23340 | MAT 5:37 | Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. |
24732 | MRK 11:23 | Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun', bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi. |
25102 | LUK 3:8 | Ku ba da 'ya'ya da sun cancanci tuba, kada ku kuma fara cewa a cikinku, 'Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu', domin ina gaya maku, Allah yana iya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin wadannan duwatsu. |
25257 | LUK 6:42 | Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka. |
25261 | LUK 6:46 | Don me kuke ce da ni, 'Ubangiji, Ubangiji', amma ba ku yin biyayya da magana ta? |
26163 | JHN 1:50 | Yesu ya amsa masa yace, “Don na ce maka, 'Na gan ka a gindin Baure', ka gaskanta? Za ka ga abubuwa da suka fi wannan girma.” |
26550 | JHN 9:41 | Yesu ya ce masu, “ Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata. |
26586 | JHN 10:36 | kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'? |