Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   T    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

2  GEN 1:2  To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
32  GEN 2:1  Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.
39  GEN 2:8  To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi.
45  GEN 2:14  Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites.
50  GEN 2:19  To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan.
57  GEN 3:1  To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen,Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
60  GEN 3:4  Maciji ya ce wa macen,Tabbatacce ba za ku mutu ba.
78  GEN 3:22  Ubangiji Allah ya kuma ce,To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.”
88  GEN 4:8  To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.
102  GEN 4:22  Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama.
174  GEN 7:14  Tare da su kuwa, akwai kowane naman jeji bisa ga irinsa, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinta, da kowane tsuntsun gida da na jeji bisa ga irinsa, da dukan abu mai fiffike.
237  GEN 10:2  ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
238  GEN 10:3  ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
239  GEN 10:4  ’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
268  GEN 11:1  To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.
291  GEN 11:24  Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera.
292  GEN 11:25  Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
293  GEN 11:26  Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.
294  GEN 11:27  Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.
295  GEN 11:28  Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa.
298  GEN 11:31  Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.
299  GEN 11:32  Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.
300  GEN 12:1  Ubangiji ya ce wa Abram,Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.
309  GEN 12:10  To, a lokacin, an yi yunwa a ƙasar, sai Abram ya gangara zuwa Masar don yă zauna a can na ɗan lokaci, domin yunwa ta yi tsanani.
318  GEN 12:19  Don me ka ruɗe ni cewa, ‘Ita ’yar’uwata ce,’ har na ɗauke ta tă zama matata? To, ga matarka. Ɗauke ta ka tafi.”
336  GEN 13:17  Tafi, ka ratsa tsawo da fāɗin ƙasar, gama zan ba ka ita.”
338  GEN 14:1  A zamanin Amrafel sarkin Shinar, shi da Ariyok sarkin Ellasar, Kedorlayomer sarkin Elam, da kuma Tidal sarkin Goyim
340  GEN 14:3  Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri).
344  GEN 14:7  Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar.
346  GEN 14:9  gāba da Kedorlayomer sarkin Elam, Tidal sarkin Goyim, Amrafel sarkin Shinar da Ariyok sarkin Ellasar; sarakuna huɗu gāba da biyar.
383  GEN 16:1  To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar,
384  GEN 16:2  saboda haka sai ta ce wa Abram, “Ubangiji ya hana mini haihuwar ’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.” Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa.
390  GEN 16:8  Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”
418  GEN 17:20  Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma!
430  GEN 18:5  Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.” Suka ce,To, sai ka yi abin da ka ce.”
434  GEN 18:9  Sai suka ce masa, “Ina Saratu matarka?” Ibrahim ya ce,Tana can cikin tenti.”
450  GEN 18:25  Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”
494  GEN 19:36  Ta haka ’ya’yan Lot biyu mata duk suka yi ciki daga mahaifinsu.
505  GEN 20:9  Sa’an nan Abimelek ya kira Ibrahim ciki ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ta wace hanya ce na yi maka laifi har da ka kawo irin wannan babban laifi a kaina da kuma masarautata? Ka yi mini abubuwan da bai kamata a yi ba.”
507  GEN 20:11  Ibrahim ya ce, “Na ce a raina,Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’
521  GEN 21:7  Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”
528  GEN 21:14  Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.
562  GEN 22:14  Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji, za a tanada.”
572  GEN 22:24  Ban da haka ma, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifa masa ’ya’ya maza, Teba, Gaham, Tahash da kuma Ma’aka.
574  GEN 23:2  Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.
589  GEN 23:17  Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka
606  GEN 24:14  Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”
608  GEN 24:16  Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.
610  GEN 24:18  Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha.
617  GEN 24:25  Ta ƙara da cewa, “Muna da isashen ciyawa da abincin dabbobi, da kuma wuri domin ku kwana.”
633  GEN 24:41  Ta haka za ka kuɓuta daga rantsuwata sa’ad da ka tafi wurin dangina, ko ma sun ƙi su ba ka ita, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’
637  GEN 24:45  “Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’
638  GEN 24:46  Ta yi sauri ta saukar da tulun daga kafaɗarta ta ce, ‘Sha, zan kuma ba wa raƙumanka su ma.’ Sai na sha, ta kuma shayar da raƙumana su ma.
639  GEN 24:47  “Na tambaye ta, ‘Ke ’yar wane ne?’Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ “Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata,
656  GEN 24:64  Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri,
659  GEN 24:67  Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.
661  GEN 25:2  Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.
674  GEN 25:15  Hadad, Tema, Yetur, Nafish da Kedema.
693  GEN 25:34  Sa’an nan Yaƙub ya ba wa Isuwa burodi da ɗan miyan lansir. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya tashi ya tafi. Ta haka Isuwa ya yi banza da matsayinsa na ɗan fari.
702  GEN 26:9  Saboda haka Abimelek ya aika Ishaku yă je, sa’an nan ya ce,Tabbatacce ita matarka ce! Me ya sa ka ce, ‘Ita ’yar’uwata ce?’ ” Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”
752  GEN 27:24  Ya tambaya, Tabbatacce kai ne ɗana Isuwa?” Ya amsa ya ce “Ni ne.”
761  GEN 27:33  Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce,To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!”
771  GEN 27:43  To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran.
776  GEN 28:2  Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin ’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka.
790  GEN 28:16  Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce,Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba.”
805  GEN 29:9  Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce.
828  GEN 29:32  Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben, gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.”
829  GEN 29:33  Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon.
831  GEN 29:35  Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda. Sa’an nan ta daina haihuwa.
847  GEN 30:16  Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare.
855  GEN 30:24  Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”
871  GEN 30:40  Sai Yaƙub yă ware ƙananan garken dabam, amma sai yă sa sauran su fuskanci dabbobin da suke dabbare-dabbare da kuma baƙaƙe da suke na Laban. Ta haka ya ware garkuna dabam domin kansa bai kuwa haɗa su da dabbobin Laban ba.
874  GEN 30:43  Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna.
883  GEN 31:9  Ta haka Allah ya kwashe dabbobin mahaifinku ya ba ni.
890  GEN 31:16  Tabbatacce dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga mahaifinmu ya zama namu da ’ya’yanmu. Saboda haka ka yi duk abin da Allah ya faɗa maka.”
912  GEN 31:38  “Na kasance tare da kai shekaru ashirin. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuwa ci raguna daga garkunanka ba.
916  GEN 31:42  Da ba don Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim da kuma Tsoron Ishaku ya kasance tare da ni ba, tabbatacce da ka sallame ni hannu wofi. Amma Allah ya ga wahalata da famar hannuwana, ya kuwa tsawata maka da dare jiya.”
927  GEN 31:53  Bari Allah na Ibrahim da Allah na Nahor, Allah na iyayensu, yă zama alƙali tsakaninmu.” Saboda haka Yaƙub ya yi rantsuwa da sunan Tsoron mahaifinsa Ishaku.
941  GEN 32:13  Amma ka riga ka faɗa,Tabbatacce zan sa ka yi albarka. Zan kuma sa zuriyarka su zama kamar yashin teku da ba a iya ƙirgawa.’ ”
976  GEN 33:15  Sai Isuwa ya ce,To, bari in bar waɗansu mutanena tare da kai.” Yaƙub ya ce, “Amma me ya sa za ka yi haka? Bari dai in sami tagomashi a idanunka ranka yă daɗe.”
982  GEN 34:1  To, Dina, ’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar.
1012  GEN 34:31  Amma ’ya’yansa suka amsa,To, ya dace ke nan da ya yi da ’yar’uwarmu kamar karuwa?”
1020  GEN 35:8  To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.
1031  GEN 35:19  Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem).
1052  GEN 36:11  ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.
1053  GEN 36:12  Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.
1056  GEN 36:15  Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa, ’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,
1063  GEN 36:22  ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ’yar’uwar Lotan ce.
1075  GEN 36:34  Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.
1081  GEN 36:40  Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne, Timna, Alwa, Yetet.
1083  GEN 36:42  Kenaz, Teman, Mibzar.
1096  GEN 37:12  To, ’yan’uwansa suka tafi kiwon garkunan mahaifinsu kusa da Shekem.
1097  GEN 37:13  Sai Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Kamar yadda ka sani, ’yan’uwanka suna kiwon garkuna kusa da Shekem. Zo, in aike ka gare su.” Ya ce,To.”
1108  GEN 37:24  suka kuma ɗauke shi suka jefa a cikin rijiya. To, rijiyar wofi ce, babu ruwa a ciki.
1117  GEN 37:33  Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”