1 | GEN 1:1 | A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. |
2 | GEN 1:2 | To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan. |
3 | GEN 1:3 | Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. |
4 | GEN 1:4 | Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. |
5 | GEN 1:5 | Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan. |
6 | GEN 1:6 | Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” |
7 | GEN 1:7 | Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. |
8 | GEN 1:8 | Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan. |
9 | GEN 1:9 | Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. |
10 | GEN 1:10 | Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. |
11 | GEN 1:11 | Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. |
12 | GEN 1:12 | Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. |
13 | GEN 1:13 | Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan. |
14 | GEN 1:14 | Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, |
15 | GEN 1:15 | bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. |
16 | GEN 1:16 | Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. |
17 | GEN 1:17 | Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, |
18 | GEN 1:18 | su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. |
19 | GEN 1:19 | Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan. |
20 | GEN 1:20 | Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” |
21 | GEN 1:21 | Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. |
22 | GEN 1:22 | Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” |
23 | GEN 1:23 | Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan. |
24 | GEN 1:24 | Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. |