Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   H    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

7  GEN 1:7  Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance.
9  GEN 1:9  Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance.
11  GEN 1:11  Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.
15  GEN 1:15  bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance.
24  GEN 1:24  Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance.
30  GEN 1:30  Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.
42  GEN 2:11  Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.
76  GEN 3:20  Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.
77  GEN 3:21  Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura.
81  GEN 4:1  Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.”
82  GEN 4:2  Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.
84  GEN 4:4  Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo,
88  GEN 4:8  To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.
89  GEN 4:9  Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”
93  GEN 4:13  Kayinu ya ce wa Ubangiji,Horon nan ya sha ƙarfina.
105  GEN 4:25  Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.”
138  GEN 5:32  Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.
148  GEN 6:10  Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
173  GEN 7:13  A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi.
191  GEN 8:7  ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya.
224  GEN 9:18  ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.)
228  GEN 9:22  Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje.
236  GEN 10:1  Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
241  GEN 10:6  ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
242  GEN 10:7  ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan.
250  GEN 10:15  Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,
252  GEN 10:17  Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
253  GEN 10:18  Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu
255  GEN 10:20  Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
258  GEN 10:23  ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash.
261  GEN 10:26  Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,
262  GEN 10:27  Hadoram, Uzal, Dikla,
264  GEN 10:29  Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
293  GEN 11:26  Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.
294  GEN 11:27  Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.
295  GEN 11:28  Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa.
296  GEN 11:29  Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska.
298  GEN 11:31  Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.
299  GEN 11:32  Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.
303  GEN 12:4  Saboda haka Abram ya tashi yadda Ubangiji ya faɗa masa; Lot ma ya tafi tare da shi. Abram yana da shekaru 75, sa’ad da ya tashi daga Haran.
304  GEN 12:5  Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana.
330  GEN 13:11  Saboda haka sai Lot ya zaɓar wa kansa dukan kwarin Urdun, ya tashi ya nufi wajen gabas. Haka fa suka rabu da juna.
337  GEN 13:18  Saboda haka Abram ya cire tentunansa, ya zo ya zauna kusa da manyan itatuwan Mamre a Hebron, inda ya gina bagade ga Ubangiji.
342  GEN 14:5  A shekara ta goma sha huɗu, Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi suka tafi suka cinye Refahiyawa a Ashterot Karnayim, Zuziyawa a Ham, Emawa a Shabe Kiriyatayim,
343  GEN 14:6  da Horiyawa a ƙasar tudun Seyir har zuwa El Faran kusa da hamada.
344  GEN 14:7  Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar.
352  GEN 14:15  Da dad dare, Abram ya rarraba mutanensa don su fāɗa wa sarakunan nan, ya ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewa da Damaskus.
366  GEN 15:5  Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa,Haka zuriyarka za tă zama.”
381  GEN 15:20  Hittiyawa, Ferizziyawa, Refahiyawa,
383  GEN 16:1  To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar,
385  GEN 16:3  Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa.
386  GEN 16:4  Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki. Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta.
388  GEN 16:6  Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta.
389  GEN 16:7  Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur.
390  GEN 16:8  Ya kuma ce mata,Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”
394  GEN 16:12  Zai zama mutum mai halin jakin jeji. Hannunsa zai yi gāba da kowa, hannun kowa kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zama gāba ga dukan ’yan’uwansa.”
397  GEN 16:15  Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa.
398  GEN 16:16  Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel.
438  GEN 18:13  Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce,Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’
483  GEN 19:25  Haka ya hallakar da waɗannan birane da kuma kwarinsu gaba ɗaya, haɗe da dukan waɗanda suke zama a biranen, da kuma dukan shuke-shuke da suke cikin ƙasar.
523  GEN 21:9  Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori,
528  GEN 21:14  Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.
531  GEN 21:17  Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can.
570  GEN 22:22  Kesed, Hazo, Fildash; Yidlaf, da kuma Betuwel.”
574  GEN 23:2  Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.
575  GEN 23:3  Sai Ibrahim ya tashi daga gefen matarsa da ta mutu, ya yi magana da Hittiyawa. Ya ce,
577  GEN 23:5  Hittiyawa suka ce wa Ibrahim,
579  GEN 23:7  Sai Ibrahim ya tashi ya rusuna a gaban mutanen ƙasar, wato, Hittiyawan.
582  GEN 23:10  Efron mutumin Hitti yana zaune a cikin mutanensa, sai ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birni.
588  GEN 23:16  Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin.
590  GEN 23:18  ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin.
591  GEN 23:19  Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana.
592  GEN 23:20  Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta.
663  GEN 25:4  ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.
668  GEN 25:9  ’Ya’yansa maza kuwa Ishaku da Ishmayel suka binne shi cikin kogon Makfela, kusa da Mamre, a cikin filin Efron ɗan Zohar mutumin Hitti,
669  GEN 25:10  filin da Ibrahim ya saya daga Hittiyawa. A nan aka binne Ibrahim tare da matarsa Saratu.
671  GEN 25:12  Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.
674  GEN 25:15  Hadad, Tema, Yetur, Nafish da Kedema.
677  GEN 25:18  Zuriyarsa sun zauna tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake kusa da gabashin iyakar Masar wajen Asshur. Sun yi zaman rikici da dukan sauran ’yan’uwansu.
727  GEN 26:34  Sa’ad da Yaƙub ya kai shekaru arba’in da haihuwa, sai ya auri Yudit ’yar Beyeri mutumin Hitti, da kuma Basemat ’yar Elon mutumin Hitti.
771  GEN 27:43  To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran.
774  GEN 27:46  Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.”
784  GEN 28:10  Yaƙub ya bar Beyersheba ya kama hanyar Haran.
800  GEN 29:4  Yaƙub ya tambayi makiyayan ya ce, “’Yan’uwa, ina kuka fito?” Suka amsa, “Mu daga Haran ne.”
824  GEN 29:28  Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa.
830  GEN 29:34  Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa ’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi.
915  GEN 31:41  Haka ya kasance shekaru ashirin da na yi a gidanka. Na yi maka aiki shekaru goma sha huɗu domin ’ya’yanka mata biyu, na kuma yi shekaru shida domin garkunanka, ka kuma canja albashina sau goma.
980  GEN 33:19  Ya sayi fili daga ’ya’yan Hamor maza, mahaifin Shekem inda ya kafa tentinsa, a bakin azurfa ɗari.
983  GEN 34:2  Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.
985  GEN 34:4  Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.”
987  GEN 34:6  Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub.
989  GEN 34:8  Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan ’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura.
994  GEN 34:13  Domin an ɓata ’yar’uwansu Dina, sai ’ya’yan Yaƙub maza suka amsa a ha’ince yayinda suke wa Shekem da mahaifinsa Hamor magana.
999  GEN 34:18  Sharuɗansu sun gamshi Hamor da ɗansa, Shekem.
1001  GEN 34:20  Saboda haka Hamor da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu don su yi magana da mutanen garinsu.
1005  GEN 34:24  Dukan mazan da suka fito ƙofar birnin suka yarda da Hamor da kuma ɗansa Shekem, aka kuwa yi wa kowane namiji a birnin kaciya.
1007  GEN 34:26  Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dina daga gidan Shekem suka tafi.