Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   Word’Word!    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

418  GEN 17:20  Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma!
1359  GEN 44:34  Yaya zan koma ga mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? A’a! Kada ka bari in ga baƙin cikin da zai auko wa mahaifina.”
4452  NUM 24:5  “Ina misalin kyan tentunanka, ya Yaƙub, wuraren zamanka, ya Isra’ila!
5841  DEU 33:29  Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.”
7056  JDG 19:30  Duk wanda ya gani, sai ya ce, “Ba a taɓa gani ko yin irin wannan abu ba, tun lokacin da Isra’ilawa suka fito daga Masar. Ku yi tunani wannan! Ku kuma yi la’akari! Ku gaya mana abin da za mu yi!”
7206  RUT 4:14  Mata suka ce wa Na’omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda a wannan rana bai bar ki ba tare da dangi mai fansa ba. Allah yă sa yă zama sananne a dukan Isra’ila!
8332  2SA 13:12  Ta ce, “Kada ka yi wannan ɗan’uwana! Kada ka tilasta ni. Bai kamata a yi irin wannan abu a Isra’ila ba! Kada ka yi wannan mugun abu.
10087  2KI 19:22  Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo? Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka, har ka tā da idanunka da fahariya? Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila!
11416  2CH 10:16  Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce, “Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda, wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse? Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila! Ka lura da gidanka, ya Dawuda!” Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida.
12984  JOB 6:2  “Da kawai za a iya auna wahalata a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!
14244  PSA 22:24  Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi! Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi! Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!
15285  PSA 81:9  “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!
17356  PRO 31:2  “Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina! Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!
17980  ISA 13:4  Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu, sai ka ce na babban taron jama’a! Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki, sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa! Ubangiji Maɗaukaki yana shirya mayaƙa don yaƙi.
18010  ISA 14:12  Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
18445  ISA 37:23  Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo? A kan wa ka tā da muryarka ka kuma daga idanu cikin fariya? A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!
19541  JER 22:18  Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’
20258  JER 50:23  Dubi yadda aka karya aka kuma ragargaza gudumar dukan duniya! Dubi yadda Babilon ta zama kufai a cikin al’ummai!
20322  JER 51:41  “Yadda za a ci Sheshak, taƙamar duniya duka za tă daina! Babilon za tă zama abar ƙyama a cikin al’ummai!
20326  JER 51:45  “Ku fito daga cikinta, jama’ata! Ku tsere da ranku! Ku tsere daga zafin fushin Ubangiji.
21460  EZK 36:32  Ina so ku san cewa ba na yi wannan saboda ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku ji kunya ku kuma giggita saboda halinku, ya gidan Isra’ila!
21674  EZK 44:6  Faɗa wa ’yan tawayen gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ayyukan banƙyamarku sun isa haka, ya gidan Isra’ila!
22222  HOS 5:1  “Ku ji wannan, ku firistoci! Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa! Ku saurara, ya ku gidan sarauta! Wannan hukunci yana a kanku, kun zama tarko a Mizfa, ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor.
22553  AMO 8:3  “A ranan nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Waƙoƙin a haikali za su koma makoki. Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!”
22903  ZEP 3:14  Ki rera, ya Diyar Sihiyona; ki tā da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki, Ya Diyar Urushalima!
23085  ZEC 9:17  Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa! Hatsi zai sa samari su yi murna, sabon ruwan inabi kuma zai sa ’yan mata su yi farin ciki.
24240  MAT 27:42  “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.
24379  MRK 3:22  Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”
24541  MRK 7:9  Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku!
25579  LUK 12:51  Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne.
25590  LUK 13:3  Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.
25592  LUK 13:5  Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.”
26446  JHN 7:49  A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.”
27522  ACT 15:11  A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
27589  ACT 16:37  Amma Bulus ya ce wa ma’aikatan, “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shari’a ba, ko da yake mu ’yan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? A’a! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.”