24292 | MRK 1:8 | Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki''. |
24295 | MRK 1:11 | Sai wata murya ta zo daga sama, tana cewa, “Kai kaunataccen Dana ne. zuciyata ta na murna da kai kwarai''. |
24322 | MRK 1:38 | Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa'azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan''. |
24685 | MRK 10:28 | Bitrus ya ce masa, ''to gashi mu mun bar kome, mun bika''. |
27561 | ACT 16:9 | Bulus ya ga wahayi cikin dare, wani mutumin Makidoniya na kiransa, yana cewa. ''Ka zo Makidoniya ka taimake mu''. |
27569 | ACT 16:17 | Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, ''Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne''. |
27570 | ACT 16:18 | Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, ''Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu''. Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take. |
27580 | ACT 16:28 | Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, ''kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan''. |
27583 | ACT 16:31 | Sun ce masa, ''ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira''. |
27588 | ACT 16:36 | Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, ''Ku tafi cikin salama''. |
27595 | ACT 17:3 | Bulus ya bude littattafai yana bayyana masu cewa, dole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu. Ya ce, ''Wannan Yesu kuwa da nake sanar maku, shine Almasihu''. |
27623 | ACT 17:31 | Akwai ranar da ya shirya zai yi wa duniya shari'a cikin adalci, ta wurin mutumin da ya zaba. Allah ya nuna wannan mutumin, ta wurin ta da shi daga matattu''. |
29081 | 2CO 11:24 | Daga hannun yahudawa sau biyar na sha bulala ''Arba'in ba daya''. |