Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   !    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

70  GEN 3:14  Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.
90  GEN 4:10  Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa.
95  GEN 4:15  Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi.
195  GEN 8:11  Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya.
232  GEN 9:26  Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem.
418  GEN 17:20  Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma!
450  GEN 18:25  Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”
467  GEN 19:9  Sai mutanen birnin suka amsa, “Ba mu wuri! Wannan mutum ya zo nan kamar baƙo, ga shi yanzu yana so yă zama alƙali! Za mu wulaƙanta ka fiye da su.” Suka ci gaba da matsa wa Lot lamba, suka matsa kusa domin su fasa ƙofar.
473  GEN 19:15  Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”
475  GEN 19:17  Da suka fitar da su, sai ɗaya daga cikin mala’ikun ya ce, “Ku gudu domin ranku; kada ku duba baya, kada kuma ku tsaya ko’ina cikin kwarin! Ku gudu zuwa cikin duwatsu, don kada a hallaka ku!
476  GEN 19:18  Amma Lot ya ce musu, “A’a, ranka yă daɗe, ka yi haƙuri!
549  GEN 22:1  Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
555  GEN 22:7  sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?”
559  GEN 22:11  Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
689  GEN 25:30  Ya ce wa Yaƙub, “Ina roƙonka, ka ɗan ɗiba mini faten nan! Ina fama da yunwa!(Shi ya sa aka kira shi Edom.)
702  GEN 26:9  Saboda haka Abimelek ya aika Ishaku yă je, sa’an nan ya ce, “Tabbatacce ita matarka ce! Me ya sa ka ce, ‘Ita ’yar’uwata ce?’ ” Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”
713  GEN 26:20  Amma makiyayan Gerar suka yi faɗa da na Ishaku suka ce, “Ruwan namu ne!Saboda haka Ishaku ya ba wa rijiyar suna Esek, domin sun yi faɗa da shi.
725  GEN 26:32  A wannan rana bayin Ishaku suka zo suka faɗa masa game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, “Mun sami ruwa!
761  GEN 27:33  Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce, “To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!
762  GEN 27:34  Sa’ad da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya fashe da kuka mai zafi kuma da ƙarfi, ya ce wa mahaifinsa, “Ka albarkace ni, ni ma, baba!
766  GEN 27:38  Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Ka albarkace ni ni ma, baba!Sai Isuwa ya ɗaga murya ya yi kuka.
791  GEN 28:17  Ya ji tsoro, ya kuma ce, “Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama.”
821  GEN 29:25  Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”
832  GEN 30:1  Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!
842  GEN 30:11  Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!Saboda haka ta ba shi suna Gad.
844  GEN 30:13  Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.
931  GEN 32:3  Sa’ad da Yaƙub ya gan su sai ya ce, “Wannan sansanin Allah ne!Saboda haka ya kira wannan wuri Mahanayim.
1103  GEN 37:19  Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa!
1114  GEN 37:30  Ya koma wurin ’yan’uwansa ya ce, “Yaron ba ya can! Ina zan bi yanzu?”
1117  GEN 37:33  Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”
1144  GEN 38:24  Bayan misalin wata uku sai aka faɗa wa Yahuda cewa, “Tamar, surukarka ta yi laifin karuwanci, a sakamakon haka yanzu ta yi ciki.” Yahuda ya ce, “A fid da ita, a ƙone!
1149  GEN 38:29  Amma sa’ad da ya janye hannunsa, sai ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “Wato, haka ne ka keta ka fito!Sai aka ba shi suna Ferez.
1157  GEN 39:7  bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!
1162  GEN 39:12  Sai ta cafke shi a riga, ta ce, “Zo ka kwana da ni!Amma ya bar rigarsa a hannunta, ya gudu ya fita daga gidan.
1164  GEN 39:14  sai ta kira bayin gidan ta ce musu, “Duba, an kawo mana wannan mutumin Ibraniyawa don yă ci mutuncinmu! Ya zo nan don yă kwana da ni, amma na yi ihu.
1239  GEN 41:43  Ya sa shi ya hau keken yaƙi a matsayi mai binsa na biyu, mutane kuwa suka yi shela a gabansa suna cewa, “A ba da hanya!Ta haka ya sa shi shugaba a kan dukan ƙasar Masar.
1262  GEN 42:9  Sa’an nan ya tuna da mafarkansa game da su, ya kuma ce musu, “Ku ’yan leƙen asiri ne! Kun zo don ku leƙi asirin ƙasar ku ga inda ba ta da tsaro.”
1265  GEN 42:12  Ya ce musu “Sam! Kun zo ne ku ga inda ƙasarmu babu tsaro.”
1267  GEN 42:14  Yusuf ya ce musu, “Daidai ne yadda na faɗa muku. Ku ’yan leƙen asiri ne!
1269  GEN 42:16  Ku aiki ɗaya daga cikinku yă kawo ɗan’uwanku; za a sa sauranku a kurkuku, saboda a gwada maganarku a ga ko gaskiya ce kuke faɗi. In ba haka ba, to, da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!
1288  GEN 42:35  Yayinda suke juyewa hatsi daga buhunansu, sai ga ƙunshin azurfan kowane mutum a buhunsa! Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshe-ƙunshen kuɗi, suka firgita.
1289  GEN 42:36  Yaƙub mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashin ’ya’yana. Yusuf ya rasu, Simeyon kuma ba ya nan, yanzu kuma kuna so ku ɗauki Benyamin. Kome yana gāba da ni!
1332  GEN 44:7  Amma suka ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake faɗin irin waɗannan abubuwa? Allah yă sawwaƙe bayinka su yi irin wannan abu!
1342  GEN 44:17  Amma Yusuf ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka! Mutumin da aka sami kwaf ɗin a hannunsa ne kaɗai zai zama bawana. Sauranku, ku koma ga mahaifinku da salama.”
1357  GEN 44:32  Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin a wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa yă zauna a kaina a gaban mahaifina, dukan raina!
1359  GEN 44:34  Yaya zan koma ga mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? A’a! Kada ka bari in ga baƙin cikin da zai auko wa mahaifina.”
1360  GEN 45:1  Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, “Kowa yă tashi daga gabana!Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga ’yan’uwansa.
1362  GEN 45:3  Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa.
1363  GEN 45:4  Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar!
1383  GEN 45:24  Sa’an nan ya sallami ’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!
1385  GEN 45:26  Suka faɗa masa, “Yusuf yana da rai! Gaskiya, shi ne mai mulkin dukan Masar.” Gaban Yaƙub ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.
1387  GEN 45:28  Sai Yaƙub ya ce, “Na yarda! Ɗana Yusuf yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”
1389  GEN 46:2  Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.”
1434  GEN 47:13  A yanzu, a cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwa ta yi tsanani ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka shiga matsananciyar wahala!
1440  GEN 47:19  Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakinmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna. Ka ba mu iri don mu rayu, kada mu mutu, don kuma kada gonakin ƙasarmu su zama kango.”
1481  GEN 49:7  La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila.
1584  EXO 3:4  Da Ubangiji ya ga Musa ya matso don yă duba, sai Allah ya yi kira daga cikin ƙaramin itacen ya ce, “Musa! Musa!Sai Musa ya amsa ya ce, “Ga ni.”
1637  EXO 5:4  Amma sarkin Masar ya ce wa, “Musa da Haruna, don me kuke hana mutane yin aikinsu? Ku koma wurin aikinku!
1649  EXO 5:16  Ba a ba wa bayinka tattaka, duk da haka ana ce mana, ‘Ku yi tubula!Ana wa bayinka dūka, amma fa laifin na mutanenka ne.”
1650  EXO 5:17  Fir’auna ya ce, “Ku ragwaye ne! Shi ya sa kuke cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya wa Ubangiji.’
1654  EXO 5:21  sai suka ce, “Bari Ubangiji yă duba, yă kuma hukunta ku! Kun maishe mu abin ƙyama ga Fir’auna da bayinsa, kuka kuma sa musu takobi a hannunsu don su kashe mu.”
1657  EXO 6:1  Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!
1788  EXO 10:10  Fir’auna ya ce, “Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba! A fili yake kuna da niyyar mugunta.
1789  EXO 10:11  Sam! Wannan ba zai taɓa yiwu ba, sai ko maza kaɗai su tafi su yi wa Ubangiji sujada, gama abin da kuke so ke nan.” Sa’an nan aka kori Musa da Haruna daga gaban Fir’auna.
1806  EXO 10:28  Fir’auna ya ce wa Musa, “Fita, ka ba ni wuri! Ka mai da hankali, kada ka ƙara bayyana a gabana, gama ran da ka sāke ganin fuskata, a ran nan za ka mutu.”
1815  EXO 11:8  Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.
1850  EXO 12:33  Masarawa suka matsa wa Isra’ilawa su fita daga ƙasarsu da sauri. Gama mutanen Masar sun ce, “Ai, za mu mutu duka, in ba su tafi ba!
1895  EXO 14:5  Sa’ad da aka faɗa wa Fir’auna cewa Isra’ilawa sun gudu, sai Fir’auna da bayinsa suka canja ra’ayinsu game da su, suka ce, “Me muka yi? Mun bar Isra’ilawa suka tafi, mun kuwa rasa hidimarsu!
1902  EXO 14:12  Ba mu faɗa maka a Masar ba, cewa ‘Ka bar mu mu bauta wa Masarawa’? Ai, da ya fi mana mu bauta wa Masarawa, da a ce mu mutu a hamada!
2470  EXO 32:31  Don haka Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Kaito, mutanen nan sun yi zunubi mai girma! Sun yi wa kansu allolin zinariya.
3098  LEV 13:45  “Mutum mai wannan cuta mai yaɗuwa dole yă sa yagaggun riguna, yă kuma bar gashin kansa ba gyara, yă rufe sashe ƙasa na fuskarsa, sa’an nan yă riga cewa, ‘Marar tsarki! Marar tsarki!
4024  NUM 10:35  Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji! Ka sa maƙiyanka su warwatse; masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.”
4029  NUM 11:4  Wata rana, baƙin da suke cikinsu, suka fara kwaɗayin waɗansu abinci, har suka sa Isra’ilawa suka fara kuka, suna cewa, “Da mun sami nama mun ci mana!
4031  NUM 11:6  Amma ga shi yanzu ba mu da wani abin marmari; in ba wannan Manna ba!
4038  NUM 11:13  Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!
4043  NUM 11:18  “Ka gaya wa mutane, ‘Ku tsarkake kanku don gobe, za ku ci nama. Ubangiji ya ji ku sa’ad da kuka yi kuka cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Ai, da ba mu da damuwa, gama lokacin da muke zama cikin Masar ba mu da damuwa!Yanzu Ubangiji zai ba ku nama, za ku kuma ci.
4046  NUM 11:21  Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!
4053  NUM 11:28  Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!
4054  NUM 11:29  Amma Musa ya amsa ya ce, “Kana kishi domina ne? Da ma a ce dukan mutanen Ubangiji annabawa ne, da ma a kuma ce Ubangiji ya sa Ruhunsa a kansu mana!
4073  NUM 12:13  Saboda haka sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Allah, ina roƙonka ka warkar da ita!
4103  NUM 13:27  Suka ce wa Musa, “Mun je ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana zub da madara da zuma! Ga kuma amfaninta.
4111  NUM 14:2  Dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, dukan taron kuwa suka ce musu, “Da ma mun mutu a Masar! Ko kuma a wannan hamada ma!
4122  NUM 14:13  Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji game da wannan! Da ikonka ka fitar da mutanen nan daga cikinsu.
4150  NUM 14:41  Amma Musa ya ce, “Don me kuke rashin biyayya da umarnin Ubangiji? Wannan ba zai yiwu ba!
4198  NUM 16:3  tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”
4202  NUM 16:7  ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!
4203  NUM 16:8  Musa ya kuma ce wa Kora, “Yanzu ku saurara, ku Lawiyawa!
4207  NUM 16:12  Sai Musa ya aika a kira Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab maza, amma suka ce, “Ba za mu zo ba!
4209  NUM 16:14  Ban da haka ma, ai, ba ka riga ka kai mu ƙasar mai zub da madara da zuma ba, ba ka ba mu gādon filaye da gonakin annabi ba, yanzu kuma kana so ka ruɗe mu. Mun ƙi, ba za mun zo ba!
4221  NUM 16:26  Ya gargaɗe taron ya ce, “Ku ƙaurace wa tentin waɗannan mugayen mutane! Kada ku taɓa kome da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”
4229  NUM 16:34  Da jin kukansu, dukan Isra’ilawa da suke kewaye da su suka gudu, suna ihu, “Ƙasa za tă haɗiye mu, mu ma!
4257  NUM 17:27  Sai Isra’ilawa suka ce wa Musa, “To, ai in haka ne, mun ƙare ke nan!
4315  NUM 20:3  Suka yi gunaguni wa Musa suka ce, “Da ma mun mutu sa’ad da ’yan’uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji!
4346  NUM 21:5  suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!
4358  NUM 21:17  Sai Isra’ilawa suka rera wannan waƙa, “Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya! Rera waƙa game da ita,
4370  NUM 21:29  Kaitonki, Mowab! Gunkinki Kemosh ya yashe mutanenki; aka kuma kama su, aka kai su bauta wajen Sihon sarkin Amoriyawa.
4405  NUM 22:29  Bala’am ya ce wa jakar “Domin kin wulaƙanta ni! Da a ce ina da takobi a hannuna da zan kashe ki nan take.”
4427  NUM 23:10  Wa zai iya ƙidaya ƙurar Yaƙub ko yă ƙidaya kashi ɗaya bisa huɗu na Isra’ila? Bari in mutu, mutuwar adali ƙarshena kuma yă zama kamar nasu!
4428  NUM 23:11  Balak ya ce wa Bala’am, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka, ka la’anta abokan gābana, sai ga shi albarka kake sa musu!
4440  NUM 23:23  Ba wata maitar da za tă ci Yaƙub, ba sihiri da zai cuci Isra’ila. Yanzu za a ce game da Yaƙub da Isra’ila, ‘Duba abin da Allah ya yi!