Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   S    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

3  GEN 1:3  Sai Allah ya ce, “Bari haske kasance,” sai kuwa ga haske.
7  GEN 1:7  Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance.
11  GEN 1:11  Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.
26  GEN 1:26  Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”
27  GEN 1:27  Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su.
29  GEN 1:29  Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku.
35  GEN 2:4  Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su. Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai,
38  GEN 2:7  Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
42  GEN 2:11  Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.
44  GEN 2:13  Sunan kogi na biyu, Gihon. Shi ne ya malala kewaye da ƙasar Kush.
45  GEN 2:14  Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites.
51  GEN 2:20  Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye. Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba.
52  GEN 2:21  Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama.
53  GEN 2:22  Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
54  GEN 2:23  Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”
62  GEN 3:6  Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.
63  GEN 3:7  Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.
67  GEN 3:11  Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
69  GEN 3:13  Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
70  GEN 3:14  Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin,Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.
72  GEN 3:16  Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.”
73  GEN 3:17  Ga Adamu kuwa ya ce,Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
79  GEN 3:23  Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi.
81  GEN 4:1  Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.”
82  GEN 4:2  Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.
85  GEN 4:5  amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace.
86  GEN 4:6  Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace?
89  GEN 4:9  Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”
90  GEN 4:10  Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa.
95  GEN 4:15  Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi.
96  GEN 4:16  Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden.
101  GEN 4:21  Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa.
105  GEN 4:25  Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.”
106  GEN 4:26  Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh. A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji.
107  GEN 5:1  Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.
108  GEN 5:2  Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”
109  GEN 5:3  Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.
110  GEN 5:4  Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
112  GEN 5:6  Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh.
113  GEN 5:7  Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
114  GEN 5:8  Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
115  GEN 5:9  Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan.
118  GEN 5:12  Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel.
121  GEN 5:15  Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared.
124  GEN 5:18  Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok.
127  GEN 5:21  Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela.
130  GEN 5:24  Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
131  GEN 5:25  Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek.
134  GEN 5:28  Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa.
138  GEN 5:32  Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.
139  GEN 6:1  Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ’ya’ya mata,
141  GEN 6:3  Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.”
145  GEN 6:7  Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
148  GEN 6:10  Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
151  GEN 6:13  Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya.
152  GEN 6:14  Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires, ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje.
161  GEN 7:1  Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu.Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani.
173  GEN 7:13  A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi.
176  GEN 7:16  Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya.
192  GEN 8:8  Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa.
195  GEN 8:11  Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya.
197  GEN 8:13  A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe.
199  GEN 8:15  Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu,
202  GEN 8:18  Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa,
204  GEN 8:20  Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden.
207  GEN 9:1  Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya.
214  GEN 9:8  Sai Allah ya ce wa Nuhu da ’ya’yansa,
223  GEN 9:17  Saboda haka Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na kafa tsakanina da dukan masu rai a duniya.”
224  GEN 9:18  ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.)
227  GEN 9:21  Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa.
229  GEN 9:23  Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu.
230  GEN 9:24  Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi,
232  GEN 9:26  Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem.
233  GEN 9:27  Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet; bari Yafet yă zauna a tentunan Shem, bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.”
236  GEN 10:1  Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
242  GEN 10:7  ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan.
244  GEN 10:9  Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
245  GEN 10:10  Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
250  GEN 10:15  Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,
252  GEN 10:17  Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
254  GEN 10:19  har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
256  GEN 10:21  Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
257  GEN 10:22  ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
259  GEN 10:24  Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
261  GEN 10:26  Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,
263  GEN 10:28  Obal, Abimayel, Sheba,
265  GEN 10:30  Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
266  GEN 10:31  Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.