30 | GEN 1:30 | Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance. |
66 | GEN 3:10 | Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.” |
70 | GEN 3:14 | Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka. |
96 | GEN 4:16 | Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden. |
102 | GEN 4:22 | Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama. |
103 | GEN 4:23 | Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla, “Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata. Na kashe wani saboda ya yi mini rauni, na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo. |
135 | GEN 5:29 | Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.” |
136 | GEN 5:30 | Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata. |
138 | GEN 5:32 | Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet. |
142 | GEN 6:4 | Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara. |
146 | GEN 6:8 | Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji. |
147 | GEN 6:9 | Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah. |
148 | GEN 6:10 | Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet. |
151 | GEN 6:13 | Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya. |
160 | GEN 6:22 | Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi. |
161 | GEN 7:1 | Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani. |
165 | GEN 7:5 | Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi. |
166 | GEN 7:6 | Nuhu yana da shekaru 106 ne sa’ad da aka yi ambaliya ruwa a duniya. |
167 | GEN 7:7 | Nuhu da matarsa da ’ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya. |
169 | GEN 7:9 | namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu. |
171 | GEN 7:11 | A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. |
173 | GEN 7:13 | A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi. |
175 | GEN 7:15 | Biyu-biyu na dukan halittu masu numfashi suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi. |
176 | GEN 7:16 | Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya. |
183 | GEN 7:23 | Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi. |
185 | GEN 8:1 | Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye. |
190 | GEN 8:6 | Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, |
193 | GEN 8:9 | Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi. |
195 | GEN 8:11 | Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya. |
197 | GEN 8:13 | A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe. |
199 | GEN 8:15 | Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, |
202 | GEN 8:18 | Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa, |
204 | GEN 8:20 | Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden. |
207 | GEN 9:1 | Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya. |
214 | GEN 9:8 | Sai Allah ya ce wa Nuhu da ’ya’yansa, |
217 | GEN 9:11 | Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba.” |
219 | GEN 9:13 | Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya. |
223 | GEN 9:17 | Saboda haka Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na kafa tsakanina da dukan masu rai a duniya.” |
224 | GEN 9:18 | ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.) |
225 | GEN 9:19 | Waɗannan su ne ’ya’yan Nuhu maza uku, daga gare su ne kuma duniya za tă cika da mutane. |
226 | GEN 9:20 | Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi. |
230 | GEN 9:24 | Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi, |
234 | GEN 9:28 | Bayan ambaliyar, Nuhu ya yi shekaru 350. |
235 | GEN 9:29 | Gaba ɗaya dai, Nuhu ya yi shekara 950, sa’an nan ya mutu. |
236 | GEN 10:1 | Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar. |
243 | GEN 10:8 | Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya. |
244 | GEN 10:9 | Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji. |
246 | GEN 10:11 | Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala |
247 | GEN 10:12 | da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni. |
248 | GEN 10:13 | Mizrayim shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa, |
267 | GEN 10:32 | Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya. |
289 | GEN 11:22 | Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor. |
290 | GEN 11:23 | Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
291 | GEN 11:24 | Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera. |
292 | GEN 11:25 | Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
293 | GEN 11:26 | Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran. |
294 | GEN 11:27 | Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot. |
296 | GEN 11:29 | Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska. |
308 | GEN 12:9 | Sa’an nan Abram ya tashi ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Negeb. |
310 | GEN 12:11 | Yayinda yana gab da shiga Masar, sai ya ce wa matarsa Saira, “Na sani ke kyakkyawar mace ce. |
320 | GEN 13:1 | Saboda haka Abram ya haura daga Masar zuwa Negeb tare da matarsa, da dukan abin da yake da shi tare da Lot. |
322 | GEN 13:3 | Daga Negeb, ya ci gaba da tafiyarsa a wurare dabam-dabam har ya kai tsakanin Betel da Ai, a inda dā ya kafa tentinsa na fari |
359 | GEN 14:22 | Amma Abram ya ce, wa sarkin Sodom, “Na ɗaga hannu ga Ubangiji Allah Mafi Ɗaukaka, Mahaliccin sama da ƙasa, na riga na rantse |
360 | GEN 14:23 | cewa ba zan karɓi kome da yake naka ba, ko zare ko maɗaurin takalma, don kada ka ce, ‘Na azurta Abram.’ |
362 | GEN 15:1 | Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa, “Kada ka ji tsoro, Abram. Ni ne garkuwarka, kuma ladanka zai zama mai girma.” |
368 | GEN 15:7 | Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.” |
387 | GEN 16:5 | Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.” |
399 | GEN 17:1 | Sa’ad da Abram ya yi shekaru 99, sai Ubangiji ya bayyana a gare shi ya ce, ni “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi tafiya a gabana ka kuma zama marar abin zargi. |
479 | GEN 19:21 | Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba. |
497 | GEN 20:1 | Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi wajajen Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. Ya zauna a Gerar na ɗan lokaci, |
501 | GEN 20:5 | Ba shi ne ya ce mini, ‘Ita ’yar’uwata ba ce,’ ita ma ba tă ce, ‘Shi ɗan’uwana ba ne’? Na yi haka da kyakkyawan nufi da hannuwa masu tsabta.” |
507 | GEN 20:11 | Ibrahim ya ce, “Na ce a raina, ‘Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’ |
538 | GEN 21:24 | Ibrahim ya ce, “Na rantse.” |
555 | GEN 22:7 | sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?” |
564 | GEN 22:16 | ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba, |
568 | GEN 22:20 | Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka, ’ya’ya maza; |
571 | GEN 22:23 | Betuwel ya haifi Rebeka. Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan ’ya’ya maza takwas. |
576 | GEN 23:4 | “Ni baƙo ne, kuma baƙo a cikinku. Ku sayar mini da wani wuri yă zama wurin binnewa a nan, domin in binne mataccena.” |
583 | GEN 23:11 | Ya ce, “A’a, ranka yă daɗe, ka ji ni, na ba ka filin, na kuma ba ka kogon da yake cikinsa. Na ba ka shi a gaban mutanena. Ka binne mataccenka.” |
602 | GEN 24:10 | Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor. |
607 | GEN 24:15 | Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim. |
616 | GEN 24:24 | Sai ta ce masa, “Ni ’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.” |
619 | GEN 24:27 | yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna alheri da amincinsa ga maigidana ba. Ni kam, Ubangiji ya bishe ni a tafiyata zuwa gidan ’yan’uwan maigidana.” |
622 | GEN 24:30 | Nan da nan da ya ga zoben hancin da woroworo a hannuwan ’yar’uwansa, ya kuma ji Rebeka ta faɗa abin da mutumin ya ce mata, sai ya fita zuwa wurin mutumin, ya same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar. |
626 | GEN 24:34 | Saboda haka ya ce, “Ni bawan Ibrahim ne. |
639 | GEN 24:47 | “Na tambaye ta, ‘Ke ’yar wane ne?’ “Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ “Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata, |
640 | GEN 24:48 | na kuma sunkuya na yi wa Ubangiji sujada. Na yabi Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim wanda ya bi da ni a hanyar da take daidai, don in samo wa ɗan maigidana jikanyar ɗan’uwansa. |
654 | GEN 24:62 | Ishaku kuwa ya zo daga Beyer-Lahai-Royi, gama yana zama a Negeb. |
672 | GEN 25:13 | Ga jerin sunayen ’ya’yan Ishmayel maza bisa ga haihuwarsu, Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam, |
674 | GEN 25:15 | Hadad, Tema, Yetur, Nafish da Kedema. |
717 | GEN 26:24 | A wannan dare Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka Ibrahim. Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan albarkace ka, zan kuma ƙara yawan zuriyarka saboda bawana Ibrahim.” |
747 | GEN 27:19 | Yaƙub ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini. Ina roƙonka tashi ka zauna ka ci naman, domin ka sa mini albarkarka.” |
752 | GEN 27:24 | Ya tambaya, “Tabbatacce kai ne ɗana Isuwa?” Ya amsa ya ce “Ni ne.” |
760 | GEN 27:32 | Mahaifinsa Ishaku ya tambaye shi, “Wane ne kai?” Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.” |
765 | GEN 27:37 | Ishaku ya amsa wa Isuwa, “Na mai da shi shugaba a kanka, na sa dukan dangoginsa su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Saboda haka me kuma zan yi maka ɗana?” |
774 | GEN 27:46 | Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.” |