1 | GEN 1:1 | A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. |
11 | GEN 1:11 | Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. |
12 | GEN 1:12 | Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. |
102 | GEN 4:22 | Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama. |
168 | GEN 7:8 | Biyu-biyu daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da tsuntsaye da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, |
175 | GEN 7:15 | Biyu-biyu na dukan halittu masu numfashi suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi. |
203 | GEN 8:19 | da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu. |
322 | GEN 13:3 | Daga Negeb, ya ci gaba da tafiyarsa a wurare dabam-dabam har ya kai tsakanin Betel da Ai, a inda dā ya kafa tentinsa na fari |
396 | GEN 16:14 | Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered. |
483 | GEN 19:25 | Haka ya hallakar da waɗannan birane da kuma kwarinsu gaba ɗaya, haɗe da dukan waɗanda suke zama a biranen, da kuma dukan shuke-shuke da suke cikin ƙasar. |
496 | GEN 19:38 | ’Yar ƙaramar ma ta haifi ɗa, ta kuwa ba shi suna Ben-Ammi, shi ne mahaifin Ammonawa a yau. |
602 | GEN 24:10 | Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor. |
654 | GEN 24:62 | Ishaku kuwa ya zo daga Beyer-Lahai-Royi, gama yana zama a Negeb. |
666 | GEN 25:7 | Duka-duka, Ibrahim ya yi shekara ɗari da saba’in da biyar. |
670 | GEN 25:11 | Bayan rasuwar Ibrahim, Allah ya albarkaci ɗansa Ishaku wanda a lokacin yana zama kusa da Beyer-Lahai-Royi. |
676 | GEN 25:17 | Duka-duka Ishmayel ya yi shekara ɗari da talatin da bakwai; sai ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa. |
686 | GEN 25:27 | Yaran suka yi girma, Isuwa kuwa ya zama riƙaƙƙen maharbi, mutumin jeji, yayinda Yaƙub, shiru-shiru ne mai son zama a tentuna. |
845 | GEN 30:14 | A lokacin girbin alkama, sai Ruben ya je jeji ya ɗebo manta-uwa ya kawo wa mahaifiyarsa Liyatu. Sai Rahila ta ce wa Liyatu, “Ina roƙonki ki ɗan sam mini manta-uwa ɗanki.” |
846 | GEN 30:15 | Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?” Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.” |
847 | GEN 30:16 | Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare. |
863 | GEN 30:32 | Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana. |
864 | GEN 30:33 | Gaskiyata kuwa za tă zama mini shaida nan gaba, duk sa’ad da ka bincika a kan albashin da ka biya ni. Duk akuyar da take tawa da ba dabbare-dabbare ko babare-babare, ko ɗan ragon da ba baƙi ba, zai kasance sata na yi.” |
866 | GEN 30:35 | A wannan rana ya ware dukan bunsurai da suke dabbare-dabbare da masu zāne-zāne, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare (duka da suke da fari-fari a jikinsu), da dukan baƙaƙen tumaki, ya sa su a hannun ’ya’yansa maza. |
870 | GEN 30:39 | sai su yi barbara a gaban rassan. Sai kuwa su haifi ƙanana masu zāne dabbare-dabbare, ko babare-babare ko masu zāne-zāne. |
871 | GEN 30:40 | Sai Yaƙub yă ware ƙananan garken dabam, amma sai yă sa sauran su fuskanci dabbobin da suke dabbare-dabbare da kuma baƙaƙe da suke na Laban. Ta haka ya ware garkuna dabam domin kansa bai kuwa haɗa su da dabbobin Laban ba. |
874 | GEN 30:43 | Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna. |
882 | GEN 31:8 | In ya ce, ‘Dabbare-dabbare ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce, ‘Masu zāne-zāne ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi ƙananan masu zāne-zāne. |
884 | GEN 31:10 | “A lokacin ɗaukar cikin garken, na taɓa yin mafarki inda na ga bunsuran da suke barbara da garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne. |
886 | GEN 31:12 | Ya ce, ‘Ɗaga idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne, gama na ga dukan abin da Laban yake yin maka. |
1030 | GEN 35:18 | Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin. |
1079 | GEN 36:38 | Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi. |
1080 | GEN 36:39 | Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab. |
1190 | GEN 40:17 | A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.” |
1241 | GEN 41:45 | Fir’auna ya ba wa Yusuf suna Zafenat-Faneya, ya kuma ba shi Asenat ’yar Fotifera firist na On, ta zama matarsa. Yusuf kuwa ya zaga dukan ƙasar Masar. |
1288 | GEN 42:35 | Yayinda suke juyewa hatsi daga buhunansu, sai ga ƙunshin azurfan kowane mutum a buhunsa! Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshe-ƙunshen kuɗi, suka firgita. |
1353 | GEN 44:28 | Ɗayansu ya tafi daga gare ni, na kuwa ce, “Tabbatacce an yayyage shi kaca-kaca.” Ban kuwa gan shi ba tuntuni. |
1382 | GEN 45:23 | Ga kuma abin da ya aika wa mahaifinsa, jakuna goma da aka jibge da abubuwa mafi kyau na Masar, da jakuna mata guda goma ɗauke da hatsi da burodi da waɗansu tanade-tanade don tafiyarsa. |
1494 | GEN 49:20 | “Abincin Asher zai zama a wadace, zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki. |
1518 | GEN 50:11 | Sa’ad da Kan’aniyawa waɗanda suke zama a can suka ga makokin a masussukan Atad, sai suka ce, “Masarawa suna bikin makoki na musamman.” Shi ya sa ake kira wannan wurin da yake kusa da Urdun, Abel-Mizrayim. |
1661 | EXO 6:5 | Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina. |
1682 | EXO 6:26 | Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.” |
1690 | EXO 7:4 | ba zai saurare ku ba. Don haka zan miƙa hannuna a kan Masar, in murƙushe ta da bala’i iri-iri, bayan haka zan fitar da taron mutanen Isra’ila daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu girma. |
1714 | EXO 7:28 | Nilu zai cika da kwaɗi. Za su haura zuwa cikin fadanka da kan gadonka, cikin gidajen bayinka da kan mutanenka, cikin kwanonin toye-toyenka da na cin abincinka. |
1725 | EXO 8:10 | Aka jibga su tsibi-tsibi, ƙasar ta yi ɗoyi saboda su. |
1793 | EXO 10:15 | Suka rufe ƙasar har ta zama baƙi. Suka cinye abin da ƙanƙara ta rage, kowane tsiron da yake girma a gonaki, da dukan ’ya’yan itatuwa. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar. |
1834 | EXO 12:17 | “Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti domin a wannan rana ce na fitar da ku ɓangare-ɓangare daga Masar. Ku kiyaye wannan rana ta zama muku dawwammamiyar farilla wa tsara masu zuwa. |
1858 | EXO 12:41 | A ranar da shekara 430 ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan ɓangare-ɓangare na mutanen Ubangiji suka bar Masar. |
1868 | EXO 12:51 | A wannan rana, Ubangiji ya fito da Isra’ilawa ɓangare-ɓangare daga Masar. |
1892 | EXO 14:2 | “Ka faɗa wa Isra’ilawa, su juya su kafa sansani a Fi Hahirot, a tsakanin Migdol da teku. Za su kafa sansanin kai tsaye kusa da teku, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon. |
1899 | EXO 14:9 | Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon. |
1962 | EXO 16:14 | Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa. |
1985 | EXO 17:1 | Dukan taron Isra’ilawa suka kama tafiya daga Hamadar Sin, suka yi ta tafiya suna sauka a wurare dabam-dabam bisa ga umarnin Ubangiji. A ƙarshe suka sauka a Refidim, suka zauna a can, amma ba ruwan da jama’a za su sha. |
2021 | EXO 18:21 | Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. |
2025 | EXO 18:25 | Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. |
2161 | EXO 23:16 | “Ku yi Bikin Girbi da nunan fari na amfanin shuke-shuken gonarku. “Ku yi Bikin Tattarawa a ƙarshen shekara, sa’ad da kuka tattara amfani daga gonarku. |
2207 | EXO 25:11 | Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya. |
2324 | EXO 28:30 | Ka kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirji, don su kasance a zuciyar Haruna, a duk sa’ad da zai shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai koke-koken Isra’ilawa a gaban Ubangiji. |
2332 | EXO 28:38 | Zai kasance a goshin Haruna, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa baye-bayensu masu tsarki. Zai kasance a goshin Haruna kullayaumin, domin su zama abin karɓa ga Ubangiji. |
2354 | EXO 29:17 | Ka yayyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikin, da ƙafafun, da kan, ka haɗa su da gunduwoyin. |
2375 | EXO 29:38 | “Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya. |
2386 | EXO 30:3 | Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi. |
2393 | EXO 30:10 | Sau ɗaya a shekara, Haruna zai yi kafara a bisa ƙahoninsa. Dole a yi wannan kafara ta shekara-shekara da jinin kafara ta hadaya don zunubi daga tsara zuwa tsara. Gama bagaden mafi tsarki ne ga Ubangiji.” |
2425 | EXO 31:4 | don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla, |
2554 | EXO 35:22 | Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji. |
2564 | EXO 35:32 | don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla. |
2567 | EXO 35:35 | Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne. |
2578 | EXO 36:11 | Suka yi rami a gefe-gefen labulen da zaren ruwan bula, haka kuma suka yi da ɗayan gefen na biyu ɗin. |
2593 | EXO 36:26 | da rammuka arba’in na azurfa, biyu-biyu don kowane katako. |
2597 | EXO 36:30 | Ta haka aka sami katakai takwas da rammukan azurfa goma sha shida, biyu-biyu a ƙarƙashin kowane katako. |
2626 | EXO 37:21 | Toho ɗaya yana a ƙarƙashin rassa biyu waɗanda suke daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu yana a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku kuma yana a ƙarƙashin rassa biyu na uku, duka-duka rassa shida ne. |
2631 | EXO 37:26 | Suka dalaye saman da dukan gefe-gefen da kuma ƙahonin da zinariya zalla, suka kuma yi zubin zinariya kewaye da shi. |
2632 | EXO 37:27 | Suka yi zobai biyu na zinariya a ƙarƙashin zubin, biyu-biyu ɗaura da juna, don su riƙe sandunan da za a ɗauka shi. |
2657 | EXO 38:23 | tare da shi akwai Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, shi gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin.) |
2668 | EXO 39:3 | Suka bubbuga zinariya ta zama falle, suka yayyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita, tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha. |
2674 | EXO 39:9 | Ƙyallen maƙalawa a ƙirjin murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya-ɗaya ne. |
2689 | EXO 39:24 | Suka yi fasalin ’ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da lallausan lilin kewaye da gefe-gefen taguwar. |
2690 | EXO 39:25 | Suka yi ƙararrawa da zinariya zalla, suka sa su a tsakanin fasalin ’ya’yan rumman kewaye da gefe-gefen taguwa. |
2691 | EXO 39:26 | Aka jera ƙararrawan da ’ya’yan rumman bi da bi. Haka aka jera su kewaye da gefe-gefen taguwar aiki, yadda Ubangiji ya umarci Musa. |
2752 | LEV 1:6 | Zai feɗe hadaya ta ƙonawar, yă yayyanka shi gunduwa-gunduwa. |
2754 | LEV 1:8 | Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su shirya gunduwa-gunduwar haɗe da kan da kuma kitsen a kan itace mai cin wuta wanda yake a kan bagaden. |
2758 | LEV 1:12 | Zai yanka shi gunduwa-gunduwa, firist kuwa zai shirya su haɗe da kan, da kuma kitsen a kan itace mai cin wutar da yake a kan bagade. |
2871 | LEV 6:14 | A shirya shi da mai a kwanon tuya, a kawo shi kwaɓaɓɓe sosai, a miƙa shi hadaya ta gari dunƙule-dunƙule don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. |
2938 | LEV 8:20 | Ya yanka ragon gunduwa-gunduwa ya ƙone kan, ya kuma ƙone gunduwa-gunduwan da kitsen. |
2967 | LEV 9:13 | Suka miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa-gunduwa, haɗe da kan, ya kuwa ƙone su a bisa bagaden. |
3072 | LEV 13:19 | kuma a inda ƙurjin yake, wani farin kumburi ko tabo ja-ja, fari-fari ya bayyana, dole yă gabatar da kansa ga firist. |
3077 | LEV 13:24 | “Sa’ad da wani yana da ƙuna a fatar jikinsa, wurin kuwa ya yi ja-ja, ko fari-fari, ko kuwa farin tabo ya bayyana a sabon miki na ƙunan, |
3092 | LEV 13:39 | firist ya bincika su, in kuma wuraren toka-toka ne, to, ƙurji marar lahani ne ya faso a fatar jikin; wannan mutum tsarkakakke. |
3095 | LEV 13:42 | Amma in yana da miki ja-ja da ya yi fari a sanƙonsa ko a goshinsa, cuta mai yaɗuwa ce take fasuwa a kai ko a goshin. |
3096 | LEV 13:43 | Sai firist ya bincike shi, in kuma kumburarren miki a kansa ko goshinsa ja-ja da fari-fari kamar cutar fatar jiki mai yaɗuwa ne, |
3102 | LEV 13:49 | in kuma cutar a cikin rigar, ko fatar, ko kayan saƙan kore-kore ne, ko ja-ja, to, cutar fatar jiki da ake samu a riguna ce mai yaɗuwa, kuma dole a nuna wa firist. |
3149 | LEV 14:37 | Zai bincike cutar fatar jiki da take a riga a bangaye, in kuma yana da tabon kore-kore ko ja-ja da suka bayyana da suka yi zurfi fiye da saman bangon, |
3309 | LEV 19:27 | “ ‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku. |
3310 | LEV 19:28 | “ ‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji. |
3356 | LEV 21:10 | “ ‘Babban firist, wanda yake ɗaya cikin ’yan’uwansa wanda aka shafe da mai a kansa, wanda kuma aka naɗa don yă sa rigunan firistoci, kada yă bar gashin kansa buzu-buzu, ko ya kyakketa rigunansa. |
3421 | LEV 23:18 | Tare da wannan, ku miƙa ’yan raguna bakwai, kowanne bana ɗaya-ɗaya marar lahani, bijimi da kuma raguna biyu. Za su zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, tare da hadayunsu na hatsi, da hadayunsu na sha, hadaya da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. |
3422 | LEV 23:19 | Sa’an nan ku miƙa bunsuru ɗaya na hadaya don zunubi, da ’yan raguna biyu, kowanne bana ɗaya-ɗaya, don hadaya ta salama. |
3623 | NUM 1:18 | suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye, |
3625 | NUM 1:20 | Daga zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. |
3627 | NUM 1:22 | Daga zuriyar Simeyon. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. |
3629 | NUM 1:24 | Daga zuriyar Gad. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. |