiwuwa ne.'' |
23859 | MAT 19:28 | Yesu ya ce masu, ''Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'anta kabilu goma sha biyu na Isra'ila. |
23882 | MAT 20:21 | Yesu ya ce mata, Me kike so in yi maki?'' Sai ta ce masa, ''Ina so ka ba 'ya'yana izinin zama a mulkinka, daya a hannun damanka, daya kuma a hannun hagunka. |
23883 | MAT 20:22 | Amma Yesu ya amsa, ya ce, ''Baku san abin da kuke roko ba. Ko zaku iya sha daga cikin kokon da zan sha bada dadewa ba?'' Sai suka ce masa, ''Zamu iya.'' |
23884 | MAT 20:23 | Sai ya ce masu, ''In dai kokon nan da zan sha ne, lallai zaku sha. Amma, zama a hannun dama na da kuma hannun hagu na, ba ni ne mai bayarwa ba, amma na wadanda Uba na ya shirya domin su ne.'' |
23886 | MAT 20:25 | Amma Yesu ya kira su wurin sa, ya ce, ''Kuna sane da cewa, sarakunan al'ummai suna gwada masu mulki, manyan-gari kuma na nuna masu iko. |
23891 | MAT 20:30 | Suka kuma ga makafi biyu zaune a bakin hanya. Da makafin suka ji cewa Yesu ne ke wucewa, sai suka tada murya suna cewa, ''Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai.'' |
23892 | MAT 20:31 | Amma jama'ar suka tsauta masu, suka ce suyi shiru. Duk da haka, makafin suka kara tada murya fiye da na da, suka ce, ''Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai.'' |
23893 | MAT 20:32 | Sai Yesu ya tsaya cik, ya sa aka kira su, sai ya ce masu, ''Me kuke so in yi maku?'' |
23922 | MAT 21:27 | Sai suka amsa ma Yesu suka ce, ''Bamu sani ba.” Shi ma yace masu, “Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba. |
23983 | MAT 22:42 | Yace, “Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?” Suka ce masa, ''Dan Dauda ne.” |
24138 | MAT 26:15 | yace, ''Me kuke da niyyar bani idan na mika maku shi?” Suka auna masa azurfa talatin. |
24140 | MAT 26:17 | To a rana ta fari na idin ketarewa almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Ina kake so mu shirya maka da zaka ci abincin idin ketarewa?” |
24145 | MAT 26:22 | Suka yi bakin ciki, suka fara tambayarsa daya bayan daya, ''Na tabbata ba ni bane ko, Ubangiji?” |
24154 | MAT 26:31 | Sai Yesu yace masu, “Dukan ku zaku yi tuntube a wannan dare sabili da ni, gama a rubuce yake, ''Zan bugi makiyayin, garken tumakin kuma za su watse.' |
24157 | MAT 26:34 | Yesu yace masa, ''Hakika ina gaya maka, a wannan daren kafin carar zakara, za ka yi musun sani na sau uku.” |
24159 | MAT 26:36 | Sa'anna Yesu ya tafi tare da su, wurin da ake kira Getsaimani sai yace wa almajiransa, ''Ku zauna a nan ni kuma zan je gaba in yi addu'a.” |
24171 | MAT 26:48 | To mutumin da zai bada Yesu ya rigaya ya basu alama, cewa, ''Duk wanda na sumbata, shine. Ku kama shi.'' |
24184 | MAT 26:61 | sukace ''Wannan mutum yace zan iya rushe haikalin Allah, in kuma gina shi cikin kwana uku.''' |
24191 | MAT 26:68 | sukace, ''Ka yi mana anabci, kai Almasihu. Wanene wanda ya dokeka. |
24197 | MAT 26:74 | Sai ya fara rantsuwa irin ta la'ana, yana cewa, ''Ban san wannan mutumin ba,” nan da nan zakara yayi cara. |
24340 | MRK 2:11 | ''Na ce maka, tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidan ka.” |
24341 | MRK 2:12 | Sai nan da nan ya tashi ya dauki tabarmarsa, ya fita gidan a gabansu, dukansu su ka yi mamaki, su ka girmama Allah, ''suka ce ba mu taba ganin abu irin wannan ba.” |
24661 | MRK 10:4 | Suka ce, ''Musa ya yarda mutum ya rubuta takardar saki ga matarsa, ya sallameta ta fita.'' |
24674 | MRK 10:17 | Lokacin da ya fara tafiya, sai wani mutum ya rugo wurinsa, ya durkusa a gabansa. Ya tambaye shi, yace ya ''Malam managarci, me zan yi domin in sami rai na har abada?'' |
24680 | MRK 10:23 | Yesu ya dubi almajiransa ya ce. ''Yana da wuya masu arziki su shiga mulkin Allah!'' |
24683 | MRK 10:26 | Sai suka cika da mamaki sosai, su kace wa juna, ''to idan haka ne wanene zai iya tsira kenan?'' |
24685 | MRK 10:28 | Bitrus ya ce masa, ''to gashi mu mun bar kome, mun bika''. |
24692 | MRK 10:35 | Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka zo wurin sa, suka ce, ''Malam muna so kayi mana duk abin da mu ka roke ka'' |
24693 | MRK 10:36 | Ya ce masu. ''Me ku ke so in yi maku?'' |
24694 | MRK 10:37 | Suka ce, ''ka yardar mana, a ranar daukakarka, mu zauna daya a damanka, daya kuma a hagunka.'' |
24695 | MRK 10:38 | Yesu ya ce masu. ''Ba ku san abinda ku ke roka ba. Kwa iya sha daga kokon da zan sha? Ko kuma za a yi maku baftismar da za a yi mani?'' |
24696 | MRK 10:39 | Suka fada masa, ''Zamu iya.'' Yesu ya ce masu, '' kokon da zan sha, da shi zaku sha, baftismar da za ayi mani kuma da ita za a yi maku.'' |
24704 | MRK 10:47 | Da ya ji Yesu Banazare ne, ya fara daga murya yana cewa, ''Ya Yesu, Dan Dauda, kaji tausayina'' |
24708 | MRK 10:51 | Yesu ya tambaye shi, ya ce, '' me ka ke so in yi maka?'' Makahon ya ce, ''Malam in sami gani.'' |
24709 | MRK 10:52 | Yesu ya ce masa. ''Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.'' Nan take idanunsa suka bude, ya bi Yesu, suka tafi tare. |
25523 | LUK 11:49 | Saboda wannan daliline hikimar Allah ta ce, ''Zan aika manzanni da annabawa a wurinsu, kuma za su tsananta masu har ma za su kashe wadansu daga cikinsu.' |
26858 | JHN 18:4 | Sai Yesu, da ya san duk abinda ke faruwa da shi, yayiwo gaba, yace masu, ''Wa kuke nema'' |
26859 | JHN 18:5 | Suka amsa masa su ka ce, ''Yesu Banazare'' Yesu yace masu, Ni ne'' Yahuza kuma, wanda ya bashe shi, yana tsaye tare da sojojin. |
26860 | JHN 18:6 | Sa'adda ya ce masu, ''Ni ne'', suka koma da baya, suka fadi a kasa. |
26861 | JHN 18:7 | Ya sake tambayarsu kuma, ''Wa ku ke nema?'' su ka ce, ''Yesu Banazare.'' |
26863 | JHN 18:9 | Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika, ''Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba.'' |
26865 | JHN 18:11 | Yesu ya ce wa Bitrus, ''Mai da takobin ka kubenta. Ba zan sha kokon da Uba ya ba ni ba.'? |
26871 | JHN 18:17 | Sai yarinyar mai tsaron kofar ta ce wa Bitrus, ''kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?'' Yace ''bani ba.'' |
26876 | JHN 18:22 | Sa'adda Yesu ya fadi wannan, wani daga cikin 'yan majalisar da ke tsaye a wurin ya nushi Yesu, yace, ''Kana amsa wa babban firist haka.'' |
26877 | JHN 18:23 | Yesu ya amsa masa yace, ''Idan na fadi mugun abu to, ka bada shaida kan hakan. In kuwa dai dai na fada, to, dan me za ka nushe ni?'' |
26879 | JHN 18:25 | To Saminu Bitrus yana tsaye yana jin dumin. Mutanen kuwa suka ce masa, ''Anya kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?'' Sai yayi musu yace, ''A'a, ba na ciki.'' |
26884 | JHN 18:30 | ''Sai suka amsa suka ce, ''idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka'' |
26885 | JHN 18:31 | bilatus yace masu, ''Ku tafi da shi da kan ku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!'' Sai Yahudawa su kace masa, ''Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa.'' |
26887 | JHN 18:33 | Sai bilatus ya sake shiga cikin fadar Gwamnan, ya kira Yesu ya ce masa, ''kai sarkin Yahudawa ne?'' |
26889 | JHN 18:35 | Bilatus ya amsa “Ni ba Bayahude bane, ko kuwa?'' Ai, jama'arka ne da manyan firistoci suka bashe ka gareni. ''Me ka yi?'' |
26890 | JHN 18:36 | Yesu ya amsa, ''Mulkina ba na duniya nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaki kada a bashe ni ga Yahudawa. To, mulkina ba daga nan ya ke ba.'' |
26891 | JHN 18:37 | Sai Bilatus yace masa, ''Wato ashe, sarki ne kai?'' Yesu ya amsa, ''Yadda ka fada, ni sarki ne. Domin wannan dalili aka haife ni, domin kuma wannan dalili na zo cikin duniya, don in bada shaida game da gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya kuma yakan saurari muryata.'' |
26892 | JHN 18:38 | Bilatus yace masa, ''Menene gaskiya?'' Bayan da ya fadi haka, ya sake fitowa wurin Yahudawa, yace masu, ''Ni kam, ban sami mutumin nan da wani laifi ba. |
26996 | ACT 1:4 | Yayin da yana zaune tare da su ya basu umarni cewa kada su bar Urushalima, amma su jira alkawarin Uban, wanda ya ce, ''Kun ji daga gare ni, |
26999 | ACT 1:7 | Ya ce masu, ''Ba naku bane ku san lokaci ko sa'a wanda Uba ya shirya ta wurin ikonsa. |
27003 | ACT 1:11 | Suka ce, ''Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama.'' |
27030 | ACT 2:12 | Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, ''Menene ma'anar wannan?'' |
27031 | ACT 2:13 | Amma wasu suka yi ba'a suka ce, ''Sun bugu ne da sabon ruwan inabi.'' |