Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   Word?    February 25, 2023 at 00:20    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23240  MAT 2:2  ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.''
23268  MAT 3:7  Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa?
23316  MAT 5:13  Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane.
23349  MAT 5:46  Domin idan kuna kaunar wadanda suke kaunarku, wanne lada kuka samu? Ba haka masu karban haraji ma suke yi ba?
23350  MAT 5:47  Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba?
23376  MAT 6:25  Saboda haka ina gaya maku, kada ku damu a kan rayuwarku, game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha- ko kuwa jikinku, abin da za ku yi tufafi da shi. Ashe rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?
23377  MAT 6:26  Ku dubi tsuntsayen da ke sararin sama. Ai, ba su shuka, balle girbi, ba su kuma tarawa a cikin rumbuna, amma Ubanku na Sama na ciyar da su. Ashe, ba ku fi su martaba ba?
23378  MAT 6:27  Kuma wanene a cikinku, don damuwarsa, zai iya kara ko taki ga tsawon rayuwarsa?
23379  MAT 6:28  To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi furannin jeji, yadda suke girma. Ba su aiki, kuma ba su sakar kaya.
23381  MAT 6:30  Idan Allah yayi wa ciyawar jeji ado, wadda yau tana wanzuwa, gobe kuwa a jefa ta cikin murhu, ina misalin adon da za ya yi maku, ya ku masu karancin bangaskiya?
23382  MAT 6:31  Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?'
23388  MAT 7:3  Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba?
23389  MAT 7:4  Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon?
23394  MAT 7:9  Ko, kuwa wane mutum ne a cikin ku, dan sa zai roke shi gurasa, ya ba shi dutse?
23395  MAT 7:10  Ko kuwa in ya roke shi kifi, zai ba shi maciji?
23396  MAT 7:11  Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa?
23401  MAT 7:16  Za ku gane su ta irin ''ya'yansu. Mutane na cirar inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya?
23418  MAT 8:4  Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu?
23443  MAT 8:29  Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”
23452  MAT 9:4  Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, yace, ''Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?
23463  MAT 9:15  Sai Yesu ya ce masu, ''Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi.''
23515  MAT 10:29  Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba.
23535  MAT 11:7  Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa?
23536  MAT 11:8  Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna.
23537  MAT 11:9  Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi.
23544  MAT 11:16  Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna
23551  MAT 11:23  Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu.
23561  MAT 12:3  Amma Yesu ya ce masu, “Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi?
23562  MAT 12:4  Yadda ya shiga gidan Allah, ya ci gurasar alfarwa da doka ta hana shi ko mazan da ke tare da shi su ci, sai dai Firistoci ne kawai doka ta basu damar ci?
23563  MAT 12:5  Sa'annan ba ku karanta cikin shari'a cewa, a ranar Asabaci, Firistoci da ke cikin haikali na sabawa ranar Asabaci, amma kamar ba su yi laifi ba?
23569  MAT 12:11  Yesu ya ce masu, “Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba?
23584  MAT 12:26  Idan Shaidan ya fitar da Shaidan, ya rabu gaba da kansa. Yaya mulkin sa za ya tsaya?
23585  MAT 12:27  Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku.
23587  MAT 12:29  Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa.
23592  MAT 12:34  Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana.
23606  MAT 12:48  Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, “Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?”
23635  MAT 13:27  Bayin mai gonar kuwa suka zo suka ce masa, maigida, ashe ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? ya ya aka yi ta kasance da ciyayi?
23659  MAT 13:51  Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, “I”.
23663  MAT 13:55  Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba?
23664  MAT 13:56  Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa?
23704  MAT 15:2  “Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.”
23718  MAT 15:16  Yesu ya ce, “Ku ma har yanzu ba ku da fahimta?
23719  MAT 15:17  Ko baku gani ba duk abin da ke shiga baki zuwa ciki ta haka yake fita zuwa salga?
23749  MAT 16:8  Yesu yana sane da wannan sai ya ce, “Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane?
23750  MAT 16:9  Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba?
23751  MAT 16:10  Ko gurasa bakwai ga mutum dubu hudu, da kuma kwanduna nawa kuka dauka ba?
23752  MAT 16:11  Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.”
23754  MAT 16:13  A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, “Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake?
23767  MAT 16:26  Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa?
23786  MAT 17:17  Yesu ya amsa ya ce, “Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.”
23794  MAT 17:25  Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?”
23808  MAT 18:12  Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba?
23817  MAT 18:21  Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?''
23835  MAT 19:4  Yesu ya amsa ya ce, ''Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace?
23848  MAT 19:17  Yesu ya ce masa, ''Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin.''
23874  MAT 20:13  Amma mai gonar ya amsa wa daya daga cikin su, ya ce, 'Aboki na, ban yi maku laifi ba. Ai mun shirya zan biya ku yadda ake biya a yini, ko ba haka ba?
23876  MAT 20:15  Ashe, ba daidai bane a gare ni, in yi abin da na ga dama da mallaka ta? Ko kishi ne kuke yi saboda kirki na?'
23923  MAT 21:28  Amma me kuke tunani? Wani mutum yana da 'ya'ya biyu. Ya je wurin na farkon yace, 'Da, je ka kayi aiki yau a cikin gona.'
23935  MAT 21:40  To idan me gonar ya zo, me zai yiwa manoman?
23958  MAT 22:17  To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?”
23959  MAT 22:18  Amma Yesu ya gane muguntarsu yace, “Don me kuke gwada ni, ku munafukai?
23969  MAT 22:28  To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta.”
23983  MAT 22:42  Yace, “Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?” Suka ce masa, ''Dan Dauda ne.”
24004  MAT 23:17  Ku wawayen makafi! wanene yafi girma, zinariyar ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?
24006  MAT 23:19  Ku makafi! Wanene yafi girma, baikon ko kuwa bagadin da yake kebe baikon ga Allah?
24020  MAT 23:33  macizai, Ku 'ya'yan ganshekai, Yaya zaku tsere wa hukuncin Gidan wuta?
24028  MAT 24:2  Amma ya amsa masu yace, “kun ga dukkan wadannan abubuwan? Ina gaya maku gaskiya, ba ko dutse daya da za'a bari akan dan'uwansa wanda ba za'a rushe shi ba.”
24071  MAT 24:45  To wanene amintaccen bawannan mai hikima, wanda maigidan sa ya sa ya kula mar da gida, domin ya ba su abinci a kan lokaci?
24114  MAT 25:37  Sa'annan masu adalcin za su amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa muka baka abinci? Ko kana jin kishi muka baka ruwan sha?
24115  MAT 25:38  Kuma yaushe muka ganka kana bakunci har muka baka masauki? Ko kuma kana huntanci da muka tufatar da kai?
24131  MAT 26:8  Amma da almajiransa suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Ina dalilin yin irin wannan asara?
24133  MAT 26:10  Amma da yake Yesu ya san tunaninsu, sai yace masu, “Don me kuke damun matar nan? Ta yi abu mai kyau domina.
24163  MAT 26:40  Ya koma wurin almajiran ya same su suna barci, sai ya cewa Bitrus, “Kai, ba zaku yi tsaro tare da ni ba koda sa'a daya?
24168  MAT 26:45  Sai Yesu ya koma wurin almajiran yace masu, “Har yanzu barci kuke kuna hutawa? Duba, lokaci ya kusato, kuma an bada Dan mutum ga hannun masu zunubi.
24176  MAT 26:53  Ko kana tunanin ba zan iya kiran Ubana ba, ya kuma aiko da rundunar Mala'iku fiye da goma sha biyu?
24178  MAT 26:55  A wannan lokacin Yesu yace wa taron, “Kun zo da takubba da kulake ku kama ni kamar dan fashi? Ina zaune kowace rana a haikali ina koyarwa, amma baku kama ni ba.
24185  MAT 26:62  Babban Firist din ya tashi tsaye yace masa, “Ba zaka ce komai ba? Wace irin shaida ce ake yi akanka?”
24188  MAT 26:65  Sai babban firist din ya yayyaga rigarsa, yana cewa, “Yayi sabo! don me ku ke neman wata shaida kuma? Duba, yanzu kun ji sabon.
24202  MAT 27:4  yace, “Na yi zunubi ta wurin cin amanar mara laifi.” Amma sukace, “Ina ruwan mu? Ka ji da shi da kanka?”
24215  MAT 27:17  To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu, “Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?”
24308  MRK 1:24  Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah”.
24311  MRK 1:27  Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!”
24336  MRK 2:7  Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi “sai Allah kadai?”
24337  MRK 2:8  Nan da nan Yesu ya sani a ruhunsa, abinda suke tunani a tsakaninsu. Ya ce masu, “Me ya sa kuke tunanin wannan a zuciyarku?
24348  MRK 2:19  Sai Yesu yace masu, “Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su? muddin suna tare da ango ba za su yi azumi ba.
24354  MRK 2:25  Yace masu, Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi?
24361  MRK 3:4  Sai ya ce wa mutane, “Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? “Amma suka yi shiru.
24380  MRK 3:23  Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, “Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan?
24390  MRK 3:33  Ya amsa masu, “Dacewa su wanene uwa-ta da “yan'uwa na?
24405  MRK 4:13  Ya ce masu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? yaushe za ku fahimci sauran?
24413  MRK 4:21  ya ce masu, “Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a karkashin gado? ku kan kawo ta ne don ku dora ta a kan madorinta.
24422  MRK 4:30  Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?
24432  MRK 4:40  Ya ce masu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu baku da bangaskiya ne?”
24440  MRK 5:7  Ya tada muryarsa da karfi ya ce, ina ruwa na da kai? Yesu Dan Allah Madaukaki Ina rokon ka da sunan Allah kada ka bani wahala,
24442  MRK 5:9  Ya tambaye shi, “Yaya sunanka? Ya ce suna na tari gama muna da yawa.
24478  MRK 6:2  Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa?
24479  MRK 6:3  Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu.
24514  MRK 6:38  Sai ya ce dasu, “Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani.” Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu.”
24550  MRK 7:18  Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba,
24586  MRK 8:17  Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, “Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?”