2117 | EXO 22:2 | amma in ya faru bayan wayewar gari, to, za a nemi alhakin jinin ɓarawon a hannun wanda ya bugi ɓarawon. “Ɓarawon da aka kama da abin da ya sata, dole yă yi cikakkiyar ramuwa, amma in ba shi da kome, dole a sayar da shi a biya abin da ya sata. |
4003 | NUM 10:14 | Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba. |
11083 | 1CH 26:1 | Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne, Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin ’ya’yan Asaf maza. |
13231 | JOB 15:24 | Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi, kamar sarkin da yake shirin yaƙi, |
22834 | HAB 2:17 | Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka, kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka. Gama ka zub da jinin mutum; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu. |
26560 | JHN 10:10 | Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace. |