43 | GEN 2:12 | (Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.) |
224 | GEN 9:18 | ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.) |
240 | GEN 10:5 | (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.) |
249 | GEN 10:14 | Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa. |
329 | GEN 13:10 | Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.) |
339 | GEN 14:2 | suka tafi don su yaƙi Bera sarkin Sodom, Birsha sarkin Gomorra, Shinab sarkin Adma, Shemeber sarkin Zeboyim, da kuma sarkin Bela (wato, Zowar). |
340 | GEN 14:3 | Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri). |
344 | GEN 14:7 | Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar. |
345 | GEN 14:8 | Sai sarkin Sodom, sarkin Gomorra, sarkin Adma, sarkin Zeboyim da sarkin Bela (wato, Zowar), suka fita suka ja dāgā a Kwarin Siddim |
354 | GEN 14:17 | Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki). |
480 | GEN 19:22 | Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa can.” (Domin haka ne ake kira garin Zowar.) |
569 | GEN 22:21 | ɗan fari shi ne Uz, ɗan’uwansa kuma Buz, Kemuwel (shi ne mahaifin Aram), |
574 | GEN 23:2 | Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita. |
591 | GEN 23:19 | Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana. |
689 | GEN 25:30 | Ya ce wa Yaƙub, “Ina roƙonka, ka ɗan ɗiba mini faten nan! Ina fama da yunwa!” (Shi ya sa aka kira shi Edom.) |
866 | GEN 30:35 | A wannan rana ya ware dukan bunsurai da suke dabbare-dabbare da masu zāne-zāne, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare (duka da suke da fari-fari a jikinsu), da dukan baƙaƙen tumaki, ya sa su a hannun ’ya’yansa maza. |
1018 | GEN 35:6 | Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana. |
1031 | GEN 35:19 | Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem). |
1039 | GEN 35:27 | Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna. |
1042 | GEN 36:1 | Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom). |
1049 | GEN 36:8 | Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir. |
1060 | GEN 36:19 | Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu. |
1395 | GEN 46:8 | Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza (Yaƙub da zuriyarsa) waɗanda suka tafi Masar, Ruben ɗan farin Yaƙub. |
1399 | GEN 46:12 | ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul. |
1459 | GEN 48:7 | Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem). |
1628 | EXO 4:26 | Sai Ubangiji ya ƙyale shi. (A lokacin ta ce “angon jini,” tana nufin kaciya.) |
1775 | EXO 9:32 | Alkama da gero kam, ba a hallaka su ba, gama lokacin nunansu bai yi ba tukuna.) |
1810 | EXO 11:3 | (Ubangiji ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.) |
1944 | EXO 15:23 | Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara). |
1984 | EXO 16:36 | (Omer guda, daidai ne da kashi ɗaya bisa goma na Efa.) |
2359 | EXO 29:22 | “Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.) |
2657 | EXO 38:23 | tare da shi akwai Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, shi gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin.) |
3441 | LEV 23:38 | Waɗannan hadayu, ƙari ne a kan waɗannan na Asabbatan Ubangiji, haɗe kuma da kyautanku, da kome da kuka yi alkawari, da kuma hadayu yardar ran da za ku ba wa Ubangiji.) |
3458 | LEV 24:11 | Ɗan mutuniyar Isra’ila ya saɓi Sunan Ubangiji, ya kuma la’ana shi, saboda haka aka kawo shi wa Musa. (Sunan mahaifiyarsa Shelomit ne, ’yar Dibri na kabilar Dan.) |
3806 | NUM 5:13 | ta wurin kwana da wani dabam, wannan kuwa ya kasance a ɓoye ga mijinta, rashin tsarkinta kuwa bai tonu ba (da yake babu shaida, ba a kuma kama ta tana yi ba), |
3814 | NUM 5:21 | (a nan firist zai sa macen a ƙarƙashin la’anar rantsuwa cewa) “bari Ubangiji yă sa mutanenki su la’ance ki, su kuma yi Allah wadai da ke, sa’ad da Ubangiji ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbura. |
4063 | NUM 12:3 | (Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.) |
4087 | NUM 13:11 | Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf); |
4092 | NUM 13:16 | Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.) |
4096 | NUM 13:20 | Yaya ƙasar take? Tana da wadata, ko babu? Akwai itatuwa, ko babu? Ku yi iya ƙoƙarinku ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Lokacin farkon nunan inabi ne.) |
4098 | NUM 13:22 | Suka kuma haura ta Negeb, suka iso Hebron, inda Ahiman, da Sheshai, da Talmai, zuriyar Anak, suke zama. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.) |
4109 | NUM 13:33 | Mun ga Nefilimawa a can (zuriyar Anak sun fito ne daga Nefilim). Sai muka ga kanmu kamar fāra ne kawai, haka kuwa muke a gare su.” |
4520 | NUM 26:29 | Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa. |
4524 | NUM 26:33 | (Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.) |
4537 | NUM 26:46 | (Asher yana da ’ya mace da ake kira Sera.) |
4552 | NUM 26:61 | Amma Nadab da Abihu sun mutu sa’ad da suka miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.) |
4570 | NUM 27:14 | gama sa’ad da jama’a suka yi tayarwa saboda rashin ruwa a Hamadan Zin, ku biyu, ba ku kiyaye umarnina don ku ɗaukaka ni matsayin mai tsarki, a gabansu ba.” (Waɗannan su ne ruwaye na Meriba da Kadesh, a Hamadan Zin.) |
4758 | NUM 32:38 | haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye. |
4896 | DEU 1:2 | (Yakan ɗauki kwana goma sha ɗaya daga Horeb zuwa Kadesh Barneya ta hanyar Dutsen Seyir.) |
4952 | DEU 2:12 | Haka ma Horiyawa, a dā sun zauna a Seyir, amma zuriya Isuwa suka kore su. Suka hallaka Horiyawa da suke kafinsu, suka kuma zauna a wurinsu, kamar dai yadda Isra’ila ta yi a ƙasar da Ubangiji ya ba su a matsayin mallaka.) |
4963 | DEU 2:23 | Kusan abu ɗaya ya faru, sa’ad da Kaftorawa daga ƙasar Kaftor suka hallaka Awwiyawa, waɗanda dā suke zaune a yankin ƙauyukan da suke kewaye da Gaza. Suka zauna a wurinsu.) |
4986 | DEU 3:9 | (Hermon ne Sidoniyawa suke kira Siriyon, Amoriyawa kuwa suna kira shi Senir.) |
4988 | DEU 3:11 | (Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.) |
4991 | DEU 3:14 | Yayir na zuriyar Manasse ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawwot Yayir.) |
4993 | DEU 3:16 | Amma ga mutanen Ruben da mutanen Gad, na ba da yankin da ya tashi daga Gileyad, ya gangara zuwa Kwarin Arnon (tsakiyar kwarin kuwa shi ne iyaka) ya fita zuwa Kogin Yabbok, wanda yake shi ne iyakar Ammonawa. |
4994 | DEU 3:17 | Iyakarsa daga yamma kuwa shi ne Urdun a Araba, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas. |
4996 | DEU 3:19 | Amma matanku, yaranku da dabbobinku (na sani kuna da dabbobi masu yawa), su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku, |
5054 | DEU 4:48 | Wannan ƙasa ta tashi daga Arower a kewayen Kwarin Arnon zuwa Dutsen Siyon (wato, Hermon), |
5060 | DEU 5:5 | (A wannan lokaci na tsaya tsakanin Ubangiji da ku, don in furta muku maganar Ubangiji, domin kun ji tsoron wutar, ba ku kuwa hau dutsen ba.) Ya ce, |
5197 | DEU 10:9 | Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.) |
5276 | DEU 13:3 | in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,” |
5281 | DEU 13:8 | allolin mutanen kewayenku, ko na kusa, ko na nisa, daga wannan ƙarshen ƙasar zuwa wancan), |
5287 | DEU 13:14 | cewa mugaye sun taso a cikinku, suna rikitar da mutane a birni, suna cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ba ku sani ba), |
5316 | DEU 14:24 | Amma in wurin nan yana da nisa sosai, Ubangiji Allahnku kuma ya albarkace ku, ba za ku kuwa iya riƙe zakkarku ba (Saboda wurin da Ubangiji ya zaɓa yă sa Sunansa ya yi nisa sosai), |
5321 | DEU 14:29 | saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku. |
5877 | JOS 2:6 | (Amma ta kai su saman rufin ɗaki ta ɓoye su a ƙarƙashin karan rama da ta baza a rufin ɗaki.) |
5911 | JOS 3:16 | sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko. |
6040 | JOS 9:1 | To, sa’ad da dukan sarakunan yammancin Urdun suka ji waɗannan abubuwa, sai waɗanda suke kan tudu, da na cikin kwari a yammanci, da dukan waɗanda suke gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon (sarakunan Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa) |
6119 | JOS 11:10 | A lokacin nan Yoshuwa ya koma da baya ya ci Hazor da yaƙi, ya kuma kashe sarkinta da takobi. (Hazor ce babbar masarautan ƙasashen nan.) |
6135 | JOS 12:3 | Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga. |
6141 | JOS 12:9 | Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya |
6155 | JOS 12:23 | sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya sarkin Goyim a Gilgal, ɗaya |
6183 | JOS 13:27 | kuma a cikin kwari, Bet-Haram, Bet-Nimra, Sukkot da Zafon da kuma sauran masarautar Sihon sarkin Heshbon (gabashin Urdun, abin da ya kama har zuwa ƙarshen Tekun Kinneret). |
6187 | JOS 13:31 | da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu. |
6204 | JOS 14:15 | (Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi. |
6212 | JOS 15:8 | Sai kuma ta gangara zuwa Kwarin Ben Hinnom a gangaren kudancin birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima). Daga can ta haura zuwa kan tudun a yammancin Kwarin Hinnom, a arewancin ƙarshen Kwarin Refayim. |
6213 | JOS 15:9 | Daga kan tudun, iyakar ta nufi maɓulɓular ruwa na Neftowa, ta ɓullo a garuruwan da suke a Dutsen Efron, ta gangara zuwa Ba’ala (wato, Kiriyat Yeyarim). |
6214 | JOS 15:10 | Sa’an nan ta karkata yamma daga Ba’ala zuwa Dutsen Seyir, ta wuce ta gangaren Dutsen Yeyarim (wato, Kesalon), ta ci gaba zuwa Bet-Shemesh, ta bi zuwa Timna. |
6217 | JOS 15:13 | Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne wuri a Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron, bisa ga umarnin Ubangiji. (Arba shi ne mahaifin Anak.) |
6219 | JOS 15:15 | Daga can ya nufi Debir ya yi yaƙi da mutanen da suke zama a can (Dā sunan Debir, Kiriyat Sefer ne). |
6229 | JOS 15:25 | Hazor-Hadatta, Keriyot Hezron (wato, Hazor), |
6240 | JOS 15:36 | Sha’arayim, Aditayim, Gedera (Gederotayim ke nan). Garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. |
6253 | JOS 15:49 | Danna, Kiriyat Sanna (wato, Debir), |
6258 | JOS 15:54 | Humta, Kiriyat Arba (wato, Hebron) da Ziyor, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu. |
6264 | JOS 15:60 | Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim) da Rabba, garuruwa biyu ke nan da ƙauyukansu. |
6269 | JOS 16:2 | Ya ci gaba daga Betel (wato, Luz), ya zarce zuwa sashen Arkitawa na Atarot, |
6285 | JOS 17:8 | (Manasse ne yake da ƙasar Taffuwa, amma garin Taffuwa kansa, a kan iyakar Manasse ta mutanen Efraim ce.) |
6288 | JOS 17:11 | A yanki tsakanin Issakar da Asher, Manasse yana da waɗannan wurare, Bet-Sheyan, Ibileyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan En Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta (Na uku cikin jerin shi ne Nafot). |
6308 | JOS 18:13 | Daga can ta ƙetare zuwa gangaren Luz a kudu (wato, Betel), ta wuce zuwa Atarot Adda a tudun arewa na kwarin Bet-Horon. |
6309 | JOS 18:14 | Daga tudun da yake fuskantar Bet-Horon a kudu, iyakar ta juya kudu ta gefen yamma ta ɓullo a Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim), birnin Yahuda. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma. |
6323 | JOS 18:28 | Zela, Hayelef, birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima), Gibeya da Kiriyat, garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon kabilar Benyamin bisa ga iyalansu. |
6325 | JOS 19:2 | Waɗannan su ne wuraren da suka gāda. Beyersheba (ko Sheba), Molada, |
6331 | JOS 19:8 | da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu. |
6370 | JOS 19:47 | (Amma ya zama wa mutanen kabilar Dan da wahala su mallaki ƙasar da aka ba su gādo, saboda haka sai suka nufi Leshem suka ci su da yaƙi, suka karkashe mutanen wurin, suka mallake ta, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato, Dan.) |
6381 | JOS 20:7 | Saboda haka suka keɓe Kedesh a Galili a ƙasar kan tudu ta Naftali, Shekem a ƙasar kan tudu ta Efraim, da Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar kan tudu ta Yahuda. |
6393 | JOS 21:10 | (ga garuruwan da aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga iyalan Kohatawa na Lawiyawa, domin ƙuri’a ta farko ta fāɗa a kansu), |
6394 | JOS 21:11 | an ba su, Kiriyat Arba (wato, Hebron), da wurin kiwon da yake kewaye da ƙasar kan tudu ta Yahuda. (Arba shi ne kakan Anak.) |
6396 | JOS 21:13 | Sai aka ba zuriyar Haruna firist, ƙasar Hebron (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Libna, |
6404 | JOS 21:21 | A ƙasar kan tudu ta Efraim, aka ba su, Shekem (garin masu neman mafaka don sun yi kisa) da Gezer, |
6410 | JOS 21:27 | Aka ba wa zuriyar Gershon, waɗanda suke Lawiyawa, rabo. Daga rabin kabilar Manasse, Golan a cikin Bashan (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Be’eshtera, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan; |