65 | GEN 3:9 | Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?” |
89 | GEN 4:9 | Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?” |
92 | GEN 4:12 | In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.” |
98 | GEN 4:18 | Aka haifa wa Enok Irad, Irad kuma ya haifi Mehujayel, Mehujayel kuma ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifin Lamek. |
104 | GEN 4:24 | Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.” |
246 | GEN 10:11 | Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala |
296 | GEN 11:29 | Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska. |
318 | GEN 12:19 | Don me ka ruɗe ni cewa, ‘Ita ’yar’uwata ce,’ har na ɗauke ta tă zama matata? To, ga matarka. Ɗauke ta ka tafi.” |
328 | GEN 13:9 | Ba ga dukan ƙasar tana gabanka ba? Bari mu rabu. In ka yi hagu sai ni in yi dama. In ka yi dama, sai ni in yi hagu.” |
350 | GEN 14:13 | Sai wani wanda ya tsira, ya zo ya faɗa wa Abram mutumin Ibraniyawa. Abram kuwa yana zama kusa da manyan itatuwan Mamre, Mamre mutumin Amoriyawa ne ɗan’uwan Eshkol da Aner, su kuwa abokan Abram ne. |
363 | GEN 15:2 | Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?” |
369 | GEN 15:8 | Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?” |
390 | GEN 16:8 | Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.” |
393 | GEN 16:11 | Mala’ikan Ubangiji ya kuma ce mata, “Ga shi kina da ciki za ki kuwa haifi ɗa. Za ki ba shi suna Ishmayel, gama Ubangiji ya ga wahalarki. |
397 | GEN 16:15 | Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa. |
398 | GEN 16:16 | Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel. |
403 | GEN 17:5 | Ba za a ƙara kiranka Abram ba; sunanka zai zama Ibrahim, gama na mai da kai uban al’ummai masu yawa. |
407 | GEN 17:9 | Sa’an nan Allah ya ce wa Ibrahim. “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, kai da zuriyarka bayanka, har tsararraki masu zuwa. |
413 | GEN 17:15 | Allah ya kuma ce wa Ibrahim, “Game da Saira matarka kuwa, ba za ka ƙara kiranta Saira ba, sunanta zai zama Saratu. |
415 | GEN 17:17 | Ibrahim ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, ya yi dariya, ya ce wa kansa, “Za a haifi ɗa wa mutum mai shekaru ɗari? Saratu za tă haifi ɗa tana da shekaru tasa’in?” |
416 | GEN 17:18 | Ibrahim ya kuma ce wa Allah, “Me zai hana a dai bar Ishmayel kawai yă gāji alkawarin nan da ka yi mini.” |
417 | GEN 17:19 | Sai Allah ya ce, “Duk da haka dai, matarka Saratu za tă haifi maka ɗa; za ka kuma kira shi Ishaku. A kansa zan tabbatar da madawwamin alkawarina, da kuma ga zuriyarsa da za su zo bayansa. |
418 | GEN 17:20 | Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma! |
419 | GEN 17:21 | Amma dai zan kafa alkawarina da Ishaku wanda Saratu za tă haifa maka war haka shekara mai zuwa.” |
420 | GEN 17:22 | Da ya gama magana da Ibrahim, sai Allah ya tashi daga gare shi. |
421 | GEN 17:23 | A wannan rana, Ibrahim ya ɗauki ɗansa Ishmayel da dukan waɗanda aka haifa cikin gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji a cikin gidansa kaciya kamar yadda Allah ya faɗa masa. |
422 | GEN 17:24 | Ibrahim yana da shekara tasa’in da tara sa’ad da aka yi masa kaciya, |
423 | GEN 17:25 | Ishmayel ɗansa kuma yana da shekara goma sha uku. |
424 | GEN 17:26 | Aka yi wa Ibrahim da ɗansa Ishmayel kaciya a rana ɗaya. |
425 | GEN 17:27 | Aka yi wa kowane namiji a gidan Ibrahim kaciya, da waɗanda aka haifa a gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙo. |
426 | GEN 18:1 | Ubangiji ya bayyana ga Ibrahim kusa da manyan itatuwan Mamre yayinda yake zaune a mashigin tentinsa da tsakar rana. |
427 | GEN 18:2 | Da Ibrahim ya ɗaga ido, sai ya ga mutum uku suna tsaye kusa da shi. Sa’ad da ya gan su, sai ya tashi nan da nan daga mashigin tentinsa, ya tarye su, ya rusuna har ƙasa. |
431 | GEN 18:6 | Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.” |
432 | GEN 18:7 | Sa’an nan Ibrahim ya yi gudu zuwa garkensa, ya zaɓi ɗan maraƙi ya ba wa bawansa, bawansa kuma ya yi sauri ya gyara shi. |
433 | GEN 18:8 | Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su. |
434 | GEN 18:9 | Sai suka ce masa, “Ina Saratu matarka?” Ibrahim ya ce, “Tana can cikin tenti.” |
436 | GEN 18:11 | Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa. |
438 | GEN 18:13 | Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’ |
441 | GEN 18:16 | Sai mutanen suka tashi suka nufi Sodom, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya, ya yi bankwana da su. |
442 | GEN 18:17 | Sai Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin yi? |
443 | GEN 18:18 | Lalle Ibrahim zai zama al’umma mai girma da kuma mai iko, kuma ta wurinsa dukan al’umman duniya za su sami albarka. |
444 | GEN 18:19 | Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.” |
447 | GEN 18:22 | Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji. |
448 | GEN 18:23 | Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta? |
451 | GEN 18:26 | Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.” |
452 | GEN 18:27 | Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka, |
453 | GEN 18:28 | in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?” Ya ce, “In na sami mutum arba’in da biyar a wurin, ba zan hallaka shi ba.” |
454 | GEN 18:29 | Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda mutum arba’in ɗin, ba zan aikata ba.” |
456 | GEN 18:31 | Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.” |
457 | GEN 18:32 | Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?” Ubangiji ya ce, “Saboda goma nan, ba zan hallaka shi ba.” |
458 | GEN 18:33 | Sa’ad da Ubangiji ya gama magana da Ibrahim, ya tafi, Ibrahim kuma ya koma gida. |
463 | GEN 19:5 | Suka kira Lot, suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka a daren nan? Fito mana da su waje domin mu kwana da su.” |
485 | GEN 19:27 | Da sassafe kashegari, Ibrahim ya tashi ya koma wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji. |
487 | GEN 19:29 | Saboda haka sa’ad da Allah ya hallaka waɗannan biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya kuma fitar da Lot daga masifar da ta hallaka biranen da Lot ya zauna. |
497 | GEN 20:1 | Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi wajajen Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. Ya zauna a Gerar na ɗan lokaci, |
498 | GEN 20:2 | a can ne Ibrahim ya ce game da matarsa Saratu, “Ita ’yar’uwata ce.” Sai Abimelek sarkin Gerar ya aiko a kawo masa Saratu. |
499 | GEN 20:3 | Amma wata rana da dad dare Allah ya zo wa Abimelek a cikin mafarki ya ce masa, “Kai da matacce ɗaya kuke, saboda matar da ka ɗauka. Ita matar aure ce.” |
501 | GEN 20:5 | Ba shi ne ya ce mini, ‘Ita ’yar’uwata ba ce,’ ita ma ba tă ce, ‘Shi ɗan’uwana ba ne’? Na yi haka da kyakkyawan nufi da hannuwa masu tsabta.” |
502 | GEN 20:6 | Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba. |
503 | GEN 20:7 | Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.” |
505 | GEN 20:9 | Sa’an nan Abimelek ya kira Ibrahim ciki ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ta wace hanya ce na yi maka laifi har da ka kawo irin wannan babban laifi a kaina da kuma masarautata? Ka yi mini abubuwan da bai kamata a yi ba.” |
506 | GEN 20:10 | Abimelek ya kuma ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan?” |
507 | GEN 20:11 | Ibrahim ya ce, “Na ce a raina, ‘Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’ |
510 | GEN 20:14 | Sai Abimelek ya kawo awaki da shanu da bayi maza da mata, ya ba wa Ibrahim, ya kuma komar da Saratu matarsa gare shi. |
512 | GEN 20:16 | Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.” |
513 | GEN 20:17 | Sai Ibrahim ya yi addu’a ga Allah, Allah kuma ya warkar da Abimelek, da matarsa da bayinsa mata domin su haihu, |
514 | GEN 20:18 | gama Ubangiji ya rufe kowace mahaifa a gidan Abimelek saboda Saratu, matar Ibrahim. |
516 | GEN 21:2 | Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari. |
517 | GEN 21:3 | Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku. |
518 | GEN 21:4 | Sa’ad da ɗansa Ishaku ya kai kwana takwas da haihuwa, sai Ibrahim ya yi masa kaciya, kamar yadda Allah ya umarce shi. |
519 | GEN 21:5 | Ibrahim yana da shekara ɗari, sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku. |
521 | GEN 21:7 | Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.” |
522 | GEN 21:8 | Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki. |
523 | GEN 21:9 | Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori, |
524 | GEN 21:10 | sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.” |
525 | GEN 21:11 | Al’amarin ya ɓata wa Ibrahim rai sosai domin zancen ya shafi ɗansa. |
526 | GEN 21:12 | Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka. |
528 | GEN 21:14 | Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba. |
536 | GEN 21:22 | A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi. |
538 | GEN 21:24 | Ibrahim ya ce, “Na rantse.” |
539 | GEN 21:25 | Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace. |
541 | GEN 21:27 | Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya. |
542 | GEN 21:28 | Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke, |
543 | GEN 21:29 | sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?” |
544 | GEN 21:30 | Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.” |
547 | GEN 21:33 | Sai Ibrahim ya shuka itacen tsamiya a Beyersheba, a can kuma ya kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami. |
548 | GEN 21:34 | Ibrahim kuwa ya zauna a ƙasar Filistiyawa na dogon lokaci. |
549 | GEN 22:1 | Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” |