23240 | MAT 2:2 | ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.'' |
23253 | MAT 2:15 | Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.'' |
23258 | MAT 2:20 | ''Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu.'' |
23264 | MAT 3:3 | Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.'' |
23278 | MAT 3:17 | Duba, wata murya daga sammai tana cewa, ''Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.'' |
23287 | MAT 4:9 | Ya ce masa, “Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada.'' |
23412 | MAT 7:27 | Ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, sai iska ta taso ta buga gidan. Sai kuma ya rushe, ya kuwa yi cikakkiyar ragargajewa.'' |
23450 | MAT 9:2 | Sai gashi, sun kawo masa wani mutum shanyayye kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, ''Da, ka yi farin ciki. An gafarta maka zunuban ka.'' |
23451 | MAT 9:3 | Sai wadansu marubuta suka ce a tsakaninsu, ''Wannan mutum sabo yake yi.'' |
23454 | MAT 9:6 | Amma domin ku sani Dan mutum yana da ikon gafarta zunubai a duniya...'' Sai ya ce wa shanyayyen, ''Tashi, ka dauki shimfidarka ka tafi gida.'' |
23457 | MAT 9:9 | Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karbar haraji. Yace masa, ''Ka biyo ni.'' Ya tashi ya bi shi. |
23463 | MAT 9:15 | Sai Yesu ya ce masu, ''Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi.'' |
23465 | MAT 9:17 | Mutane kuma ba su dura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Idan sun yi haka, sai salkunan kuma su fashe inabin ya tsiyaye, sai salkunan su lalace. A maimakon haka, ana sa sabon inabi cikin sababbin salkuna, ta haka an tsirar da duka biyun kenan.'' |
23466 | MAT 9:18 | Yesu kuwa yana cikin yi masu magana sai ga wani shugaban jama'a ya zo ya yi masa sujada, ya ce, ''Yanzun nan 'yata ta rasu, amma ka zo ka dora mata hannu, za ta rayu.'' |
23469 | MAT 9:21 | Domin ta ce a ran ta, ''Ko da mayafinsa ma na taba, sai in warke.'' |
23470 | MAT 9:22 | Sai Yesu ya juya, ya gan ta ya ce, '''Yata, ki karfafa. Bangaskiyarki ta warkar da ke.'' Nan take matar ta warke. |
23472 | MAT 9:24 | Sai ya ce, ''Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci ta ke yi.'' Sai suka yi masa dariyar raini. |
23475 | MAT 9:27 | Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai wadansu makafi biyu suka bi shi, suna daga murya suna cewa, ''Ya Dan Dauda, ka ji tausayinmu.'' |
23476 | MAT 9:28 | Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?'' Sai suka ce masa. ''I, ya Ubangiji.'' |
23477 | MAT 9:29 | Sai Yesu ya taba idanunsu, ya ce, ''Ya zama maku gwargwadon bangaskiyarku.'' |
23478 | MAT 9:30 | Sai idanunsu suka bude. Amma Yesu ya umarce su kwarai, ya ce, ''Kada fa kowa ya ji labarin nan.'' |
23482 | MAT 9:34 | Amma sai Farisawa suka ce, ''Ai, da ikon sarkin aljanu ya ke fitar da aljanu.'' |
23486 | MAT 9:38 | Saboda haka sai ku yi sauri ku roki Ubangijin girbin ya turo ma'aikata cikin girbinsa.'' |
23519 | MAT 10:33 | Amma duk wanda ya yi musun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi musun sanin sa a gaban Ubana da yake cikin Sama.'' |
23528 | MAT 10:42 | Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba.'' |
23816 | MAT 18:20 | Wurin da mutum biyu ko uku suka taru a cikin sunana, zan kasance tare da su.'' |
23831 | MAT 18:35 | Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan'uwansa daga zuciya ba.'' |
23837 | MAT 19:6 | Su ba biyu ba ne kuma, amma jiki daya. Don haka, duk abin da Allah ya hada, kada wani ya raba.'' |
23840 | MAT 19:9 | Ina gaya maku, duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, yana zina kenan. Wanda kuma ya auri macen da aka saka, yana aikata zina.'' |
23841 | MAT 19:10 | Almajiran suka ce wa Yesu, ''Idan haka yake game da mutum da matarsa, ba kyau ayi aure ba.'' |
23843 | MAT 19:12 | Akwai wadanda aka haife su babanni. Akwai wadanda mutane ne suka maida su babanni. Sa'annan akwai wadanda sun mayar da kansu babanni saboda mulkin sama. Duk wanda zai iya karbar wannan koyarwa, ya karba.'' |
23845 | MAT 19:14 | Amma Yesu ya ce masu, ''Ku bar yara kanana, kada ku hana su zuwa wuri na, domin mulkin sama na irinsu ne.'' |
23848 | MAT 19:17 | Yesu ya ce masa, ''Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin.'' |
23850 | MAT 19:19 | ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.'' |
23852 | MAT 19:21 | Yesu ya ce masa, ''Idan kana so ka zama cikakke, ka tafi ka sayar da mallakarka, ka kuma ba matalauta, zaka sami dukiya a sama. Sa'annan ka zo ka biyo ni.'' |
23855 | MAT 19:24 | Ina sake gaya maku, zai fi wa rakumi sauki ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.'' |
23857 | MAT 19:26 | Yesu ya dube su, ya ce, ''A wurin mutane wannan ba zai yiwu ba, amma a wurin Allah, kome mai yiwuwa ne.'' |
23877 | MAT 20:16 | Haka yake, na karshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na karshe.'' [An kira dayawa, amma kadan ne zababbu]. |
23880 | MAT 20:19 | za su kuma bada shi ga al'ummai don suyi masa ba'a, su bulale shi, su kuma gicciye shi. Amma a rana ta uku, za a tada shi.'' |
23883 | MAT 20:22 | Amma Yesu ya amsa, ya ce, ''Baku san abin da kuke roko ba. Ko zaku iya sha daga cikin kokon da zan sha bada dadewa ba?'' Sai suka ce masa, ''Zamu iya.'' |
23884 | MAT 20:23 | Sai ya ce masu, ''In dai kokon nan da zan sha ne, lallai zaku sha. Amma, zama a hannun dama na da kuma hannun hagu na, ba ni ne mai bayarwa ba, amma na wadanda Uba na ya shirya domin su ne.'' |
23889 | MAT 20:28 | Kamar dai yadda Dan mutum bai zo don a bauta masa ba, amma yayi bauta, ya kuma bada ransa fansa domin mutane dayawa.'' |
23891 | MAT 20:30 | Suka kuma ga makafi biyu zaune a bakin hanya. Da makafin suka ji cewa Yesu ne ke wucewa, sai suka tada murya suna cewa, ''Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai.'' |
23892 | MAT 20:31 | Amma jama'ar suka tsauta masu, suka ce suyi shiru. Duk da haka, makafin suka kara tada murya fiye da na da, suka ce, ''Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai.'' |
23894 | MAT 20:33 | Sai suka ce masa, Ya Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.'' |
24171 | MAT 26:48 | To mutumin da zai bada Yesu ya rigaya ya basu alama, cewa, ''Duk wanda na sumbata, shine. Ku kama shi.'' |
24186 | MAT 26:63 | Amma Yesu yayi shiru. Babban Firist ya ce, “Na umarce ka da sunan Allah mai rai, ka gaya mana ko kai Almasihu ne, Dan Allah.'' |
24198 | MAT 26:75 | Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya fada, “Kafin carar zakara zaka yi musun sani na sau uku.” Sai ya fita waje yayi kuka mai zafi.'' |
24661 | MRK 10:4 | Suka ce, ''Musa ya yarda mutum ya rubuta takardar saki ga matarsa, ya sallameta ta fita.'' |
24694 | MRK 10:37 | Suka ce, ''ka yardar mana, a ranar daukakarka, mu zauna daya a damanka, daya kuma a hagunka.'' |
24696 | MRK 10:39 | Suka fada masa, ''Zamu iya.'' Yesu ya ce masu, '' kokon da zan sha, da shi zaku sha, baftismar da za ayi mani kuma da ita za a yi maku.'' |
24706 | MRK 10:49 | Yesu ya tsaya ya ce, ku kirawo shi. Su kuwa suka kirawo makahon suka ce masa. ''Albishrinka, ta so! Yana kiranka.'' |
24708 | MRK 10:51 | Yesu ya tambaye shi, ya ce, '' me ka ke so in yi maka?'' Makahon ya ce, ''Malam in sami gani.'' |
24709 | MRK 10:52 | Yesu ya ce masa. ''Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.'' Nan take idanunsa suka bude, ya bi Yesu, suka tafi tare. |
24773 | MRK 12:31 | ta biyu itace, 'ka kaunaci makwabcinka kamar kanka, Ba wata doka da ta fi wadannan.'' |
26861 | JHN 18:7 | Ya sake tambayarsu kuma, ''Wa ku ke nema?'' su ka ce, ''Yesu Banazare.'' |
26863 | JHN 18:9 | Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika, ''Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba.'' |
26871 | JHN 18:17 | Sai yarinyar mai tsaron kofar ta ce wa Bitrus, ''kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?'' Yace ''bani ba.'' |
26876 | JHN 18:22 | Sa'adda Yesu ya fadi wannan, wani daga cikin 'yan majalisar da ke tsaye a wurin ya nushi Yesu, yace, ''Kana amsa wa babban firist haka.'' |
26879 | JHN 18:25 | To Saminu Bitrus yana tsaye yana jin dumin. Mutanen kuwa suka ce masa, ''Anya kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?'' Sai yayi musu yace, ''A'a, ba na ciki.'' |
26885 | JHN 18:31 | bilatus yace masu, ''Ku tafi da shi da kan ku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!'' Sai Yahudawa su kace masa, ''Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa.'' |
26890 | JHN 18:36 | Yesu ya amsa, ''Mulkina ba na duniya nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaki kada a bashe ni ga Yahudawa. To, mulkina ba daga nan ya ke ba.'' |
26891 | JHN 18:37 | Sai Bilatus yace masa, ''Wato ashe, sarki ne kai?'' Yesu ya amsa, ''Yadda ka fada, ni sarki ne. Domin wannan dalili aka haife ni, domin kuma wannan dalili na zo cikin duniya, don in bada shaida game da gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya kuma yakan saurari muryata.'' |
26894 | JHN 18:40 | Sai suka sake daukar kururuwa suna cewa, ''A; a, ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas.'' Barabbas din nan kuwa dan fashi ne. |
26997 | ACT 1:5 | cewa Yahaya babu shakka ya yi baftisma da ruwa, amma ku za a yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki nan da kwanaki kadan.'' |
27003 | ACT 1:11 | Suka ce, ''Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama.'' |
27029 | ACT 2:11 | Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.'' |
27031 | ACT 2:13 | Amma wasu suka yi ba'a suka ce, ''Sun bugu ne da sabon ruwan inabi.'' |
27057 | ACT 2:39 | Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira.'' |
27058 | ACT 2:40 | Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, ''Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara.'' |
27069 | ACT 3:4 | Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, ''Ka dube mu.'' |
27103 | ACT 4:12 | Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto.'' |
27108 | ACT 4:17 | Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna.'' |
27111 | ACT 4:20 | Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba.'' |
27137 | ACT 5:9 | Sa'annan Bitrus ya ce mata, ''Don me kuka shirya wannan makidar tare da mijinki don ku gwada Ruhun Ubangiji? Kiji tafiyar wadanda suka bizne mijinki a bakin kofa, kuma za su dauke ki yanzu.'' |
27160 | ACT 5:32 | Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi.'' |
27167 | ACT 5:39 | Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah.'' Sai suka rinjayu. |
27174 | ACT 6:4 | Mu kuwa mu ci gaba da da addu'a da kuma hidimar kalmar.'' |
27181 | ACT 6:11 | Sai a asirce suka zuga wasu mutane su je su ce, ''Ai munji Istifanus yana maganganun sabo game da Musa da kuma Allah.'' |
27184 | ACT 6:14 | Domin kuwa mun ji shi, yana cewa wannan Yesu Banazarat zai rushe wannan wuri zai kuma canza al'adun da muka gada daga wurin Musa.'' |
27255 | ACT 8:10 | Dukan Samariyawa, manya da yara, suna sauraronsa, su kan ce, ''Wannan mutum shine ikon Allahn nan wanda ake kira mai girma.'' |
27264 | ACT 8:19 | Ya ce, “Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki.'' |
27268 | ACT 8:23 | Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi.'' |
27269 | ACT 8:24 | Siman ya amsa ya ce, ''Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni.'' |
27274 | ACT 8:29 | Ruhun ya ce wa Filibus, ''Ka je kusa da karussar nan.'' |
27278 | ACT 8:33 | Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya.'' |
27295 | ACT 9:10 | Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, ''Hananiya.'' Sai ya ce, ''Duba, gani nan Ubangiji.'' |
27297 | ACT 9:12 | kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude.'' |
27299 | ACT 9:14 | An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka.'' |
27301 | ACT 9:16 | Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana.'' |
27302 | ACT 9:17 | Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, ''Dan'uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa'adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki.'' |
27306 | ACT 9:21 | Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce ''Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci.'' |
27319 | ACT 9:34 | Bitrus ya ce masa, ''Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka.'' Nan take sai ya mike. |
27323 | ACT 9:38 | Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, ''Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba.'' |
27325 | ACT 9:40 | Bitrus ya fitar da su duka daga cikin dakin, ya durkusa, ya yi addu'a; sai, ya juya wurin gawar, ya ce, ''Tabita, tashi.'' Ta bude idanunta, da ta ga Bitrus ta zauna, |
27464 | ACT 13:33 | Ubangiji ya bar mana alkawaran. Don haka ya ta da Yesu daga matattu. Kamar yadda ya ke a littafin zabura ta biyu: ''Kai da na ne yau na zama mahaifinka.'' |
27465 | ACT 13:34 | Kuma dalilin tayar da shi daga matattu shine saboda kada jikinsa ya rube, ya yi magana kamar haka: ''Zan baku albarkun Dauda masu tsarki tabatattu.'' |
27599 | ACT 17:7 | Wadannan mutane da Yason ya marabta, sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu.'' |
27612 | ACT 17:20 | Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su.'' |
27624 | ACT 17:32 | Da mutanen Atina sun ji batun tashi daga matattu, wadansu suka yi wa Bulus ba'a; amma wadansu kuma sun ce, ''Za mu saurare ka kuma, a kan wannan maganar.'' |