2 | GEN 1:2 | To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan. |
11 | GEN 1:11 | Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. |
12 | GEN 1:12 | Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. |
26 | GEN 1:26 | Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.” |
29 | GEN 1:29 | Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. |
35 | GEN 2:4 | Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su. Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, |
37 | GEN 2:6 | amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa. |
38 | GEN 2:7 | Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki. |
47 | GEN 2:16 | Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, |
53 | GEN 2:22 | Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin. |
54 | GEN 2:23 | Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.” |
57 | GEN 3:1 | To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?” |
58 | GEN 3:2 | Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, |
59 | GEN 3:3 | amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ” |
61 | GEN 3:5 | Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.” |
62 | GEN 3:6 | Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci. |
63 | GEN 3:7 | Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura. |
68 | GEN 3:12 | Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.” |
70 | GEN 3:14 | Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka. |
72 | GEN 3:16 | Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.” |
73 | GEN 3:17 | Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka. |
76 | GEN 3:20 | Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka. |
77 | GEN 3:21 | Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura. |
81 | GEN 4:1 | Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.” |
82 | GEN 4:2 | Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. |
84 | GEN 4:4 | Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, |
88 | GEN 4:8 | To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe. |
89 | GEN 4:9 | Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?” |
90 | GEN 4:10 | Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa. |
91 | GEN 4:11 | Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka. |
95 | GEN 4:15 | Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi. |
101 | GEN 4:21 | Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa. |
102 | GEN 4:22 | Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama. |
104 | GEN 4:24 | Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.” |
107 | GEN 5:1 | Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah. |
108 | GEN 5:2 | Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.” |
109 | GEN 5:3 | Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set. |
110 | GEN 5:4 | Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
111 | GEN 5:5 | Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu. |
112 | GEN 5:6 | Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh. |
113 | GEN 5:7 | Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
114 | GEN 5:8 | Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu. |
115 | GEN 5:9 | Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan. |
116 | GEN 5:10 | Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
117 | GEN 5:11 | Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu. |
118 | GEN 5:12 | Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel. |
119 | GEN 5:13 | Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata |
120 | GEN 5:14 | Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu. |
121 | GEN 5:15 | Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared. |
122 | GEN 5:16 | Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata |
123 | GEN 5:17 | Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu. |
124 | GEN 5:18 | Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok. |
125 | GEN 5:19 | Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
126 | GEN 5:20 | Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu. |
127 | GEN 5:21 | Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela. |
128 | GEN 5:22 | Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
130 | GEN 5:24 | Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi. |
131 | GEN 5:25 | Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek. |
132 | GEN 5:26 | Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
133 | GEN 5:27 | Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu. |
134 | GEN 5:28 | Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa. |
135 | GEN 5:29 | Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.” |
136 | GEN 5:30 | Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata. |
137 | GEN 5:31 | Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu. |
139 | GEN 6:1 | Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ’ya’ya mata, |
140 | GEN 6:2 | sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. |
141 | GEN 6:3 | Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.” |
142 | GEN 6:4 | Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara. |
148 | GEN 6:10 | Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet. |
156 | GEN 6:18 | Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai. |
161 | GEN 7:1 | Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani. |
164 | GEN 7:4 | Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.” |
166 | GEN 7:6 | Nuhu yana da shekaru 106 ne sa’ad da aka yi ambaliya ruwa a duniya. |
167 | GEN 7:7 | Nuhu da matarsa da ’ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya. |
172 | GEN 7:12 | Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in. |
173 | GEN 7:13 | A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi. |
176 | GEN 7:16 | Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya. |
177 | GEN 7:17 | Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya. |
190 | GEN 8:6 | Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, |
195 | GEN 8:11 | Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya. |
199 | GEN 8:15 | Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, |
200 | GEN 8:16 | “Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu. |
202 | GEN 8:18 | Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa, |
205 | GEN 8:21 | Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba. |
207 | GEN 9:1 | Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya. |
211 | GEN 9:5 | Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa. |
214 | GEN 9:8 | Sai Allah ya ce wa Nuhu da ’ya’yansa, |
220 | GEN 9:14 | Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan, |
222 | GEN 9:16 | Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.” |
224 | GEN 9:18 | ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.) |
225 | GEN 9:19 | Waɗannan su ne ’ya’yan Nuhu maza uku, daga gare su ne kuma duniya za tă cika da mutane. |
227 | GEN 9:21 | Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa. |
228 | GEN 9:22 | Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje. |
229 | GEN 9:23 | Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu. |
230 | GEN 9:24 | Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi, |
231 | GEN 9:25 | sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.” |
232 | GEN 9:26 | Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem. |
233 | GEN 9:27 | Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet; bari Yafet yă zauna a tentunan Shem, bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.” |
235 | GEN 9:29 | Gaba ɗaya dai, Nuhu ya yi shekara 950, sa’an nan ya mutu. |
236 | GEN 10:1 | Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar. |