492 | GEN 19:34 | Kashegari, ’yar farin ta ce wa ƙanuwar, “Jiya da dare na kwana da mahaifina. Bari mu sa yă sha ruwan inabi kuma yau da dare, ke ma ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” |
535 | GEN 21:21 | Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar. |
681 | GEN 25:22 | Jariran suka kama kokawa da juna a cikinta, sai ta ce, “Me ya sa wannan yake faruwa da ni?” Saboda haka ta tafi don ta nemi nufin Ubangiji. |
737 | GEN 27:9 | Je garke ka kawo mini awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi wa mahaifinka, kamar yadda dai yake so. |
1098 | GEN 37:14 | Saboda haka Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Jeka ka ga ko kome lafiya yake da ’yan’uwanka da kuma garkunan, ka kawo mini labari.” Sa’an nan ya sallame shi daga Kwarin Hebron. Sa’ad da Yusuf ya kai Shekem, |
1605 | EXO 4:3 | Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi. |
1705 | EXO 7:19 | Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka ɗauki sandanka, ka miƙa hannunka kan ruwan Masar, kan kogunansu da rafuffukansu da kududdufansu da kuma dukan tafkunansu, za su zama jini.’ Jini zai kasance ko’ina a Masar, har ma a cikin abubuwan ajiyar ruwansu da aka yi da itace da kuma dutse.” |
1707 | EXO 7:21 | Kifin da suke cikin Nilu suka mutu, kogin kuwa ya yi wari sosai yadda Masarawa ba su iya shan ruwan ba. Jini ya bazu ko’ina a Masar. |
1779 | EXO 10:1 | Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu, |
1797 | EXO 10:19 | Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar. |
1830 | EXO 12:13 | Jinin zai zama alama a gare ku, a gidajen da kuke; sa’ad da kuwa na ga jinin, zan ƙetare ku. Ba wata annoba mai hallakarwa da za tă taɓa ku yayinda na bugi Masar. |
1886 | EXO 13:18 | Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi. |
2176 | EXO 23:31 | “Zan kafa iyakokinku daga Jan Teku zuwa Bahar Rum, daga hamada kuma zuwa Kogi. Zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kuwa kore su daga gabanku. |
2658 | EXO 38:24 | Jimillar zinariya daga hadaya ta kaɗawar da aka yi amfani da su domin aikin wuri mai tsarki ta kai talenti 29 da shekel 730, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. |
3626 | NUM 1:21 | Jimillar maza daga mutanen Ruben 46,500 ne. |
3628 | NUM 1:23 | Jimillar maza daga mutanen Simeyon 59,300 ne. |
3630 | NUM 1:25 | Jimillar maza daga mutanen Gad 45,650 ne. |
3632 | NUM 1:27 | Jimillar maza daga mutanen Yahuda 74,600 ne. |
3634 | NUM 1:29 | Jimillar maza daga mutanen Issakar 54,400 ne. |
3636 | NUM 1:31 | Jimillar maza daga mutanen Zebulun 57,400 ne. |
3638 | NUM 1:33 | Jimillar maza daga mutanen Efraim 40,500 ne. |
3640 | NUM 1:35 | Jimillar maza daga mutanen Manasse 32,200 ne. |
3642 | NUM 1:37 | Jimillar maza daga mutanen Benyamin 35,400 ne. |
3644 | NUM 1:39 | Jimillar maza daga mutanen Dan 62,700 ne. |
3646 | NUM 1:41 | Jimillar maza daga mutanen Asher 41,500 ne. |
3648 | NUM 1:43 | Jimillar maza daga mutanen Naftali kuwa 53,400 ne. |
3651 | NUM 1:46 | Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550. |
3715 | NUM 3:22 | Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya zuwa gaba da haihuwa su kai 7,500. |
3721 | NUM 3:28 | Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 8,600 ne. Kohatawa ne suke lura da wuri mai tsarki. |
3727 | NUM 3:34 | Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 6,200 ne. |
3732 | NUM 3:39 | Jimillar Lawiyawan da Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga umarnin Ubangiji bisa ga danginsu, haɗe da kowane jariri daga wata ɗaya ko fiye, 22,000 ne. |
3736 | NUM 3:43 | Jimillar ’ya’yan fari maza daga wata ɗaya da kuma fiye, da aka rubuta bisa ga sunayensu, 22,273 ne. |
3781 | NUM 4:37 | Jimillar dukan waɗanda suke na kabilan Kohatawa, waɗanda suka yi hidimar aiki a Tentin Sujada ke nan. Musa da Haruna sun ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji. |
3785 | NUM 4:41 | Jimillar waɗanda suke na kabilar Gershonawa ke nan, waɗanda suka yi hidimar aiki a Tentin Sujada. Musa da Haruna sun ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji. |
3789 | NUM 4:45 | Jimillar waɗanda suke na kabilar Merari ke nan. Musa da Haruna suka ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji. |
3938 | NUM 7:87 | Jimillar dabbobi don hadaya ta ƙonawa, ta kai ƙanana bijimai goma sha biyu, raguna goma sha biyu da ’yan raguna goma sha biyu, dukansu bana ɗaya-ɗaya, tare da hadayarsu ta hatsi. Aka yi amfani da bunsurai goma sha biyu domin hadaya don zunubi. |
3939 | NUM 7:88 | Jimillar dabbobi don hadaya ta salama, ta kai shanu ashirin huɗu, raguna sittin, bunsurai sittin da kuma ’yan raguna sittin, dukansu bana ɗaya-ɗaya. Waɗannan su ne hadayu saboda keɓewar bagade, bayan an shafe shi. |
4134 | NUM 14:25 | Da yake Amalekawa da Kan’aniyawa suna zama a kwarin, gobe sai ka koma baya, ka nufi wajen hamada ta hanyar Jan Teku.” |
4299 | NUM 19:9 | “Mutumin da yake da tsarki, zai tara tokar karsanar, yă sa ta a wurin da yake da tsabta a bayan sansani. Jama’ar Isra’ilawa ne za su adana shi don amfani a ruwan tsabtaccewa; wannan domin tsarkakewa ne daga zunubi. |
4334 | NUM 20:22 | Dukan Jama’ar Isra’ilawa suka tashi daga Kadesh, suka zo Dutsen Hor. |
4345 | NUM 21:4 | Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya; |
4406 | NUM 22:30 | Jakar ta ce wa Bala’am, “Ni ba jakarka ba ce wadda kake hawa kullum, har yă zuwa yau? Na taɓa yin maka haka?” Bala’am ya ce, “A’a.” |
4409 | NUM 22:33 | Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da a ce ba tă kauce ba, lalle da na kashe ka, in kuwa bar ta da rai.” |
4471 | NUM 24:24 | Jiragen ruwa za su zo daga Kittim; za su murƙushe Asshur da Eber, amma su ma za a hallaka su.” |
4772 | NUM 33:10 | Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku. |
4773 | NUM 33:11 | Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin. |
4934 | DEU 1:40 | Amma ku kam, sai ku juya, ku koma cikin hamada ta hanyar Jan Teku.” |
4941 | DEU 2:1 | Sai muka juya muka kama hanya, muka nufi hamada, ta hanyar Jan Teku yadda Ubangiji ya umarce ni. Da daɗewa muka yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun Seyir. |
5085 | DEU 5:30 | “Je, ka faɗa musu su koma tentunansu. |
5214 | DEU 11:4 | ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba. |
5873 | JOS 2:2 | Aka gaya wa sarkin Yeriko cewa, “Ji fa, waɗansu Isra’ilawa sun shigo nan da dare don su leƙi asirin ƙasar.” |
5881 | JOS 2:10 | Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai. |
5935 | JOS 4:23 | Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa. |
6205 | JOS 15:1 | An raba wa kabilar Yahuda gādonsu ta wurin yin ƙuri’a, bisa ga iyalansu, rabon ya kai har zuwa sashen Edom, zuwa Jejin Zin can kurewar kudu. |
6424 | JOS 21:41 | Jimillar birane da wurarensu na kiwon da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama’ar Isra’ila guda arba’in da takwas ne. |
6484 | JOS 24:6 | Lokacin da na fitar da iyayenku daga Masar, suka zo teku, sai Masarawa suka fafare su da kekunan yaƙi da dawakai har zuwa Jan Teku. |
6607 | JDG 4:6 | Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor. |
6615 | JDG 4:14 | Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi. |
6847 | JDG 11:16 | Amma sa’ad da suka bar Masar, Isra’ila ta bi ta hamada zuwa Jan Teku har suka zo Kadesh. |
7161 | RUT 2:10 | Jin haka, sai ta rusuna da fuskata har ƙasa ta ce, “Me ya sa na sami irin wannan tagomashi a idanunka da har ka lura da ni, ni da nake baƙuwa?” |
7287 | 1SA 3:9 | Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’ ” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa. |
7341 | 1SA 6:8 | Ku ɗauki wani akwati ku sa siffofin zinariyan nan a ciki, waɗanda za su zama kyautai na shafen laifi, ku ajiye kusa da Akwati na UBANGIJI. Bayan haka sai ku sa keken shanun da akwatin a hanya, ku bar shi yă tafi. |
7529 | 1SA 14:19 | Yayinda Shawulu yake magana da firist kuwa, harguwa ya yi ta ƙaruwa a sansanin Filistiyawa. Sai Shawulu ya ce wa firist, “Janye hannunka.” |
7657 | 1SA 17:37 | Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.” |
7751 | 1SA 20:19 | Jibi wajajen yamma, ka tafi wurin da ka ɓuya lokacin da wannan matsala ta fara, ka tsaya kusa da dutsen Etsel. |
7753 | 1SA 20:21 | Sa’an nan zan aiki yaro in ce masa, ‘Je ka nemo kibiyoyin.’ In na ce masa, ‘Duba, kibiyoyin suna wannan gefen da kake, kawo su,’ sai ka fito, wato, tabbatacce muddin Ubangiji yana raye, ka tsira, ba wani hatsari. |
7815 | 1SA 23:2 | Sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya ce, “In tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Jeka ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci Keyila.” |
7843 | 1SA 24:2 | Bayan da Shawulu ya komo daga fafaran Filistiyawa, sai aka gaya masa cewa, “Dawuda yana can a Jejin En Gedi.” |
7844 | 1SA 24:3 | Saboda haka Shawulu ya zaɓi mutum dubu uku daga cikin dukan Isra’ila, suka fita neman Dawuda da mutanensa kusa da Duwatsun Awakin Jeji. |
7865 | 1SA 25:1 | Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran. |
7910 | 1SA 26:2 | Sai Shawulu ya tashi ya gangara zuwa Jejin Zif, tare da zaɓaɓɓun mutane dubu uku na Isra’ila. Suka fita neman Dawuda a can. |
8040 | 2SA 1:15 | Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin mutanensa ya ce, “Je ka kashe shi!” Haka kuwa ya buge shi, ya kuwa mutu. |
8050 | 2SA 1:25 | “Jarumawa sun fāɗi a yaƙi! Ga Yonatan matacce a tuddanku. |
8052 | 2SA 1:27 | “Jarumawa sun fāɗi! Makaman yaƙi sun hallaka!” |
8053 | 2SA 2:1 | Bayan ’yan kwanaki, sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In haura zuwa ɗaya daga cikin biranen Yahuda?” Ubangiji ya ce, “Haura.” Dawuda ya ce, “Wanne zan tafi?” Ubangiji ya ce, “Je Hebron.” |
8154 | 2SA 5:19 | saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In tafi in kai wa Filistiya hari? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Je ka, gama tabbatacce zan bashe Filistiyawa a hannunka.” |
8188 | 2SA 7:5 | “Je ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, kai ne za ka gina mini gida in zauna? |
8325 | 2SA 13:5 | Yonadab ya ce, “Je gado ka kwanta kamar ba ka da lafiya. Sa’ad da mahaifinka ya zo ganinka, sai ka ce masa, ‘Ina so ƙanuwata Tamar tă kawo mini wani abu in ci. Bari tă shirya abincin a gabana don in ganta, in kuma ci daga hannunta.’ ” |
8380 | 2SA 14:21 | Sarki ya ce wa Yowab, “To, da kyau, zan yi haka. Je ka, ka dawo da saurayin nan Absalom.” |
8412 | 2SA 15:20 | Jiya-jiya ka zo. Yau kuma in sa ka yi ta yawo tare da mu, ga shi ban ma san inda za ni ba? Koma, ka tafi da ’yan’uwanka. Bari alheri da amincin Ubangiji su kasance tare da kai.” |
8431 | 2SA 16:2 | Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?” Ziba ya ce, “Jakuna domin iyalin gidan sarki su hau ne, burodi da ’ya’yan itace domin mutane su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suka gaji a hamada.” |
8450 | 2SA 16:21 | Ahitofel ya ce wa Absalom, “Je ka kwana da ƙwarƙwaran mahaifinka waɗanda ya bari su lura da fada. Ta haka dukan Isra’ila za su ji cewa ka mai da kanka abin wari a hancin mahaifinka, dukan hannuwan waɗanda suke tare da kai kuwa za su sami ƙarfi.” |
8502 | 2SA 18:21 | Sai Yowab ya ce wa wani mutumin Kush, “Je ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Mutumin Kush ɗin kuwa ya rusuna wa Yowab, sai ya ruga a guje. |
8696 | 2SA 24:1 | Fushin Ubangiji ya sāke ƙuna a kan Isra’ila, sai ya zuga Dawuda, yana cewa, “Je ka ƙidaya Isra’ila da Yahuda.” |
8707 | 2SA 24:12 | “Je ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, ina ba ka zaɓi uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata maka shi.’ ” |
8802 | 1KI 2:29 | Aka faɗa wa Sarki Solomon cewa Yowab ya gudu zuwa tentin Ubangiji, yana kuma kusa da bagade. Sai Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada ya ce, “Je ka kashe shi!” |
9080 | 1KI 9:26 | Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku. |
9093 | 1KI 10:11 | (Jiragen ruwan Hiram suka kawo zinariya daga Ofir. Daga can kuma suka kawo kaya masu yawa na katakon almug, da kuma duwatsu masu daraja. |
9228 | 1KI 14:7 | Je ki faɗa wa Yerobowam cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na tā da kai daga cikin mutane, na mai da kai shugaba a bisa mutanena Isra’ila. |
9329 | 1KI 17:9 | “Je ka, nan take, zuwa Zarefat na Sidon, ka zauna a can. Na umarci wata gwauruwa a can tă ciyar da kai.” |
9388 | 1KI 18:44 | Sau na bakwai, bawan ya ce, “Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku.” Sai Iliya ya ce, “Je ka faɗa wa Ahab, ‘Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama yă tare ka.’ ” |
9517 | 1KI 22:34 | Amma wani ya ja bakansa kawai ya bugi Ahab sarkin Isra’ila a tsakanin sassan kayan yaƙinsa. Sai sarki ya ce wa mahayin keken yaƙinsa, “Juye, ka fitar da ni daga yaƙin. An ji mini rauni.” |
9518 | 1KI 22:35 | Dukan yini aka yi ta yaƙi, aka kuma riƙe sarki a keken yaƙinsa yana fuskanci Arameyawa. Jini daga mikinsa ya yi ta zuba a ƙasan keken yaƙin, a wannan yamma kuwa ya mutu. |
9603 | 2KI 3:23 | Sai suka ce, “Jini ne! Ba shakka sarakunan nan sun yaƙe juna, suka karkashe juna. Ya Mowabawa, mu tafi mu kwashi ganima!” |
9661 | 2KI 5:10 | Sai Elisha ya aika ’yan saƙo su ce masa, “Je, ka nutse sau bakwai a Urdun, fatar jikinka za tă koma daidai, ka kuma tsarkaka.” |
9741 | 2KI 8:10 | Elisha ya amsa ya ce, “Je ka ce masa, ‘Ba shakka za ka warke’; ammaUbangiji ya nuna mini cewa ba shakka zai mutu.” |
9786 | 2KI 9:26 | ‘Jiya na ga jinin Nabot da jinin ’ya’yansa, in ji Ubangiji, kuma ba shakka zan ɗauki fansa a wannan fili, in ji Ubangiji.’ Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar da shi a bisa wannan fegi, bisa ga faɗin Ubangiji. Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar a filin, in ji Ubangiji.” |
10047 | 2KI 18:19 | Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama? |
10703 | 1CH 11:26 | Jarumawan nan su ne, Asahel ɗan’uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem, |
10954 | 1CH 21:15 | Allah kuwa ya aiki mala’ika yă hallaka Urushalima. Amma yayinda mala’ikan yana gab da yin haka, sai Ubangiji ya gani ya kuma yi nadama saboda masifar, sai ya ce wa mala’ikan wanda yake hallaka mutane, “Ya isa! Janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa yana tsaye a masussukar Ornan mutumin Yebus. |