23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
23275 | MAT 3:14 | Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?” |
23440 | MAT 8:26 | Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. |
23443 | MAT 8:29 | Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” |
23568 | MAT 12:10 | Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, “Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?” Domin su zarge shi a kan zunubi. |
23581 | MAT 12:23 | Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?” |
23618 | MAT 13:10 | Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, “Don me ka ke yi wa taron magana da misali?” |
23697 | MAT 14:31 | Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?” |
23714 | MAT 15:12 | Sai al'majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?” |
23736 | MAT 15:34 | Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.” |
23756 | MAT 16:15 | Ya ce masu, “Amma ku wa kuke ce da ni?” |
23779 | MAT 17:10 | Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, “Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?” |
23788 | MAT 17:19 | Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce, “Me ya sa muka kasa fitar da shi?” |
23793 | MAT 17:24 | Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?” |
23794 | MAT 17:25 | Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?” |
23836 | MAT 19:5 | Shi wanda ya yi su kuma ya ce, “Saboda wannan dalilin, mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya hade da matarsa, su biyun su zama jiki daya?” |
23905 | MAT 21:10 | Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, “Wanene wannan?” |
23915 | MAT 21:20 | Da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suka ce, “Kaka bishiyar bauren ta bushe nan da nan?” |
23918 | MAT 21:23 | Sa'adda Yesu ya shiga haikalin, sai manyan fristocin da shugabannin jama'a suka zo suka same shi yayin da yake koyarwa, suka ce, “Da wane iko kake yin wadannan abubuwa?” |
23920 | MAT 21:25 | Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?” Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, “In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?' |
23926 | MAT 21:31 | Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?” Suka ce, “na farkon.” Yesu ya ce masu, “Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku. |
23961 | MAT 22:20 | Yesu yace masu, “Hoto da sunan wanene wadannan?” |
23983 | MAT 22:42 | Yace, “Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?” Suka ce masa, ''Dan Dauda ne.” |
23986 | MAT 22:45 | Idan Dauda ya kira Almasihu 'Ubangiji,' ta yaya ya zama dan Dauda?” |
24029 | MAT 24:3 | Yayin da ya zauna a kan dutsen zaitun, almajiran sa suka zo wurin sa a boye suka ce, “me zai zama alamar zuwanka da kuma na karshen duniya?” |
24138 | MAT 26:15 | yace, ''Me kuke da niyyar bani idan na mika maku shi?” Suka auna masa azurfa talatin. |
24140 | MAT 26:17 | To a rana ta fari na idin ketarewa almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Ina kake so mu shirya maka da zaka ci abincin idin ketarewa?” |
24145 | MAT 26:22 | Suka yi bakin ciki, suka fara tambayarsa daya bayan daya, ''Na tabbata ba ni bane ko, Ubangiji?” |
24148 | MAT 26:25 | Yahuza da zai bada shi yace, “Mallam ko ni ne?” Yace masa, “Ka fada da kanka.” |
24185 | MAT 26:62 | Babban Firist din ya tashi tsaye yace masa, “Ba zaka ce komai ba? Wace irin shaida ce ake yi akanka?” |
24189 | MAT 26:66 | Menene tunaninku?” Suka amsa sukace, “Ya cancanci mutuwa.” |
24202 | MAT 27:4 | yace, “Na yi zunubi ta wurin cin amanar mara laifi.” Amma sukace, “Ina ruwan mu? Ka ji da shi da kanka?” |
24209 | MAT 27:11 | Sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamna ya kuma tambaye shi, “Kai sarkin Yahudawa ne?” Yesu ya amsa, “Haka ka fada.” |
24211 | MAT 27:13 | Sai Bilatus yace masa, “Baka ji dukan zarge-zargen da ake yi maka ba?” |
24215 | MAT 27:17 | To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu, “Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?” |
24219 | MAT 27:21 | Sai gwamna ya tambayesu, “Wa kuke so a sakar maku?” Sukace, “Barabbas.” |
24220 | MAT 27:22 | Bilatus yace masu, “Me zan yi da Yesu wanda ake kira Almasihu?” Sai duka suka amsa, “A gicciye shi.” |
24221 | MAT 27:23 | Sai yace, “Don me, wane laifi ya aikata?” Amma suka amsa da babbar murya, “A gicciye shi” |
24244 | MAT 27:46 | Wajen karfe uku, Yesu ya tada murya mai karfi yace, “Eli, Eli lama sabaktani?” wanda ke nufin, “Allahna, Allahna, don me ka yashe ni?” |
24336 | MRK 2:7 | Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi “sai Allah kadai?” |
24345 | MRK 2:16 | Da Marubuta wadanda su ke Farisawa, sun ga cewa Yesu na cin abinci da masu zunubi da masu karbar haraji, sai su ka ce wa almajiransa, “Me ya sa ya ke ci da masu karbar haraji da mutane masu zunubi?” |
24347 | MRK 2:18 | Almajiran Yahaya da Farisawa suna azumi, sai wadansu mutane suka zo suka ce, “Don me almajiran Yahaya da almajiran Farisawa na azumi amma na ka almajiran ba su yi?” |
24353 | MRK 2:24 | Sai Farisawa su ka ce masa, “Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?” |
24430 | MRK 4:38 | Yesu kuwa na daga karshen bayan jirgin a kan kujera, yana barci, sai suka tashe shi, suka ce masa “Malam za mu hallaka ba ka kula ba?” |
24432 | MRK 4:40 | Ya ce masu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu baku da bangaskiya ne?” |
24433 | MRK 4:41 | Sai suka tsorata kwarai suka ce wa juna, “wanene wannan kuma, wanda har Iska da teku ma suke yi masa biyayya?” |
24463 | MRK 5:30 | Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce “wanene ya taba rigata?” |
24464 | MRK 5:31 | Almajiransa suka ce, “ a cikin wannan taron mutane da yawa ka ce wanene ya taba ni?” |
24468 | MRK 5:35 | Sa'adda ya ke magana da ita sai ga mutane daga gidan shugaban majami'a suka ce “Diyarka ta mutu me ya sa za ka dami malam?” |
24472 | MRK 5:39 | Sa'adda ya shiga gidan ya ce da mutane “Me ya sa kuke damuwa da kuka?” Yarinyar ba ta mutu ba barci ta ke yi. |
24500 | MRK 6:24 | Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, “ me zan ce ya bani?” Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma. |
24513 | MRK 6:37 | Amma sai ya ba su amsa ya ce,”Ku ku basu abinci su ci mana”. Sai suka ce da shi, “ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?” |
24537 | MRK 7:5 | Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, “Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?” |
24573 | MRK 8:4 | Almajiransa suka amsa masa cewa, “A ina za mu iya samu gurasa a wannan jeji da zai ishi wadannan mutane haka?” |
24574 | MRK 8:5 | Ya tambaye su, “gurasa nawa kuke da su?” Sai suka ce, “Bakwai.” |
24586 | MRK 8:17 | Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, “Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?” |
24590 | MRK 8:21 | Ya ce masu, “har yanzu baku gane ba?” |
24592 | MRK 8:23 | Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi “kana ganin wani abu kuwa?” |
24596 | MRK 8:27 | Yesu da almajiransa sun shiga kauyukan kaisariya ta Filibi. Da suke kan hanya, sai ya tambaye su, “Shin wanene mutane ke ce da ni?” |
24598 | MRK 8:29 | Ya tambaye su, “Amma me ku ke ce da ni?” Bitrus ya ce, “Kai ne Almasihu.” |
24618 | MRK 9:11 | Suka tambaye shi yaya malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?” |
24623 | MRK 9:16 | Ya tambayi almajiransa, “ Wacce muhawara ce kuke yi da su?” |
24635 | MRK 9:28 | Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?” |
24756 | MRK 12:14 | Da suka zo, suka ce masa, “Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. “Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?” |
24770 | MRK 12:28 | Sai wani malamin attuara ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu yana ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wanne Umarni ne mafi girma dukka?” |
24779 | MRK 12:37 | Dauda da kansa ya kira shi 'Ubangiji; To, ta yaya ya Almasihu zai zama Dan Dauda?” Babban taron jama'ar suka saurare shi da murna. |
24842 | MRK 14:19 | Sai suka damu suka tambaye shi daya bayan daya suna cewa “Hakika bani bane ko?” |
24907 | MRK 15:12 | Bilatus ya sake yi masu tambaya “Yaya zan yi da Sarkin Yahudawa?” |
24929 | MRK 15:34 | A sa'a ta tara, Yesu ya tada murya da karfi ya ce Eloi, Eloi lamathsabathani?” Ma'ana Ya Allahna Ya Allahna, me ya sa ka yashe ni?” |
24945 | MRK 16:3 | Suna magana a tsakaninsu suna cewa, wanene zai gangarar da dutsen da aka rufe bakin kabarin da shi?” |
24996 | LUK 1:34 | Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?” |
25028 | LUK 1:66 | Kuma dukan wadanda suka ji su, sun ajiye su a cikin zuciyarsu, suna cewa, “To me wannan yaro zai zama ne?” Domin hannun Ubangiji yana nan tare da shi. |
25091 | LUK 2:49 | Ya ce masu, “Don me kuke nema na? Ba ku sani cewa dole in kasance a gidan Ubana ba?” |
25104 | LUK 3:10 | Sai mutanen da ke cikin taron jama'ar suka tambaye shi cewa, “To me za mu yi?” |
25106 | LUK 3:12 | Masu karban haraji ma suka zo domin a yi masu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?” |
25108 | LUK 3:14 | Wasu sojoji ma suka tambaye shi cewa, “To, mu fa? Yaya za mu yi?” Ya ce masu, “Kada ku kwace wa wani kudi, kada ku kuma yi wa wani zargin karya. Ku dogara ga albashinku.” |
25154 | LUK 4:22 | Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, “Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?” |
25197 | LUK 5:21 | Marubuta da Farisawa suka fara sukar wannan, suna cewa, “Wanene wannan da ke sabo? Wa zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai ba?” |
25199 | LUK 5:23 | Wanne ne ya fi sauki a ce, 'An yafe zunubanka' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya?” |
25206 | LUK 5:30 | Amma Farisawa da Marubuta suka fara korafi ga almajiransa, suna cewa, “Don menene kuna ci da sha tare da masu karban haraji da mutane masu zunubi?” |
25209 | LUK 5:33 | Sun ce masa, “Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?” |
25217 | LUK 6:2 | Amma wasu daga cikin Farisawa suka ce, “Saboda me kuke yin abin da bai halatta a yi a ranar Asabaci ba?” |
25283 | LUK 7:19 | Sai Yahaya ya kira biyu daga cikin almajiransa, ya aike su wurin Ubangiji, suka ce da shi, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?” |
25284 | LUK 7:20 | Sa'adda suka zo kusa da Yesu, sai mutanen suka ce, “Yahaya Mai Baftisma, ya aiko mu, mu tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?” |
25306 | LUK 7:42 | Da yake ba su da kudin da za su iya biyan sa, sai ya yafe masu, su duka biyu. A cikin su biyu, wanne ne zai fi nuna kauna ga wannan mutum?” |
25339 | LUK 8:25 | Daga nan sai ya ce da su, “Ina bangaskiyar ku?” Almajiran suka tsorata suka yi mamakin abin da ya faru nan take. Suka ce wa junansu, “Wanene wannan wanda har zai ba iska da ruwa umarni kuma su yi masa biyayya?” |
25344 | LUK 8:30 | Sa'annan Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Sai ya ba da amsa, “Suna na dubbai.” Ya ce haka ne domin aljanu da yawa sun shiga wannan mutum. |
25359 | LUK 8:45 | Yesu ya ce, “Wanene ya taba ni?” Wadanda suke kewaye da shi, kowa ya ce bai taba shi ba, Bitrus ya ce, “Shugaba, mutane da yawa suna ta taruwa kewaye da kai suna ta matsowa kusa da kai.” |
25379 | LUK 9:9 | Hirudus ya ce, “Ba zai yiwu Yahaya ne ba, domin na datse masa kai. To, wanene wannan da ni ke jin wadannan abubuwa a kansa?” Daga nan sai ya cigaba da neman hanyar da zai ga Yesu. |
25388 | LUK 9:18 | Wata rana Yesu yana yin addu'a shi kadai, sai almajiransa suka zo sai ya tambaye su, “Wa mutane suke cewa da ni?” |
25390 | LUK 9:20 | Ya tambaye su, “Ku fa? Wa kuke cewa da ni?” Bitrus ya amsa, “Kai Almasihu ne wanda ya zo daga wurin Allah.” |
25424 | LUK 9:54 | Sa'adda biyu daga cikin almajiransa, wato Yakubu da Yahaya suka ga haka, suka ce, “Ubangiji, kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama, ta hallaka su?” |
25457 | LUK 10:25 | Sai ga wani malamin shari'ar Yahudawa, ya zo ya gwada shi da cewa, “Malam, me zan yi domin in gaji rai na har abada?” |
25461 | LUK 10:29 | Amma, malamin ya na so ya 'yantar da kansa, sai ya ce da Yesu, “To, wanene makwabcina?” |
25468 | LUK 10:36 | A cikinsu ukun nan, wanene kake tsammani makwabcin wannan mutum da ya fada hannun 'yan fashi?” |
25487 | LUK 11:13 | To, da yake ku da kuke masu mugunta kun san ku ba 'yanyan ku abu mai kyau. Yaya fa ga Ubanku wanda yake cikin sama, za ya ba da Ruhu Mai Tsarki ga wadanda suka roke shi?” |
25542 | LUK 12:14 | Yesu ya ce masa, “Kai, wanene ya sa ni in zama alkali, ko matsakanci a kanku?” |
25569 | LUK 12:41 | Sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, mu ka ke fadawa wannan misali, ko ga kowa da kowa ne?” |
25610 | LUK 13:23 | Sai wani ya ce masa, “Ubangiji, wadanda za su sami ceto kadan ne?” Sai ya ce masu, |
25627 | LUK 14:5 | Sai yace masu, “Wanene a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya fadi a rijiya ran Asabaci, ba zai fitar da shi nan da nan ba?” |