24303 | MRK 1:19 | Sa'adda Yesu ya yi tafiya kadan, sai ya ga Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan'uwansa; suna gyaran tarunsu a jirgin ruwa. |
26643 | JHN 11:51 | Ya fadi wannan ne ba don kansa ba, amma sabo da shine babban firist, ya yi anabci ne cewa ya kamata Yesu ya mutu domin al'ummar; |
27296 | ACT 9:11 | Ubangiji ya ce masa, ''Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a; |
27300 | ACT 9:15 | Amma Ubangiji ya ce masa, ''Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al'ummai da sarakuna da 'ya'yan Isra'ila; |
27325 | ACT 9:40 | Bitrus ya fitar da su duka daga cikin dakin, ya durkusa, ya yi addu'a; sai, ya juya wurin gawar, ya ce, ''Tabita, tashi.'' Ta bude idanunta, da ta ga Bitrus ta zauna, |
27624 | ACT 17:32 | Da mutanen Atina sun ji batun tashi daga matattu, wadansu suka yi wa Bulus ba'a; amma wadansu kuma sun ce, ''Za mu saurare ka kuma, a kan wannan maganar.'' |
28382 | ROM 15:11 | Kuma.” Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi.” |
30051 | HEB 2:7 | Ka sa mutum ya gaza mala'iku; Ka nada shi da daukaka da girma. Bisa dukkan hallitta. |