23679 | MAT 14:13 | Sa'adda da Yesu ya ji haka, ya fita daga cikin kwale-kwale zuwa wani kebabben wuri. Da taron suka ji haka, suka bi shi da kafa daga biranen. |
23688 | MAT 14:22 | Nan take sai ya sa almajiran suka shiga kwale-kwalen su haye zuwa dayan gefen kafin shi, domin ya sallami taron. |
23690 | MAT 14:24 | Amma yanzu fa kwale-kwalen na tsakiyar tekun, kuma da wuyar sarrafawa saboda rakuman ruwa da iska na gaba da su. |
23699 | MAT 14:33 | Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.” |
23878 | MAT 20:17 | Da Yesu zai tafi Urushalima, ya dauki sha-biyun nan a gefe, yayin da suke tafiya, sai ya ce masu, |
23886 | MAT 20:25 | Amma Yesu ya kira su wurin sa, ya ce, ''Kuna sane da cewa, sarakunan al'ummai suna gwada masu mulki, manyan-gari kuma na nuna masu iko. |
24032 | MAT 24:6 | Za ku ji labarin yake-yake da kuma shelar yake-yake. Ku kula kar ku tsorata, domin dole abubuwan nan su faru; amma karshen dai tukunna. |
24211 | MAT 27:13 | Sai Bilatus yace masa, “Baka ji dukan zarge-zargen da ake yi maka ba?” |
24374 | MRK 3:17 | Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan-uwan Yakubu wanda ya basu sunan Buwanarjis watau 'ya'yan tsawa, |
24389 | MRK 3:32 | Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka.” |
24390 | MRK 3:33 | Ya amsa masu, “Dacewa su wanene uwa-ta da “yan'uwa na? “ |
24391 | MRK 3:34 | Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, “Ga uwa-ta da yan-uwana anan! |
24424 | MRK 4:32 | Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta.” |
24557 | MRK 7:25 | Amma nan da nan wata mace, wadda diyarta ke da mugun ruhu-wannan mace kuwa ta ji game da Yesu sai ta zo ta durkusa a gabansa. |
24793 | MRK 13:7 | In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba. |
24997 | LUK 1:35 | Mala'ikan ya amsa ya ce mata, “Ruhu Mai-tsarki zai sauko a kan ki, kuma ikon Madaukaki zai lullube ki. Sabili da haka, za a kira mai tsarkin da za ki haifa Dan Allah. |
25029 | LUK 1:67 | Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa, |
25067 | LUK 2:25 | Ga shi akwai wani mutum a Ushalima mai suna Siman. Wannan mutum adali ne kuma mai ibada. Yana jiran mai ta'aziyar Isra'ila, kuma Ruhu Mai-sarki na bisansa. |
25068 | LUK 2:26 | An kuma bayyana masa ta wurin Ruhu Mai-tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kristi na Ubangiji. |
25238 | LUK 6:23 | Za ku yi farin ciki a ranan nan kuna tsalle domin murna, domin hakika za ku samu lada mai girma a sama, domin haka kakannin-kakannin su suka yi wa annabawa. |
25241 | LUK 6:26 | Kaiton ku idan kowadanne mutane suna yabon ku! Domin haka kakannin-kakanninsu suka yi wa annabawan karya. |
25521 | LUK 11:47 | Kaiton ku, gama kuna gina abubuwan tunawa a kabuburan annabawa, alhali kuwa kakanni-kakanninku ne suka kashe su. |
25615 | LUK 13:28 | Za a yi kuka da cizon hakora a lokacin da kun ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu da dukan annabawa a mulkin Allah amma ku-za a jefar da ku waje. |
25645 | LUK 14:23 | Sai maigidan ya ce wa bawan, 'Jeka, ka bi kwararo-kwararo da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana. |
25682 | LUK 15:25 | A wannan lokacin, babban dansa yana gona. Da ya kai kusa da gida, ya ji ana kade-kade da raye-raye. |
25748 | LUK 17:28 | Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine. |
26232 | JHN 4:7 | Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha.” |
26234 | JHN 4:9 | Sai ba-Samariyar tace masa, “Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?” Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa. |
26297 | JHN 5:18 | Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah. |
26397 | JHN 6:71 | Wato yana magana akan Yahuda dan Siman Iskariyoti, shi kuwa daya daga cikin sha-biyun ne, wanda zai ba da Yesu. |
26459 | JHN 8:9 | Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su. |
26494 | JHN 8:44 | Ku na ubanku, shaidan ne, kuma kuna so ku yi nufe-nufe na ubanku. Shi mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma. |
26794 | JHN 15:26 | Sa'adda Mai Ta'aziya- wanda zan aiko maku daga wurin Uban, wato, Ruhun gaskiya, wanda ke fita daga wurin Uban-ya zo, zai bada shaida a kai na. |
27221 | ACT 7:36 | Bayan alamu da al'ajibai iri-iri a Masar da kuma Baharmaliya, Musa ya fito da su daga Masar da kuma cikin jeji, a lokacin da suka yi tafiya shekara arbain. |
27437 | ACT 13:6 | Bayan sun zaga tsibirin duka har Bafusa, nan suka iske wani Bayahude mai suna Bar-yeshua mai tsafi kuma annabin karya. |
27863 | ACT 24:26 | A wannan lokacin, yasa zuciya Bulus zai bashi kudi, yayi ta nemansa akai-akai domin yayi magana da shi. |
28210 | ROM 8:26 | Hakanan, Ruhu kuma ke taimako a kasawarmu. Gama ba mu da san yadda zamu yi addu'a ba, amma Ruhu kansa na roko a madadinmu da nishe-nishen da ba'a iya ambatawa. |
28225 | ROM 9:2 | cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata. |
28306 | ROM 11:29 | Domin baye-baye da kiran Allah basa canzawa. |
28310 | ROM 11:33 | Ina misalin zurfin wadata da kuma hikima da sani na Allah! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban a bincika, hanyoyinsa kuma sun fi gaban ganewa! |
28319 | ROM 12:6 | Muna da baye-baye dabam-dabam bisa ga alherin da aka bayar a gare mu. Idan baiwar wani anabci ne, yayi shi bisa ga iyakar bangaskiyarsa. |
28506 | 1CO 4:5 | Sabili da haka, kada ku yanke shari'a kafin lokaci, kafin Ubangiji ya dawo. Zai bayyana dukkan boyayyun ayyuka na duhu, ya kuma tona nufe-nufen zuciya. San nan kowa zai samu yabonsa daga wurin Allah. |
28546 | 1CO 6:11 | Kuma da haka wadansu a cikinku suke, amma an tsarkake ku, an mika ku ga Allah, an maida tsayuwar ku dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu. |
28567 | 1CO 7:12 | Amma ga sauran ina cewa-Ni, ba Ubangiji ba-idan wani dan'uwa yana da mata wadda ba mai bi ba, kuma idan ta yarda ta zauna da shi, to kada ya sake ta. |
28583 | 1CO 7:28 | Amma idan ka yi aure, ba ka yi zunubi ba. Kuma idan mace marar aure ta yi aure, bata yi zunubi ba. Saidai su wadanda suka yi aure za sha wahalhalu iri-iri a yayinda suke raye, kuma ina so in raba ku da su. |
28880 | 2CO 1:12 | Muna kuwa alfahari da haka: wato shaidar lamirinmu. Gama da kyakkyawan nufi da aminci da ke zuwa daga Allah muka tafiyar da rayuwarmu a Duniya. Mun yi wannan ne musamman tare da ku-ba kuwa cikin hikimar Duniya ba, amma ta wurin alherin Allah. |
28902 | 2CO 2:10 | Duk mutumin da kuka gafarta wa, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta-idan na gafarta wani abu-an gafarta ne domin ku a gaban Almasihu. |
28979 | 2CO 6:13 | Yanzu a sabanin haka-Ina magana da ku kamar yara-ku bude mana zukatanku. |
28994 | 2CO 7:10 | Domin bakinciki daga Allah ya kan kai ga tuba da ke kammala ceto ba tare da-da na sani ba. Bakinciki na duniya kuwa ya kan kai ga mutuwa. |
29007 | 2CO 8:7 | Amma kun habaka cikin komai-cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin aiki tukuru, cikin kaunarku dominmu. Don haka, ku tabbata kun habaka a wannan aiki na bayarwa. |
29012 | 2CO 8:12 | Idan kuna niyya ku yi wannan aiki, abu mai kyau ne karbabbe kuma. Tabbas ya zama dai-dai da abinda mutum ke da shi, ba abinda ba ya da shi ba. |
29028 | 2CO 9:4 | Idan kuwa ba haka ba, idan wani cikin makidoniyawa ya biyoni kuma ya tarar da baku shirya ba, za mu ji kunya-ba ni cewa komai game da ku-domin ina da gabagadi a kan ku. |
29078 | 2CO 11:21 | Ina mai cewa mun kunyata da muka rasa gabagadin yi maku haka. Duk da haka idan wani zai yi fahariya-Ina magana kamar wawa-Ni ma zan yi fahariya. |
29092 | 2CO 12:2 | Na san wani mutum cikin Almasihu, wanda shekaru goma sha hudu da suka wuce-ko a cikin jiki ne ko ba a jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-an dauke shi zuwa sama ta uku. |
29093 | 2CO 12:3 | Kuma na san wannan mutumin-ko cikin jiki ko kuma ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani- |
29138 | GAL 1:14 | Ina gaba-gaba cikin Yahudanci fiye da yawancin tsararrakina. A kwazo kuwa fiye da kima game da al'adun ubannina. |
29784 | 1TI 2:1 | Don haka da farko dai, Ina roko a yi roke-roke da addu'o'i, da yin roko domin jama, a dukka, da ba da godiya, a yi haka domin dukkan mutane, |
29835 | 1TI 5:5 | Amma gwamruwa ta gaske da ke ita kadai, ta kafa begenta ga Allah. Kullum tana tsananta yin roke-roke da addu'o'i dare da rana. |
29943 | 2TI 4:6 | Gama ana-tsiyaye ni. Lokacin yin kaurata yayi. |
30084 | HEB 4:3 | Ai mu, wadanda muka gaskata-mune zamu shiga wannan hutun, kamar yadda ya ce, “Yadda na yi rantsuwa cikin fushina, baza su shiga hutu na ba.” Ya fadi hakan, ko da yake ya gama aikin hallittarsa tun daga farkon duniya. |
30118 | HEB 6:7 | Kasa ma da take shanye ruwan da ake yi a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga wadanda ake nomanta dominsu, Allah yakan sa mata albarka. |
30119 | HEB 6:8 | Amma idan tsire-tsirenta kaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, karshenta dai konewa ne. |
30422 | JAS 5:1 | Ku zo yanzu, ku da kuke masu arziki, ku yi ta kuka da kururuwa domin bakin ciki iri-iri da ke zuwa gare ku. |
30458 | 1PE 1:17 | Idan ku na kira bisa gare shi “Uba” shi wanda yake hukuntawa ba da tara ba, amma gwar-gwadon aikin kowane mutum, sai kuyi zaman bakuncinku da tsoro da bangirma. |
30469 | 1PE 2:3 | idan kun dandana Ubangiji mai-alheri ne. |
30470 | 1PE 2:4 | Kuzo gareshi rayayyen dutse wanda mutane suka ki, amma zababbe ne mai-daraja wurin Allah. |
30471 | 1PE 2:5 | Ku kuma kamar rayayyun duwatsu ana gina ku gida mai ruhaniya, domin ku zama tsarka-kan fristoci, domin ku mika hadayu masu ruhaniya abin karba ga Allah ta wurin Yesu Almasihu. |
30477 | 1PE 2:11 | Kaunatattu, ina rokon ku misalin baki da masu-tafiya kuma, ku guje wa sha'awoyin jiki wadanda ke yaki da rai. |
30516 | 1PE 4:3 | Gama lokaci ya wuce da zamu yi abin da al'ummai suke son yi, wato fajirci, mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa da shashanci da shaye-shaye da bautar gumaku da abubuwan kyama. |
30744 | JUD 1:4 | Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu. |
30745 | JUD 1:5 | Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba. |
30746 | JUD 1:6 | Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a. |
30830 | REV 3:16 | Amma saboda kai tsaka-tsaka ne - ba zafi ba sanyi - na kusa tofar da kai daga bakina. |
31150 | REV 22:1 | Sai mala'ika ya nuna mani kogin ruwan rai, ruwa mai tsabta. Yana fitowa daga cikin kursiyin Allah da na Dan-Rago |