23325 | MAT 5:22 | Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. |
23408 | MAT 7:23 | Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!' |
23547 | MAT 11:19 | Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita. |
24807 | MRK 13:21 | To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata. |
25614 | LUK 13:27 | Amma zai amsa ya ce, “Ina gaya maku, ban san ko daga ina ku ka fito ba, ku tafi daga wurina, dukanku masu aikata mugunta!' |
25741 | LUK 17:21 | Ba kuwa za a ce, 'Gashi nan!' Ko kuwa, 'Ga shi can ba!' domin mulkin Allah yana tsaknaninku.” |
25743 | LUK 17:23 | Za su ce maku, 'Duba can! 'Duba nan!' Amma kada ku je kuna dubawa, ko kuwa ku bi su. |