Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   E    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

39  GEN 2:8  To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi.
41  GEN 2:10  Akwai wani kogi mai ba da ruwa ga lambun wanda ya gangaro daga Eden, daga nan ya rarrabu, ya zama koguna huɗu.
46  GEN 2:15  Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.
79  GEN 3:23  Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi.
80  GEN 3:24  Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.
96  GEN 4:16  Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden.
97  GEN 4:17  Kayinu ya kwana da matarsa, ta kuwa yi ciki, ta haifi Enok. A lokacin Kayinu yana gina birni, sai ya sa wa birnin sunan ɗansa Enok.
98  GEN 4:18  Aka haifa wa Enok Irad, Irad kuma ya haifi Mehujayel, Mehujayel kuma ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifin Lamek.
106  GEN 4:26  Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh. A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji.
112  GEN 5:6  Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh.
113  GEN 5:7  Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
115  GEN 5:9  Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan.
116  GEN 5:10  Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
117  GEN 5:11  Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
124  GEN 5:18  Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok.
125  GEN 5:19  Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
127  GEN 5:21  Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela.
128  GEN 5:22  Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
129  GEN 5:23  Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365.
130  GEN 5:24  Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
239  GEN 10:4  ’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
245  GEN 10:10  Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
256  GEN 10:21  Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
257  GEN 10:22  ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
259  GEN 10:24  Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
260  GEN 10:25  Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.
281  GEN 11:14  Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber.
282  GEN 11:15  Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
283  GEN 11:16  Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg.
284  GEN 11:17  Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
338  GEN 14:1  A zamanin Amrafel sarkin Shinar, shi da Ariyok sarkin Ellasar, Kedorlayomer sarkin Elam, da kuma Tidal sarkin Goyim
342  GEN 14:5  A shekara ta goma sha huɗu, Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi suka tafi suka cinye Refahiyawa a Ashterot Karnayim, Zuziyawa a Ham, Emawa a Shabe Kiriyatayim,
343  GEN 14:6  da Horiyawa a ƙasar tudun Seyir har zuwa El Faran kusa da hamada.
344  GEN 14:7  Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar.
346  GEN 14:9  gāba da Kedorlayomer sarkin Elam, Tidal sarkin Goyim, Amrafel sarkin Shinar da Ariyok sarkin Ellasar; sarakuna huɗu gāba da biyar.
350  GEN 14:13  Sai wani wanda ya tsira, ya zo ya faɗa wa Abram mutumin Ibraniyawa. Abram kuwa yana zama kusa da manyan itatuwan Mamre, Mamre mutumin Amoriyawa ne ɗan’uwan Eshkol da Aner, su kuwa abokan Abram ne.
361  GEN 14:24  Ba zan karɓi kome ba, sai dai abin da mutanena suka ci da kuma rabon mutanen da suka tafi tare da ni, ga Aner, Eshkol, da Mamre. Bari su ɗauki rabonsu.”
363  GEN 15:2  Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?”
580  GEN 23:8  Ya ce musu, “In kuna so in binne mataccena, sai ku ji ni, ku roƙi Efron ɗan Zohar a madadina
582  GEN 23:10  Efron mutumin Hitti yana zaune a cikin mutanensa, sai ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birni.
585  GEN 23:13  ya ce wa Efron a kunnuwansu, “Ka ji, in ka yarda. Zan biya farashin filin. Ka karɓa daga gare ni don in iya binne mataccena a can.”
586  GEN 23:14  Efron ya ce wa Ibrahim,
588  GEN 23:16  Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin.
589  GEN 23:17  Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka
663  GEN 25:4  ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.
668  GEN 25:9  ’Ya’yansa maza kuwa Ishaku da Ishmayel suka binne shi cikin kogon Makfela, kusa da Mamre, a cikin filin Efron ɗan Zohar mutumin Hitti,
689  GEN 25:30  Ya ce wa Yaƙub, “Ina roƙonka, ka ɗan ɗiba mini faten nan! Ina fama da yunwa!” (Shi ya sa aka kira shi Edom.)
713  GEN 26:20  Amma makiyayan Gerar suka yi faɗa da na Ishaku suka ce, “Ruwan namu ne!” Saboda haka Ishaku ya ba wa rijiyar suna Esek, domin sun yi faɗa da shi.
727  GEN 26:34  Sa’ad da Yaƙub ya kai shekaru arba’in da haihuwa, sai ya auri Yudit ’yar Beyeri mutumin Hitti, da kuma Basemat ’yar Elon mutumin Hitti.
932  GEN 32:4  Sai Yaƙub ya aiki manzanni su sha gabansa zuwa wurin ɗan’uwansa Isuwa a ƙasar Seyir, a ƙauyen Edom.
981  GEN 33:20  A can ya kafa bagade ya kuma kira shi El Elohe Isra’ila.
1019  GEN 35:7  A can ya gina bagade, ya kuma kira wurin El Betel, gama a can ne Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake gudu daga ɗan’uwansa.
1028  GEN 35:16  Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai.
1031  GEN 35:19  Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem).
1033  GEN 35:21  Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder.
1042  GEN 36:1  Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).
1043  GEN 36:2  Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye
1045  GEN 36:4  Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel.
1049  GEN 36:8  Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.
1050  GEN 36:9  Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.
1051  GEN 36:10  Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isuwa maza, Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
1052  GEN 36:11  ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.
1053  GEN 36:12  Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.
1056  GEN 36:15  Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa, ’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,
1057  GEN 36:16  Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.
1058  GEN 36:17  ’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
1060  GEN 36:19  Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.
1062  GEN 36:21  Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
1064  GEN 36:23  ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
1067  GEN 36:26  ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
1068  GEN 36:27  ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan.
1071  GEN 36:30  Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.
1072  GEN 36:31  Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,
1073  GEN 36:32  Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.
1082  GEN 36:41  Oholibama, Ela, Finon.
1084  GEN 36:43  Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.
1123  GEN 38:3  ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa, wanda aka kira Er.
1126  GEN 38:6  Sai Yahuda ya auro wa Er mata, ɗansa na fari, sunanta Tamar.
1127  GEN 38:7  Amma Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a fuskar Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.
1134  GEN 38:14  sai ta tuɓe rigunan gwaurancinta ta rufe kanta da lulluɓi don ta ɓad da kamanninta, sa’an nan ta je ta zauna a ƙofar shigar Enayim, wadda take a hanyar zuwa Timna. Gama ta lura cewa ko da yake Shela yanzu ya yi girma, ba a ba da ita gare shi ta zama matarsa ba.
1141  GEN 38:21  Ya tambayi mutanen da suke zama a can ya ce, “Ina karuwar haikalin da take a bakin hanya a Enayim?” Sai suka ce, “Ba a taɓa kasance da karuwar haikali a nan ba.”
1248  GEN 41:52  Ya ba wa ɗansa na biyu suna Efraim ya ce, “Gama Allah ya wadata ni cikin wahalata.”
1399  GEN 46:12  ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.
1401  GEN 46:14  ’Ya’yan Zebulun maza su ne, Sered, Elon da Yaleyel.
1403  GEN 46:16  ’Ya’yan Gad maza su ne, Zafon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi da Areli.
1407  GEN 46:20  A Masar, Asenat ’yar Fotifera, firist na On ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf.
1408  GEN 46:21  ’Ya’yan Benyamin maza su ne, Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard.
1453  GEN 48:1  Bayan wani lokaci aka faɗa wa Yusuf, “Mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ’ya’yansa maza biyu, Manasse da Efraim suka tafi tare da shi.
1457  GEN 48:5  “To, yanzu, ’ya’ya mazanka biyu da aka haifa maka a Masar kafin in zo a nan za su zama nawa; Efraim da Manasse za su zama nawa, kamar yadda Ruben da Simeyon suke nawa.
1459  GEN 48:7  Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem).
1465  GEN 48:13  Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi.
1466  GEN 48:14  Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.