Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   “Word,    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23233  MAT 1:20  Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi.
23236  MAT 1:23  “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.”
23416  MAT 8:2  Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
23422  MAT 8:8  Sai hafsan, ya ce, “Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke.
23424  MAT 8:10  Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba.
23433  MAT 8:19  Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”
23435  MAT 8:21  Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.”
23439  MAT 8:25  Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”
23446  MAT 8:32  “Yesu ya ce masu, “To, ku je.” Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa.
23560  MAT 12:2  Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. “Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci.”
23576  MAT 12:18  “Dubi, bawa na zababbe; kaunatacce na, wanda ya ke faranta mani raina sosai. Zan sa Ruhu na bisan sa, za ya furta hukunci zuwa al'ummai.
23596  MAT 12:38  Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, “Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”
23605  MAT 12:47  Sai wani ya ce masa, “Duba, mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai”.
23607  MAT 12:49  Sai ya mika hannu ya nuna almajiransa ya ce, “Duba, ga mahaifiyata da 'yan'uwana!
23694  MAT 14:28  Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.”
23696  MAT 14:30  Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
23729  MAT 15:27  Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.”
23730  MAT 15:28  Sai Yesu ya amsa ya ce mata, “Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.”'Yarta ta warke a lokacin.
23773  MAT 17:4  Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.”
23780  MAT 17:11  Yesu ya amsa ya ce, “Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa.
23784  MAT 17:15  “Ubangiji, ka ji tausayin yarona, domin yana da farfadiya, kuma yana shan wuya kwarai, domin sau da yawa yana fadawa cikin wuta ko ruwa.
23822  MAT 18:26  Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, “Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba.”
23945  MAT 22:4  Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, “Ku gaya wa wadanda aka gayyata, “Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren.”
23957  MAT 22:16  Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, “Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane.
23965  MAT 22:24  cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya.
23977  MAT 22:36  “Mallam, wace doka ce mafi girma a cikin shari'a?”
24163  MAT 26:40  Ya koma wurin almajiran ya same su suna barci, sai ya cewa Bitrus, “Kai, ba zaku yi tsaro tare da ni ba koda sa'a daya?
24172  MAT 26:49  Nan da nan ya kaiga Yesu ya ce, “Gaisuwa, Mallam!” sai ya sumbace shi.
24173  MAT 26:50  Yesu kuwa yace masa, “Aboki, kayi abin da ya kawo ka.” Sai suka iso suka sa hannuwansu kan Yesu suka kama shi.
24244  MAT 27:46  Wajen karfe uku, Yesu ya tada murya mai karfi yace, “Eli, Eli lama sabaktani?” wanda ke nufin, “Allahna, Allahna, don me ka yashe ni?”
24334  MRK 2:5  Da ganin bangaskiyarsu, Yesu ya ce wa shanyayyen mutumin, “Da, an gafarta maka zunuban ka”.
24353  MRK 2:24  Sai Farisawa su ka ce masa, “Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?”
24378  MRK 3:21  Da iyalansa suka ji haka, sai suka fito sun kamo shi, saboda sun ce, “Ai, baya cikin hankalinsa “
24405  MRK 4:13  Ya ce masu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? yaushe za ku fahimci sauran?
24413  MRK 4:21  ya ce masu, “Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a karkashin gado? ku kan kawo ta ne don ku dora ta a kan madorinta.
24560  MRK 7:28  Sai ta amsa masa cewa, “I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan.”
24608  MRK 9:1  Sai ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”
24632  MRK 9:25  Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, “kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa.
24633  MRK 9:26  Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, “Ai, yaron ya mutu.
24636  MRK 9:29  Ya ce masu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.”
24730  MRK 11:21  Bitrus kuwa ya tuna ya ce “Malam, dubi! Baurenan da ka la'anta ya bushe.”
24740  MRK 11:31  Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, “in kuwa muka ce, 'daga sama take,' za ya ce, “To, don me ba ku gaskata shi ba?
24749  MRK 12:7  Amma manoman nan suka ce wa juna, “ai, wannan shine magajinsa, 'ku zo mu kashe shi, gadon ya zama namu.”
24756  MRK 12:14  Da suka zo, suka ce masa, “Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. “Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?”
24759  MRK 12:17  Yesu ya ce, “to, ku ba Kaisar abinda yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah. Sai suka yi mamakinsa kwarai.
24761  MRK 12:19  “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba da, lallai ne dan'uwan mutumin ya auri matar, ya haifa wa dan'uwansa 'ya'ya.'
24785  MRK 12:43  Ya kira almajiransa, ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, abinda gwauruwa nan ta saka a akwatin baikon nan ya fi na sauran dukka.
24787  MRK 13:1  da Yesu ke fita daga Haikalin, sai daya daga cikin almajirnsa ya ce masa “malam, dubi kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan!”
24844  MRK 14:21  Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! “zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba”.
24884  MRK 14:61  Amma yayi shiru abinsa, bai ce kome ba. Sai babban firist din ya sake tambayarsa “To, ashe kai ne Allmasihu Dan Madaukaki?
24930  MRK 15:35  Wasu daga cikin na tsaye, da suka ji shi, sai suka ce, “Duba, yana kiran Iliya.”
24934  MRK 15:39  Sa'adda da jarumin sojan da ke tsaye yana fuskantar Yesu ya ga yadda ya mutum, Sai ya ce “hakika, wannan mutum Dan Allah ne.”
25000  LUK 1:38  Maryamu ta ce, “To, ni baiwar Ubangiji ce. Bari ya faru da ni bisa ga sakonka.” Sai mala'ikan ya bar ta.
25106  LUK 3:12  Masu karban haraji ma suka zo domin a yi masu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?”
25108  LUK 3:14  Wasu sojoji ma suka tambaye shi cewa, “To, mu fa? Yaya za mu yi?” Ya ce masu, “Kada ku kwace wa wani kudi, kada ku kuma yi wa wani zargin karya. Ku dogara ga albashinku.”
25181  LUK 5:5  Siman ya amsa ya ce, “Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun.”
25188  LUK 5:12  Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, “Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
25196  LUK 5:20  Da ya ga bangaskiyarsu, Yesu ya ce, “Maigida, an gafarta zunubanka.”
25223  LUK 6:8  Amma ya san abin da suke tunani, sai ya ce wa mai shanyeyen hannun, “Tashi, ka tsaya a nan tsakiyar jama'a.” Sai mutumin ya tashi ya tsaya a nan.
25291  LUK 7:27  Wannan shine wanda aka rubuta a kansa, “Duba, ina aika manzo na a gabanka, wanda za ya shirya maka hanya a gabanka.
25304  LUK 7:40  Yesu ya amsa ya ce masa, “Siman, ina so in gaya maka wani abu.” Ya ce, “malam sai ka fadi!”
25359  LUK 8:45  Yesu ya ce, “Wanene ya taba ni?” Wadanda suke kewaye da shi, kowa ya ce bai taba shi ba, Bitrus ya ce, “Shugaba, mutane da yawa suna ta taruwa kewaye da kai suna ta matsowa kusa da kai.”
25362  LUK 8:48  Sai ya ce da ita, “Diya, bangaskiyarki ta warkar da ke. Tafi cikin salama.”
25368  LUK 8:54  Amma ya kama hannun ta yayi kira cewa, “Yarinya, na ce ki tashi!”
25408  LUK 9:38  Nan da nan, wani mutum daga cikin taron mutanen ya yi magana da karfi, “Mallam, kayi wani abu dominka taimaki da na, shi kadai ne gare ni.
25424  LUK 9:54  Sa'adda biyu daga cikin almajiransa, wato Yakubu da Yahaya suka ga haka, suka ce, “Ubangiji, kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama, ta hallaka su?”
25429  LUK 9:59  Yesu, ya ce da wani mutumin kuma, “Ka biyo ni.” Amma mutumin ya ce, “Ubangiji, ka bari in koma gida in bizine mahaifina tukuna.”
25449  LUK 10:17  Su saba'in din suka dawo da murna, suna cewa, “Ubangiji, har ma aljanu suna yi mana biyayya, a cikin sunanka.”
25457  LUK 10:25  Sai ga wani malamin shari'ar Yahudawa, ya zo ya gwada shi da cewa, “Malam, me zan yi domin in gaji rai na har abada?”
25461  LUK 10:29  Amma, malamin ya na so ya 'yantar da kansa, sai ya ce da Yesu, “To, wanene makwabcina?”
25472  LUK 10:40  Amma ita Marta ta na ta kokari ta shirya abinci. Sai ta zo wurin Yesu ta ce, “Ubangiji, ba ka damu ba 'yar'uwata ta bar ni ina ta yin aiki ni kadai? Ka ce da ita ta taya ni.”
25473  LUK 10:41  Amma Ubangiji ya amsa ya ce da ita, “Marta, Marta, kin damu a kan abubuwa da yawa,
25475  LUK 11:1  Wani lokaci, Yesu yana yin addu'a a wani wuri, sai daya daga cikin almajiransa yace da shi, “Ubangiji, ka koya mana yin addu'a kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.”
25519  LUK 11:45  Wani malami a cikin shari'ar Yahudawa ya amsa masa ya ce, “Malam, abin da ka ce ya bata mana rai mu ma.”
25541  LUK 12:13  Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, ka yi wa dan'uwana magana ya raba gado da ni
25542  LUK 12:14  Yesu ya ce masa, “Kai, wanene ya sa ni in zama alkali, ko matsakanci a kanku?”
25569  LUK 12:41  Sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, mu ka ke fadawa wannan misali, ko ga kowa da kowa ne?”
25610  LUK 13:23  Sai wani ya ce masa, “Ubangiji, wadanda za su sami ceto kadan ne?” Sai ya ce masu,
25675  LUK 15:18  Zan tashi, in tafi gun mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka.
25733  LUK 17:13  sai suka daga murya suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka yi mana jinkai.”
25739  LUK 17:19  Sai ya ce masa, “Tashi, kayi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”
25757  LUK 17:37  Sai suka tambaye shi, “Ina, Ubangiji?” Sai ya ce masu, “Duk in da gangar jiki yake, a nan ungulai sukan taru.”
25785  LUK 18:28  Sai Bitrus ya ce, “To, ga shi mun bar mallakarmu, mun bi ka.”
25786  LUK 18:29  Yesu ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda mulkin Allah,
25795  LUK 18:38  Sai makahon ya ta da murya mai karfi, ya ce, “Yesu, Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
25798  LUK 18:41  “Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ubangiji, ina so in samu gani.”
25805  LUK 19:5  Sa'adda Yesu ya zo wurin, ya kalli sama sai ya ce masa, “Zakka, ka sauko da sauri, domin yau dole in sauka a gidanka.”
25808  LUK 19:8  Zakka ya tsaya ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji, zan ba matalauta rabin arzikina, idan kuma na cuci wani a kome, zan mai da adadinsa sau hudu.”
25839  LUK 19:39  Wadansu Farisawa daga cikin taron jama'a suka ce masa, “Malam, ka tsauta wa almajiranka.”
25869  LUK 20:21  Suka tambaye shi, cewa, “Malam, mun sani da cewa kana fada da koyar da abin ke daidai, kuma ba wanda yake cusa maka ra'ayi, amma kana koyar da gaskiya game da hanyar Allah.
25876  LUK 20:28  suka tambaye shi, cewa, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, mai mace kuma ba shi da yaro, sai dan'uwansa ya auri matar, ya samar wa dan'uwansa yaro.
25887  LUK 20:39  Wadansu marubuta suka amsa, “Malam, ka amsa da kyau.”
25902  LUK 21:7  Sai suka yi masa tambaya, cewa, “Malam, yaushe ne wadannan abubuwan zasu faru? Menene kuma zai zama alama sa'adda wadannan abubuwa suna shirin faruwa?”
25966  LUK 22:33  Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ina shirye in tafi tare da kai zuwa cikin kurkuku da zuwa mutuwa.”
25971  LUK 22:38  Sai suka ce, “Ubangiji, duba! Ga takuba biyu.” Sai ya ce masu, “Ya isa.”
25975  LUK 22:42  yana cewa “Uba, in ka yarda, ka dauke wannan kokon daga gareni. Ko da yake ba nufina ba, amma bari naka nufin ya kasance.”
25981  LUK 22:48  amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, za ka ba da Dan Mutum da sumba?”
25982  LUK 22:49  Sa'adda wadanda suke kewaye da Yesu suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takobi ne?”
25990  LUK 22:57  Amma Bitrus ya yi musu, yana cewa, “Mace, ban san shi ba.”
25991  LUK 22:58  Bayan dan karamin lokaci sai wani mutum ya gan shi, sai ya ce, “Kaima kana daya daga cikinsu.” Amma Bitrus ya ce, “Mutumin, ba ni ba ne.”