549 | GEN 22:1 | Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” |
5602 | DEU 27:15 | “La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa siffa, ko ya yi zubin gunki, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannu mai sana’a da aka kafa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5603 | DEU 27:16 | “La’ananne ne mutumin da ya ƙasƙantar da mahaifinsa ko mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5604 | DEU 27:17 | “La’ananne ne mutumin da ya gusar da dutsen da aka kafa don nuna shaidar iyaka.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5605 | DEU 27:18 | “La’ananne ne mutumin da ya karkatar da makaho daga hanya.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5606 | DEU 27:19 | “La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5607 | DEU 27:20 | “La’ananne ne mutumin da ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya ƙasƙantar da gadon mahaifinsa ke nan.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5608 | DEU 27:21 | “La’ananne ne mutumin da ya yi jima’i da dabba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5609 | DEU 27:22 | “La’ananne ne mutumin da ya kwana da ’yar’uwarsa, ’yar mahaifinsa ko ’yar mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5610 | DEU 27:23 | “La’ananne ne mutumin da ya kwana da mahaifiyar matarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5611 | DEU 27:24 | “La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5612 | DEU 27:25 | “La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5613 | DEU 27:26 | “La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
8236 | 2SA 9:6 | Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.” |
8504 | 2SA 18:23 | Ya ce, “Ko mene ne zai faru, ina so in ruga da gudu.” Sai Yowab ya ce, “Ruga!” Sai Ahimawaz ya sheƙa a guje ya bi ta hanyar fili ya riga mutumin Kush nan. |
14334 | PSA 29:9 | Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!” |
15766 | PSA 106:48 | Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Yabo ga Ubangiji. |
20643 | EZK 6:11 | “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ku tafa hannuwanku tare ku kuma taka ƙafafunku ku yi ihu ku ce, “Kaito!” Saboda dukan mugaye da kuma abubuwan banƙyama na gidan Isra’ila, gama za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba. |
24566 | MRK 7:34 | Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”). |
24718 | MRK 11:9 | Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!” |
24868 | MRK 14:45 | Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba. |
26662 | JHN 12:13 | Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!” |
26952 | JHN 20:16 | Yesu ya ce mata, “Maryamu.” Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”). |
27295 | ACT 9:10 | A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.” |
27331 | ACT 10:3 | Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!” |
30862 | REV 6:1 | Na kalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!” |
30864 | REV 6:3 | Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!” |
30866 | REV 6:5 | Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa. |
30868 | REV 6:7 | Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!” |
31166 | REV 22:17 | Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta. |