23215 | MAT 1:2 | Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da 'yan'uwansa. |
23402 | MAT 7:17 | Haka kowanne itace mai kyau yakan haifi kyawawan 'ya'ya, amma mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. |
23591 | MAT 12:33 | Ko dai a mai da itace mai kyau 'ya'yansa kuma su yi kyau, ko a mai da itace marar kyau 'ya'yansa kuma marasa kyau, gama ana sanin itace ta wurin 'ya'yansa. |
23630 | MAT 13:22 | Shi wanda aka shuka a cikin kayayuwa wannan shine wanda ya ji maganar, amma dawainiyar duniya da kuma yaudarar dukiya suka shake maganar, sai ya kasa ba da 'ya'ya. |
23881 | MAT 20:20 | Sai uwar 'ya'yan Zabadi ta zo wurin Yesu tare da 'ya'yanta. Ta rusuna a gabansa tana neman alfarma a wurinsa. |
23965 | MAT 22:24 | cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. |
24722 | MRK 11:13 | Da ya hango itacen baure mai ganye daga nesa sai ya je ya ga ko za sami 'ya'ya. Da ya iso wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan baure ba ne. |
24763 | MRK 12:21 | Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba 'ya'ya. Na ukun ma haka. |
24764 | MRK 12:22 | Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar 'ya'ya. A karshe kuma ita matar ta mutu. |
25258 | LUK 6:43 | Domin babu itace mai kyau da ke haifar rubabbun 'ya'ya, ko rubabben itace da zai haifi kyawawan 'ya'ya. |
25329 | LUK 8:15 | Amma irin da suka fada a kan kasa mai kyau, wadannan sune mutanen da suka ji maganar, suka karbe ta da gaskiya da zuciya daya, sun rike ta kam-kam, suna jimrewa wurin ba da 'ya'ya. |
25844 | LUK 19:44 | Za su sare ki kasa tare da 'ya'yanki. Ba za su bar wani dutse akan dan'uwansa ba, domin ba ki lura da lokacin da Allah ya na kokarin ceton ki ba.” |
26032 | LUK 23:28 | Amma da ya juya wurinsu, Yesu yace, “Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka domina, amma ku yi kuka domin kanku da 'ya'yanku. |
26770 | JHN 15:2 | Yakan cire duk wani rashe a cikina da ba ya bada 'ya'ya, mai bada 'ya'ya kuwa ya kan gyara shi domin ya kara bada 'ya'ya. |
27006 | ACT 1:14 | Dukansu kuwa suka hada kai gaba daya, yayin da suka ci gaba da naciya cikin addu'a. Tare da su kuma akwai mata, Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma 'yan'uwansa. |
27087 | ACT 3:22 | Musa hakika ya ce, 'Ubangiji Allah zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin, 'yan'uwanku. Za ku saurari dukan abin da zai fada maku. |
27485 | ACT 14:2 | Amma Yahudawa da basu yi biyayya ba, suka zuga al'umman har suka yi fushi da 'yan'uwan. |
27514 | ACT 15:3 | Da shike iklisiya ce ta aike su, sai suka bi ta Finikiya da ta Samariya suka sanar da tuban al'ummai. Ya kawo murna mai yawa a wurin 'yan'uwa. |
28163 | ROM 7:4 | Domin wannan, 'yan'uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari'a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah 'ya'ya. |
28856 | 1CO 16:12 | Game da zancen dan'uwanmu Afollos kuwa, na karfafa shi ya ziyarce ku tare da 'yan'uwa. Sai dai baya sha'awar zuwa yanzu. Amma zai zo sa'adda lokaci ya yi. |
29203 | GAL 4:5 | Ya yi haka ne domin ya fanshi wadanda ke a karkashin shari'a, domin mu karbi diyanci a matsayin 'ya'ya. |
29223 | GAL 4:25 | Yanzu fa, Hajaratu ita ce dutsen Sinayi da ke Arebiya. Misali ce na Urushalima na yanzu, domin tana cikin bauta tare da 'ya'yanta. |
29273 | GAL 6:18 | Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance da ruhun ku, 'yan'uwa. Amin. |
29298 | EPH 2:2 | A cikinsu kuka yi rayuwa bisa ga al'amuran duniyan nan. Kuka biye wa mai sarautar ikokin sararin sama, wannan ruhun ne da ke aiki cikin kangararrun 'ya'ya. |
29372 | EPH 5:1 | Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun 'ya'yansa. |
29377 | EPH 5:6 | Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun 'ya'ya. |
29505 | PHP 3:17 | Ku zama masu koyi da ni, 'yan'uwa. Ku duba da kyau wadannan da suke tafiya yadda muka zama abin koyi a gare ku. |
29679 | 1TH 4:9 | Game da kaunar 'yan'uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar 'yan'uwa. |
29715 | 1TH 5:27 | Ina rokon ku saboda Ubangiji ku karanta wasikar nan ga dukkan 'yan'uwa. |
29831 | 1TI 5:1 | Kada ka tsauta wa dattijo. Sai dai ka gargade shi kamar mahaifi. Ka gargadi samari kamar 'yan'uwa. |
29958 | 2TI 4:21 | Ka yi iyakar kokarinka, ka zo kamin hunturu. Yubulus yana gayar da kai, haka ma Budis da Linus da Kalafidiya da dukan 'yan'uwa. |
29979 | TIT 2:4 | domin su koyar da kananan mataye da hikima su kaunaci mazajensu da 'ya'yansu. |
30055 | HEB 2:11 | Domin da shi mai tsarkakewar da kuma wadanda aka tsarkaken, duk tushensu daya ne. Saboda wanan dalili ne shi ya sa ba ya jin kunyar kiran su 'ya'uwansa. |
30387 | JAS 3:1 | Ba mutane dayawa za su zama masu koyarwa ba, 'yan'uwana. Mun san cewa za mu karbi hukunci mafi tsanani. |
30415 | JAS 4:11 | Kada ku rika zargin juna, 'yan'uwa. Wanda ya ke zargin dan'uwa ko shari'anta dan'uwansa, yana zargin shari'a kuma yana hukunta shari'a. Idan ka hukunta shari'a, ya nuna ba ka biyayya da shari'ar, amma mai hukunci. |
30660 | 1JN 3:14 | Mun sani mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai, saboda muna kaunar 'yan'uwa. Dukkan wanda ba ya yin kauna, shi matacce ne. |
30662 | 1JN 3:16 | Ta wurin haka muka san kauna, da ya ke Almasihu ya bayar da ransa saboda mu. Mu ma ya kamata mu bada ranmu saboda 'yan'uwamu. |
30735 | 3JN 1:10 | Saboda haka, idan na zo, zan tuna masa da irin ayukkan sa, da kuma yadda yake babbata sunayen mu a wurin jama'a da miyagun kalmomi. Wannan ma bai ishe shi ba, har ma yana kin karbar 'yan'uwa. Ya kuma hana wadanda suke son su yin hakan, harma ya kan kore su daga ikilisiya. |