Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   A    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

1  GEN 1:1  A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa.
2  GEN 1:2  To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
3  GEN 1:3  Sai Allah ya ce, “Bari haske kasance,” sai kuwa ga haske.
4  GEN 1:4  Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu.
5  GEN 1:5  Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.
6  GEN 1:6  Allah ya ce, “Bari sarari kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.”
7  GEN 1:7  Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙaashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance.
8  GEN 1:8  Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.
9  GEN 1:9  Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙaashin sama tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa bayyana.” Haka kuwa ya kasance.
10  GEN 1:10  Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
11  GEN 1:11  Saan nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.
12  GEN 1:12  Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau.
14  GEN 1:14  Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru,
16  GEN 1:16  Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken mallaki yini, ƙaramin kuma mallaki dare. Ya kuma yi taurari.
17  GEN 1:17  Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya,
18  GEN 1:18  su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
20  GEN 1:20  Allah ya ce, “Bari ruwa cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.”
21  GEN 1:21  Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
22  GEN 1:22  Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.”
24  GEN 1:24  Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance.
25  GEN 1:25  Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
26  GEN 1:26  Saan nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”
27  GEN 1:27  Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su.
28  GEN 1:28  Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”
29  GEN 1:29  Saan nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku.
31  GEN 1:31  Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.
33  GEN 2:2  Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa.
34  GEN 2:3  Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
35  GEN 2:4  Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya saad da aka halicce su. Saad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai,
36  GEN 2:5  babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar,
38  GEN 2:7  Saan nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
39  GEN 2:8  To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi.
40  GEN 2:9  Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.
41  GEN 2:10  Akwai wani kogi mai ba da ruwa ga lambun wanda ya gangaro daga Eden, daga nan ya rarrabu, ya zama koguna huɗu.
45  GEN 2:14  Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites.
46  GEN 2:15  Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.
47  GEN 2:16  Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun,
49  GEN 2:18  Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
50  GEN 2:19  To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan.
51  GEN 2:20  Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye. Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba.
52  GEN 2:21  Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙaarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama.
53  GEN 2:22  Saan nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙaarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
57  GEN 3:1  To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
59  GEN 3:3  amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”
61  GEN 3:5  Gama Allah ya san cewa saad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”
64  GEN 3:8  Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.
65  GEN 3:9  Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
69  GEN 3:13  Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
70  GEN 3:14  Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na laanta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.
73  GEN 3:17  Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a laanta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
77  GEN 3:21  Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura.
78  GEN 3:22  Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda miƙa hannunsa ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.”
79  GEN 3:23  Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi.
81  GEN 4:1  Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.”
83  GEN 4:3  Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji.
84  GEN 4:4  Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo,
87  GEN 4:7  Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.”
95  GEN 4:15  Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Saan nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada kashe shi.
97  GEN 4:17  Kayinu ya kwana da matarsa, ta kuwa yi ciki, ta haifi Enok. A lokacin Kayinu yana gina birni, sai ya sa wa birnin sunan ɗansa Enok.
98  GEN 4:18  Aka haifa wa Enok Irad, Irad kuma ya haifi Mehujayel, Mehujayel kuma ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifin Lamek.
99  GEN 4:19  Lamek ya auri mata biyu, ana ce da ɗaya Ada, ɗayan kuma Zilla.
100  GEN 4:20  Ada ta haifi Yabal, shi ne mahaifi waɗanda suke zama a tentuna, suna kuma kiwon dabbobi.
103  GEN 4:23  Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla, “Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata. Na kashe wani saboda ya yi mini rauni, na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo.
105  GEN 4:25  Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce,Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.”
106  GEN 4:26  Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh. A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji.
107  GEN 5:1  Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Saad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.
109  GEN 5:3  Saad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.
110  GEN 5:4  Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
111  GEN 5:5  Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, saan nan ya mutu.
128  GEN 5:22  Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
130  GEN 5:24  Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, saan nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
140  GEN 6:2  sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da banshaawa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.
142  GEN 6:4  Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a saad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.
146  GEN 6:8  Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
147  GEN 6:9  Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.
149  GEN 6:11  Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.
150  GEN 6:12  Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu.
151  GEN 6:13  Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya.
156  GEN 6:18  Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai.
160  GEN 6:22  Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi.
169  GEN 7:9  namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu.
171  GEN 7:11  A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.
173  GEN 7:13  A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi.
176  GEN 7:16  Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Saan nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya.
183  GEN 7:23  Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.
185  GEN 8:1  Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye.
186  GEN 8:2  Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari.
187  GEN 8:3  Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu.
188  GEN 8:4  A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat.
189  GEN 8:5  Ruwan ya ci gaba da janyewa har watan goma. A rana ta fari ga watan goma kuwa ƙwanƙolin duwatsun suka bayyana.