23340 | MAT 5:37 | Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. |
23406 | MAT 7:21 | Ba duk mai ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ne, zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi nufin Ubana da yake cikin sama. |
23407 | MAT 7:22 | A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?' |
23538 | MAT 11:10 | Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, 'Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi'. |
23547 | MAT 11:19 | Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita. |
23923 | MAT 21:28 | Amma me kuke tunani? Wani mutum yana da 'ya'ya biyu. Ya je wurin na farkon yace, 'Da, je ka kayi aiki yau a cikin gona.' |
23925 | MAT 21:30 | Sai mutumin ya je wurin da na biyun ya fada masa abu guda. Wannan dan ya amsa ya ce, 'zanje, baba,' amma bai je ba. |
23945 | MAT 22:4 | Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, “Ku gaya wa wadanda aka gayyata, “Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren.” |
23953 | MAT 22:12 | Sai sarkin ya ce masa, 'Aboki, ta yaya ka shigo nan ba tare da kayan aure ba?' Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. |
23995 | MAT 23:8 | Amma ba sai an kira ku 'mallam, ba' domin malami daya kuke da shi, ku duka kuwa 'yan'uwan juna ne. |
24097 | MAT 25:20 | Bawan da ya karbi talanti biyar, ya kawo nasa da ribar wasu biyar. Yace, 'Maigida, ka bani talanti biyar, gashi na samo ribar karin talanti biyar.' |
24098 | MAT 25:21 | Maigidansa yace masa, 'Madalla, bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abu kadan. Zan sa ka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.' |
24099 | MAT 25:22 | Bawan da ya karbi talanti biyun, ya zo yace, 'Maigida, ka ba ni talanti biyu. Gashi kuwa na sami karin ribar wasu biyun.' |
24100 | MAT 25:23 | Ubangidansa yace masa, 'Madalla, kai bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abubuwa kadan. Zan saka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.' |
24101 | MAT 25:24 | Sai bawan da ya karbi talanti daya ya zo yace, 'Maigida, na san kai mai tsanani ne. Kana girbi inda baka yi shuka ba, kuma kana tattarawa inda ba ka watsa ba. |
24114 | MAT 25:37 | Sa'annan masu adalcin za su amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa muka baka abinci? Ko kana jin kishi muka baka ruwan sha? |
24121 | MAT 25:44 | Sa'annan suma zasu amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa, ko kishin ruwa, ko kana bakunci, ko kana huntanci, ko ciwo, kuma a kurkuku, da bamu yi maka hidima ba?' |
24338 | MRK 2:9 | Me yafi sauki a cewa shanyayyen mutumin, 'An gafarta maka zunuban ka' ko kwa a ce masa, 'tashi, ka dauki shinfidarka, ka yi tafiyarka'? |
25155 | LUK 4:23 | Yesu ya ce masu, “Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'” |
25200 | LUK 5:24 | Amma domin ku sani cewa Dan Mutum yana da yancin gafarta zunubai a duniya, na ce maka, 'Tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidanka.'” |
25261 | LUK 6:46 | Don me kuke ce da ni, 'Ubangiji, Ubangiji', amma ba ku yin biyayya da magana ta? |
25612 | LUK 13:25 | In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe kofa, sannan za ku tsaya a waje kuna kwankwasa kofar kuna cewa, 'Ubangiji, Ubangiji, bari mu shiga ciki'. Sai ya amsa yace maku, 'Ni ban san ku ba ko daga ina ku ka fito.' |
25619 | LUK 13:32 | Yesu ya ce, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, 'Duba, na fitar da aljanu, ina warkarwa yau da gobe, kuma a rana ta uku kuwa zan gama aiki na.' |
25632 | LUK 14:10 | Amma idan an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi kaskanci, domin idan wanda ya gayyace ka ya zo, yana iya ce maka, 'Aboki, hawo nan mana'. Sannan za ka sami girma kenan a gaban dukan wadanda kuke zaune tare a kan teburi. |
25644 | LUK 14:22 | Sai bawan ya ce, 'Maigida, abin da ka umarta an gama, amma har yanzu da sauran wuri.” |
25645 | LUK 14:23 | Sai maigidan ya ce wa bawan, 'Jeka, ka bi kwararo-kwararo da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana. |
25669 | LUK 15:12 | sai karamin ya ce wa mahaifinsa, 'Baba, bani rabona daga cikin dukiyarka.' Sai mahaifinsa ya raba masu dukiyarsa tsakaninsu. |
25678 | LUK 15:21 | Dan kuma ya ce masa, 'Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka. Ban isa a kara kira na danka ba.' |
25686 | LUK 15:29 | Amma babban dan ya amsa wa ubansa ya ce, 'Duba, duk yawan shekarun nan da nake bauta maka, ban taba karya umarnin ka ba, duk da haka ba ka taba bani ko dan taure da zan yi shagali tare da abokaina ba, |
25688 | LUK 15:31 | Sai mahaifin ya ce masa, 'Dana, ai kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne. |
25714 | LUK 16:25 | Amma Ibrahim ya ce, 'Yaro, ka tuna fa a zamanka na duniya ka sha duniyarka, ka kuma karba abubuwa masu kyau, amma Li'azaru kuma sai wahala. Amma yanzu dadi ake bashi a nan, kai kuwa kana shan azaba. |
25768 | LUK 18:11 | Sai Bafarisen ya mike, ya yi addu'a a kan wadannan abubuwa game da kansa, 'Allah, na gode maka, da cewa ni ba kamar sauran mutane dake mazambata ba, ko marasa adalci, ko mazinata, ko kamar wannan mai karbar harajin. |
25770 | LUK 18:13 | Amma mai karbar harajin kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya daga kai sama ba, sai dai yana bugun kirjin sa, yana cewa, 'Allah, ka yi mini jinkai, ni mai zunubi.' |
25816 | LUK 19:16 | Na farkon ya zo wurinsa, cewa, 'Ubangiji, fam nan na ka ya yi riban fam goma.' |
25817 | LUK 19:17 | Masaraucin ya ce masa, 'Madalla, bawan kirki. Domin ka yi aminci a karamin abu, za a baka iko kan birane goma.' |
25820 | LUK 19:20 | Wani kuma ya zo, yana cewa, 'Ubangiji, ga fam naka da na ajjiye shi da kyau cikin kaya, |
25825 | LUK 19:25 | Suka ce masa, 'Ubangiji, yana da fam goma.' |
26164 | JHN 1:51 | Sai yace, 'Hakika, hakika ina gaya maka, zaka ga sammai a bude, mala'ikun Allah kuma suna hawa suna sauka akan Dan Mutum.” |
26676 | JHN 12:27 | Yanzu raina na cikin damuwa, to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a? Amma Saboda wannan dalili ne na zo wannan sa'a. |
26712 | JHN 13:13 | kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake. |
27211 | ACT 7:26 | Washegari ya ga wasu Isra'ilawa na fada da junansu; ya yi kokari ya raba su; sai ya ce masu, 'Malamai, ku 'yan'uwan juna ne; don me kuke fada da junanku?' |
27779 | ACT 22:7 | Na fadi kasa sa'anan na ji murya na ce da ni, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?' |
27791 | ACT 22:19 | Na ce, 'Ubangiji, su da kansu sun san yadda na sa su a kurkuku na kuma doddoke wadanda suka gaskanta da kai a kowacce masujada. |
27793 | ACT 22:21 | Amma ya ce mani, 'Tafi, domin zan aike ka can wurin Al'ummai.' |
27905 | ACT 26:14 | Da dukanmu muka fadi kasa, na ji wata murya na magana da ni a harshen Ibraniyawa tana cewa, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani? Yana da wuya ka hauri abin da ke mai tsini.' |
28576 | 1CO 7:21 | Kai bawa ne lokacin da Allah ya kirawo ka? Kada ka damu da haka. Amma idan kana da zarafin samun 'yanci, ka yi haka. |
29197 | GAL 3:28 | Babu Bayahude ko Baheline, bawa ko 'yantacce, babu na miji ko mace, domin dukanku daya ne cikin Almasihu Yesu. |
30184 | HEB 9:12 | Ba ta jinin awaki da 'yan, maruka bane, amma Almasihu da jininsa ya shiga wuri mafi tsarki sau daya tak domin kowa dukka ya karbo mana fansa ta har abada. |
30207 | HEB 10:7 | Sai na ce, 'Duba, gani na zo in yi nufinka, kamar yadda aka rubuta akaina.''' |
30358 | JAS 1:25 | Amma duk mai duba shari'ar da bin ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace biyayya da ita, ba zai zama kamar wanda zai ji ya manta ba, wannan mutum zai zama da albarka a cikin abin da yake yi. |