22 | GEN 1:22 | Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” |
28 | GEN 1:28 | Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.” |
33 | GEN 2:2 | Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. |
44 | GEN 2:13 | Sunan kogi na biyu, Gihon. Shi ne ya malala kewaye da ƙasar Kush. |
45 | GEN 2:14 | Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites. |
47 | GEN 2:16 | Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, |
57 | GEN 3:1 | To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?” |
59 | GEN 3:3 | amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ” |
67 | GEN 3:11 | Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?” |
73 | GEN 3:17 | Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka. |
78 | GEN 3:22 | Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.” |
81 | GEN 4:1 | Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.” |
82 | GEN 4:2 | Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. |
83 | GEN 4:3 | Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. |
85 | GEN 4:5 | amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace. |
86 | GEN 4:6 | Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace? |
88 | GEN 4:8 | To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe. |
89 | GEN 4:9 | Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?” |
93 | GEN 4:13 | Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina. |
95 | GEN 4:15 | Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi. |
96 | GEN 4:16 | Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden. |
97 | GEN 4:17 | Kayinu ya kwana da matarsa, ta kuwa yi ciki, ta haifi Enok. A lokacin Kayinu yana gina birni, sai ya sa wa birnin sunan ɗansa Enok. |
102 | GEN 4:22 | Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama. |
103 | GEN 4:23 | Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla, “Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata. Na kashe wani saboda ya yi mini rauni, na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo. |
104 | GEN 4:24 | Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.” |
105 | GEN 4:25 | Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.” |
115 | GEN 5:9 | Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan. |
116 | GEN 5:10 | Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
118 | GEN 5:12 | Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel. |
119 | GEN 5:13 | Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata |
120 | GEN 5:14 | Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu. |
154 | GEN 6:16 | Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin. Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe. |
162 | GEN 7:2 | Ka ɗauki bakwai na kowace iri tsabtaccen dabba tare da kai, namiji da ta mace, da kuma biyu na kowace dabba marar tsabta, namiji da ta mace, |
164 | GEN 7:4 | Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.” |
177 | GEN 7:17 | Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya. |
181 | GEN 7:21 | Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane. |
182 | GEN 7:22 | Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu. |
201 | GEN 8:17 | Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.” |
207 | GEN 9:1 | Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya. |
209 | GEN 9:3 | Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome. |
224 | GEN 9:18 | ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.) |
228 | GEN 9:22 | Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje. |
231 | GEN 9:25 | sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.” |
232 | GEN 9:26 | Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem. |
233 | GEN 9:27 | Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet; bari Yafet yă zauna a tentunan Shem, bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.” |
239 | GEN 10:4 | ’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. |
241 | GEN 10:6 | ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana. |
242 | GEN 10:7 | ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan. |
243 | GEN 10:8 | Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya. |
245 | GEN 10:10 | Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar. |
246 | GEN 10:11 | Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala |
247 | GEN 10:12 | da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni. |
249 | GEN 10:14 | Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa. |
250 | GEN 10:15 | Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa, |
253 | GEN 10:18 | Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu |
254 | GEN 10:19 | har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha. |
270 | GEN 11:3 | Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka. |
271 | GEN 11:4 | Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.” |
295 | GEN 11:28 | Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa. |
298 | GEN 11:31 | Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can. |
304 | GEN 12:5 | Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana. |
305 | GEN 12:6 | Abram ya ratsa ƙasar har zuwa wurin babban itace na More a Shekem. A lokacin Kan’aniyawa suna a ƙasar. |
326 | GEN 13:7 | Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne. |
327 | GEN 13:8 | Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne. |
331 | GEN 13:12 | Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom. |
338 | GEN 14:1 | A zamanin Amrafel sarkin Shinar, shi da Ariyok sarkin Ellasar, Kedorlayomer sarkin Elam, da kuma Tidal sarkin Goyim |
340 | GEN 14:3 | Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri). |
341 | GEN 14:4 | Shekara goma sha biyu suna bauta wa Kedorlayomer, amma a shekara ta sha uku sai suka yi tawaye. |
342 | GEN 14:5 | A shekara ta goma sha huɗu, Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi suka tafi suka cinye Refahiyawa a Ashterot Karnayim, Zuziyawa a Ham, Emawa a Shabe Kiriyatayim, |
344 | GEN 14:7 | Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar. |
345 | GEN 14:8 | Sai sarkin Sodom, sarkin Gomorra, sarkin Adma, sarkin Zeboyim da sarkin Bela (wato, Zowar), suka fita suka ja dāgā a Kwarin Siddim |
346 | GEN 14:9 | gāba da Kedorlayomer sarkin Elam, Tidal sarkin Goyim, Amrafel sarkin Shinar da Ariyok sarkin Ellasar; sarakuna huɗu gāba da biyar. |
347 | GEN 14:10 | Kwarin Siddim kuwa ya cika da ramummukan kwalta, sa’ad da sarakunan Sodom da Gomorra suka gudu kuwa, waɗansu mutane suka fāɗa cikin ramummukan kwaltan, sauran kuwa suka gudu zuwa tuddai. |
354 | GEN 14:17 | Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki). |
357 | GEN 14:20 | Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.” Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. |
358 | GEN 14:21 | Sarkin Sodom ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanena da ka ƙwace daga hannun sarakunan nan kawai, ka riƙe kayayyakin don kanka.” |
362 | GEN 15:1 | Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa, “Kada ka ji tsoro, Abram. Ni ne garkuwarka, kuma ladanka zai zama mai girma.” |
366 | GEN 15:5 | Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.” |
368 | GEN 15:7 | Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.” |
370 | GEN 15:9 | Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.” |
374 | GEN 15:13 | Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani tabbatacce cewa shekaru ɗari huɗu, zuriyarka za tă zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, za a mai da su bayi, a kuma wulaƙanta su. |
380 | GEN 15:19 | ƙasar Keniyawa, Kenizziyawa, Kadmoniyawa, |
382 | GEN 15:21 | Amoriyawa, Kan’aniyawa, Girgashiyawa da kuma Yebusiyawa.” |
385 | GEN 16:3 | Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa. |
387 | GEN 16:5 | Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.” |
388 | GEN 16:6 | Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta. |
391 | GEN 16:9 | Sai mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki Saira, ki yi mata biyayya.” |
395 | GEN 16:13 | Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.” |
396 | GEN 16:14 | Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered. |
406 | GEN 17:8 | Dukan ƙasar Kan’ana inda kake baƙo a yanzu, zan ba da ita a matsayin madawwamiyar mallaka gare ka da kuma zuriyarka a bayanka, zan kuma zama Allahnsu.” |
407 | GEN 17:9 | Sa’an nan Allah ya ce wa Ibrahim. “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, kai da zuriyarka bayanka, har tsararraki masu zuwa. |