1566 | EXO 2:11 | Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa. |
1647 | EXO 5:14 | Manyan Isra’ilawa waɗanda shugabannin gandun Fir’auna suka naɗa, suka sha dūka, aka kuma yi musu tambayoyi ana cewa, “Don me ba ku cika yawan tubula na jiya da na yau kamar yadda kuka saba ba?” |
1649 | EXO 5:16 | Ba a ba wa bayinka tattaka, duk da haka ana ce mana, ‘Ku yi tubula!’ Ana wa bayinka dūka, amma fa laifin na mutanenka ne.” |
2098 | EXO 21:20 | “In mutum ya dūke bawansa ko baiwarsa da sanda, sai bawan ko baiwar ta mutu saboda dūkan, dole a hukunta shi, |
3231 | LEV 16:29 | “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare ku. A rana ta goma ga wata na bakwai, dole ku yi mūsu kanku, ba kuwa za ku yi wani aiki ba, ko da mutum baƙo ne a cikinku ko kuwa ɗan ƙasa, |
3233 | LEV 16:31 | Asabbaci ne don hutawa, kuma dole ku yi mūsun kanku; wannan dawwammamiyar farilla ce. |
3430 | LEV 23:27 | “Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. |
3432 | LEV 23:29 | Duk wanda bai yi mūsun kansa a wannan rana ba, dole a raba shi daga mutanensa. |
3435 | LEV 23:32 | Asabbaci ne na hutu dominku, kuma dole ku yi mūsun kanku. Daga yamman rana ta tara ga wata, har zuwa yamma na biye, za ku kiyaye Asabbacinku.” |
5550 | DEU 25:1 | Idan mūsu ya tashi tsakanin mutum biyu har abin ya kai su kotu, alƙalai kuwa suka yanke hukunci a kan batun, suka kuɓutar da marar laifi sa’an nan suka hukunta mai laifi, |
14256 | PSA 23:4 | Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya. |
16643 | PRO 6:33 | Dūka da kunya ne za su zama rabonsa, kuma kunyarsa za tă dawwama. |
16953 | PRO 17:10 | Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari. |
16977 | PRO 18:6 | Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka. |
17024 | PRO 19:29 | An shirya tara saboda masu ba’a ne, dūka kuma saboda bayan wawaye. |
17054 | PRO 20:30 | Naushi da rauni kan share mugunta, dūka kuma kan tsabtacce lamiri. |
17675 | SNG 5:7 | Masu gadi suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni. Suka yi mini dūka, suka yi mini rauni; suka ƙwace gyalena waɗannan masu gadin katanga! |
17729 | ISA 1:5 | Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo. |
17944 | ISA 10:24 | Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ya mutanena masu zama a Sihiyona, kada ku ji tsoron Assuriyawa, waɗanda suka dūke ku da sanda suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi. |
18738 | ISA 50:6 | Na ba da bayana ga masu dūkana, kumatuna ga masu jan gemuna; ban ɓoye fuskata daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba. |
18883 | ISA 59:13 | tawaye da mūsun Ubangiji, mun juye bayanmu ga Allahnmu, zugawa a yi zalunci da tayarwa, faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya. |
19493 | JER 20:2 | sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji. |
19958 | JER 37:15 | Suka yi fushi da Irmiya suka sa aka yi masa dūka aka kuma jefa shi cikin kurkuku a gidan Yonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku. |
23519 | MAT 10:33 | Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama. |
23930 | MAT 21:35 | “Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun. |
24075 | MAT 24:49 | Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. |
24157 | MAT 26:34 | Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.” |
24158 | MAT 26:35 | Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka. |
24193 | MAT 26:70 | Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.” |
24195 | MAT 26:72 | Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!” |
24198 | MAT 26:75 | Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka. |
24745 | MRK 12:3 | Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi. |
24853 | MRK 14:30 | Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyukai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.” |
24854 | MRK 14:31 | Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka. |
24891 | MRK 14:68 | Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure. |
24895 | MRK 14:72 | Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu,za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka. |
25393 | LUK 9:23 | Sai ya ce wa dukansu, “In wani zai bi ni, dole yă mūsanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni. |
25462 | LUK 10:30 | Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa. |
25537 | LUK 12:9 | Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah. |
25573 | LUK 12:45 | Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sa’an nan ya fara dūkan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa. |
25576 | LUK 12:48 | Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi. |
25858 | LUK 20:10 | A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi. |
25859 | LUK 20:11 | Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi. |
25967 | LUK 22:34 | Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.” |
25990 | LUK 22:57 | Amma ya yi mūsu ya ce, “Mace, ban san shi ba!” |
25994 | LUK 22:61 | Ubangiji kuma ya juya ya kafa wa Bitrus ido. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Ubangiji ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.” |
25996 | LUK 22:63 | Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka. |
26133 | JHN 1:20 | Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.” |
26737 | JHN 13:38 | Sai Yesu ya amsa ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku! |
26879 | JHN 18:25 | Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?” Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.” |
26881 | JHN 18:27 | Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara. |
27078 | ACT 3:13 | Allah na Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub, Allah na kakanninmu, ya ɗaukaka bawansa Yesu. Ku kuka ba da shi domin a kashe, kuka yi mūsun saninsa a gaban Bilatus, ko da yake ya yi niyya ya sake shi. |
27079 | ACT 3:14 | Kuka yi mūsun sanin Mai Tsarki da Mai Adalci kuka roƙa a sakar muku mai kisankai. |
27107 | ACT 4:16 | Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba. |
27574 | ACT 16:22 | Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. |
27589 | ACT 16:37 | Amma Bulus ya ce wa ma’aikatan, “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shari’a ba, ko da yake mu ’yan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? A’a! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.” |
27643 | ACT 18:17 | Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majami’a suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yă kula. |
27670 | ACT 19:16 | Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba. |
27690 | ACT 19:36 | Saboda haka, da yake ba dama a yi mūsun wannan gaskiya, ya kamata ku natsu kada ku yi kome da garaje. |
27764 | ACT 21:32 | Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron. Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus. |
27791 | ACT 22:19 | “Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka. |
28971 | 2CO 6:5 | Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. |
29080 | 2CO 11:23 | In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. |
29838 | 1TI 5:8 | In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni. |
29875 | 1TI 6:20 | Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi, |
29906 | 2TI 2:12 | in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu; |
29907 | 2TI 2:13 | in ba mu da aminci, shi dai mai aminci ne, domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.” |
29925 | 2TI 3:5 | suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su. |
29975 | TIT 1:16 | Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba. |
30568 | 2PE 2:1 | Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. |
30639 | 1JN 2:22 | Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi, ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan. |
30640 | 1JN 2:23 | Ba wanda yake mūsun Ɗan, sa’an nan yă ce yana da Uban; duk wanda ya yarda da Ɗan, yana da Uban a cikinsa ke nan. |
30744 | JUD 1:4 | Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu. |
30749 | JUD 1:9 | Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!” |
30798 | REV 2:13 | Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama. |
30822 | REV 3:8 | Na san ayyukanka. Duba, na sa a gabanka buɗaɗɗen ƙofa wadda ba mai iya rufewa. Na san cewa kana da ɗan ƙarfi, duk da haka ka kiyaye maganata ba ka kuwa yi mūsun sunana ba. |