3 | GEN 1:3 | Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. |
10 | GEN 1:10 | Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. |
395 | GEN 16:13 | Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.” |
610 | GEN 24:18 | Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha. |
635 | GEN 24:43 | Duba, ina tsaye kusa da wannan rijiya; in wata yarinya ta fito domin tă ɗiba ruwa, wadda in na ce mata, “Ina roƙonki bari in ɗan sha ruwa daga tulunki,” |
636 | GEN 24:44 | in ta ce, “Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma,” bari tă zama wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’ |
700 | GEN 26:7 | Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, “’Yar’uwata ce,” gama yana tsoro yă ce, “Ita matata ce.” Ya yi tunani, “Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce.” |
1133 | GEN 38:13 | Sa’ad da aka faɗa wa Tamar cewa, “Surukinki yana kan hanyarsa zuwa Timna don askin tumakinsa,” |
1169 | GEN 39:19 | Sa’ad da maigidansa ya ji labarin da matarsa ta faɗa masa cewa, “Ga yadda bawanka ya yi da ni,” sai ya husata. |
1454 | GEN 48:2 | Sa’ad da aka faɗa wa Yaƙub, “Ɗanka Yusuf ya zo gare ka,” sai Isra’ila ya ƙoƙarta ya tashi ya zauna a kan gado. |
1628 | EXO 4:26 | Sai Ubangiji ya ƙyale shi. (A lokacin ta ce “angon jini,” tana nufin kaciya.) |
3813 | NUM 5:20 | Amma in kin kauce yayinda kike auren mijinki, kika kuma ƙazantar da kanki ta wurin kwana da wani dabam da ba mijinki ba,” |
5262 | DEU 12:20 | Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya fadada iyakarku kamar yadda ya yi muku alkawari, kuka kuma ji marmarin nama, kuka kuma ce, “Muna so mu ci nama,” to, za ku iya cin yadda kuke so. |
5276 | DEU 13:3 | in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,” |
5330 | DEU 15:9 | Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku. |
5337 | DEU 15:16 | Amma in bawanka ya ce maka, “Ba na so in bar ka,” saboda yana ƙaunarka da iyalinka, ya kuma fiye masa yă zauna da kai, |
5380 | DEU 17:14 | Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta, sai kuka ce, “Bari mu naɗa sarki a kanmu kamar sauran al’umman da suke kewaye da mu,” |
5486 | DEU 22:14 | ya kuma zarge ta, ya ba ta mummunan suna, yana cewa, “Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, ban sami tabbaci cewa ita budurwa ba ce,” |
5557 | DEU 25:8 | Sai dattawan garinsa su kira shi, su kuma yi masa magana. In ya nace yana cewa, “Ba na so in aure ta,” |
6688 | JDG 6:32 | Saboda haka a ranar suka kira Gideyon, “Yerub-Ba’al,” suna cewa, “Bari Ba’al ya yi hamayya da shi,” domin ya rushe bagaden Ba’al. |
6869 | JDG 11:38 | Ya ce mata, “Ki tafi,” Ya bar ta tă tafi har wata biyu. Ita da ’yan matan suka tafi a kan duwatsu suka yi ta makoki domin ba za tă taɓa aure ba. |
6876 | JDG 12:5 | Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,” |
7088 | JDG 20:32 | Yayinda mutanen Benyamin suna cewa, “Muna cin nasara a kansu kamar dā,” Isra’ilawa kuwa suna cewa, “Mu yi ta jan da baya mu janye su daga birni zuwa kan hanyoyi.” |
7194 | RUT 4:2 | Bowaz kuwa ya kira dattawa guda goma na garin ya ce, “Ku zauna a nan,” suka kuwa zauna. |
8272 | 2SA 11:10 | Da aka gaya wa Dawuda, “Uriya bai tafi gida ba,” sai Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Ba ka zo daga wuri mai nisa ba? Me ya sa ba ka je gida ba?” |
8522 | 2SA 19:9 | Saboda haka sarki ya tashi, ya zauna a bakin hanyar shiga. Da aka faɗa wa mutane cewa, “Sarki yana zaune a bakin hanyar shiga,” sai duk suka zo gabansa. Ana cikin haka, Isra’ilawa dai sun riga sun tsere zuwa gidajensu. |
9378 | 1KI 18:34 | Ya ce, “Ku sāke yin haka,” sai suka sāke yin haka. Ya umarta, “Ku yi haka sau na uku,” suka kuma yi haka sau na uku. |
9446 | 1KI 20:35 | Ta wurin maganar Ubangiji, ɗaya daga cikin ’ya’ya maza na annabawa ya ce wa abokinsa, “Ka buge ni da makaminka,” amma mutumin ya ƙi. |
9533 | 1KI 22:50 | A lokacin Ahaziya ɗan Ahab ya ce wa Yehoshafat, “Bari mutanena su tafi tare da mutanenka,” amma Yehoshafat ya ƙi. |
9738 | 2KI 8:7 | Sai Elisha ya tafi Damaskus, Ben-Hadad mutumin Aram kuwa yana ciwo. Sa’ad da aka faɗa wa sarki, “Mutumin Allah ya hauro tun daga can zuwa nan,” |
9890 | 2KI 13:15 | Elisha ya ce wa Yehowash, “Ka samo baka da kibiyoyi,” ya kuwa yi haka. |
9892 | 2KI 13:17 | Ya ce masa, “Ka buɗe taga wajen gabas,” sai ya buɗe. Sai Elisha ya ce, “Ka harba!” Sai ya harba. Elisha ya ce, “Kibiyar nasara ta Ubangiji, kibiyar nasara a kan Aram! Za ka hallaka Arameyawa sarai a Afek.” |
9893 | 2KI 13:18 | Sa’an nan ya ce, “Ka ɗauki kibiyoyi,” sai sarkin ya ɗauko. Sai Elisha ya ce, “Ka caki ƙasa.” Sai ya caka sau uku sa’an nan ya daina. |
10002 | 2KI 17:15 | Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su. |
10050 | 2KI 18:22 | Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”? |
14083 | PSA 12:6 | “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.” |
14091 | PSA 13:5 | abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,” kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi. |
15090 | PSA 73:15 | Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka. |
15515 | PSA 94:18 | Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni. |
16318 | PSA 139:11 | In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,” |
16553 | PRO 3:28 | Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu. |
16649 | PRO 7:4 | Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka; |
17121 | PRO 23:7 | gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai. |
17161 | PRO 24:12 | In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba? |
17190 | PRO 25:7 | gara ya ce maka, “Ka hauro nan,” da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami. Abin da ka gani da idanunka |
17522 | ECC 7:23 | Dukan waɗannan na gwada su ta wurin hikima na kuma ce, “Na ƙudurta in zama mai hikima,” amma abin ya fi ƙarfina. |
17594 | ECC 12:1 | Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin lokacin wahala ta zo shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu,” |
18020 | ISA 14:22 | “Zan yi gāba da su,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta, ’ya’yanta da zuriyarta,” in ji Ubangiji. |
18021 | ISA 14:23 | “Zan mai da ita wuri domin mujiyoyi da kuma fadama; zan share ta da tsintsiyar hallaka,” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa. |
18078 | ISA 19:4 | Zan ba da Masarawa ga ikon azzalumi shugaba, mugun sarki kuma zai yi mulki a kansu,” in ji mai girma, Ubangiji Maɗaukaki. |
18136 | ISA 22:14 | Ubangiji Maɗaukaki ya bayyana wannan a kunnena cewa, “Har ranar mutuwarka ba za a yi kafarar wannan zunubi ba,” in ji mai girma Ubangiji Maɗaukaki. |
18274 | ISA 29:11 | Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.” |
18275 | ISA 29:12 | Ko kuwa in kun ba da littafin ga wani wanda ba zai iya karantawa ba, kuka kuma ce, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ban iya karatu ba.” |
18288 | ISA 30:1 | “Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,” in ji Ubangiji, “ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba, suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba, suna jibga zunubi a kan zunubi; |
18329 | ISA 31:9 | Kagararsu za tă fāɗi saboda razana; da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,” in ji Ubangiji, wanda wutarsa tana a Sihiyona, wanda matoyarsa tana a Urushalima. |
18359 | ISA 33:10 | “Yanzu zan tashi,” in ji Ubangiji. “Yanzu ne za a ɗaukaka ni; yanzu za a ɗaga ni sama. |
18456 | ISA 37:34 | Ta hanyar da ya zo da ita zai koma; ba zai shiga wannan birni ba,” in ji Ubangiji. |
18535 | ISA 41:14 | Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi, ya ƙaramin Isra’ila, gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji, Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. |
18542 | ISA 41:21 | “Ka gabatar da damuwarka,” in ji Ubangiji. “Ka kawo gardandaminka,” in ji Sarki na Yaƙub. |
18585 | ISA 43:10 | “Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “bawana kuma wanda na zaɓa, saboda ka sani ka kuma gaskata ni ka kuma fahimci cewa ni ne shi. Kafin ni babu allahn da aka siffanta, ba kuwa za a yi wani a bayana ba. |
18587 | ISA 43:12 | Na bayyana na ceci na kuma furta, Ni ne, ba wani baƙon allah a cikinku. Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “cewa ni ne Allah. |
18631 | ISA 44:28 | wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’ |
18724 | ISA 49:18 | Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye; dukan ’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki. Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “Za ki yafa su duka kamar kayan ado; za ki yi ado da su, kamar amarya. |
18794 | ISA 54:1 | “Ki rera, ya ke bakararriya, ke da ba ki taɓa haihuwa ba; ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki, ke da ba ki taɓa naƙuda ba; domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,” in ji Ubangiji. |
18799 | ISA 54:6 | Ubangiji zai kira sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta, macen da ta yi aure a ƙuruciya, sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki. |
18801 | ISA 54:8 | Cikin fushi mai zafi na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci, amma da madawwamin alheri zan ji tausayinki,” in ji Ubangiji Mai Fansarki. |
18803 | ISA 54:10 | Ko da duwatsu za su girgiza a kuma tumɓuke tuddai, duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,” in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki. |
18810 | ISA 54:17 | ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara, za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki. Wannan ne gādon bayin Ubangiji, kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,” in ji Ubangiji. |
18818 | ISA 55:8 | “Gama tunanina ba tunaninku ba ne, yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,” in ji Ubangiji. |
18854 | ISA 57:19 | ina ƙirƙiro yabo a leɓunan masu makoki a Isra’ila. Salama, salama, ga waɗanda suke nesa da kuma kusa,” in ji Ubangiji. “Zan kuma warkar da su.” |
18856 | ISA 57:21 | “Babu salama ga mugaye,” in ji Allahna. |
18890 | ISA 59:20 | “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji. |
18891 | ISA 59:21 | “Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji. |
18973 | ISA 65:7 | saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,” in ji Ubangiji. “Gama sun ƙone turare a kan duwatsu suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai, zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.” |
18991 | ISA 65:25 | Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi, amma ƙura ce za tă zama abincin maciji. Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna a kan dukan dutsena mai tsarki ba,” in ji Ubangiji. |
19008 | ISA 66:17 | “Waɗanda suka tsarkake suka kuma tsabtacce kansu don su je lambu, suna bin wannan da yake tsakiya waɗannan da suke cin naman aladu da ɓeraye da waɗansu abubuwan banƙyama, za su sadu da ƙarshensu tare,” in ji Ubangiji. |
19011 | ISA 66:20 | Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore. |
19012 | ISA 66:21 | Zan kuwa zaɓa waɗansunsu kuma su zama firistoci da Lawiyawa,” in ji Ubangiji. |
19013 | ISA 66:22 | “Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata. |
19014 | ISA 66:23 | Daga wannan sabon wata zuwa wancan, kuma daga wannan Asabbaci zuwa wancan, dukan mutane za su zo su rusuna a gabana,” in ji Ubangiji. |
19023 | JER 1:8 | Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka,” in ji Ubangiji. |
19030 | JER 1:15 | Ina shirin kiran dukan mutanen masarautar arewanci,” in ji Ubangiji. “Sarakunansu za su zo su kafa kursiyoyinsu a mashigin ƙofofin Urushalima; za su zo su kewaye dukan katangarta su kewaye dukan garuruwan Yahuda. |
19034 | JER 1:19 | Za su yi yaƙi da kai amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, zan kuma kiyaye ka,” in ji Ubangiji. |
19043 | JER 2:9 | “Saboda haka ina sāke tuhumarku,” in ji Ubangiji. “Zan kuma tuhumi ’ya’ya ’ya’yanku. |
19046 | JER 2:12 | Ku girgiza saboda wannan, ya sammai, ku kuma razana don tsoro mai girma,” in ji Ubangiji. |
19053 | JER 2:19 | Muguntarka za tă hukunta ka; jan bayanka zai tsawata maka. Sai ka lura ka kuma gane yaya mugu da kuma ɗaci suke a gare ka sa’ad da ka rabu da Ubangiji Allahnka kuma ba ka tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. |
19056 | JER 2:22 | Ko da yake ka wanke kanka da sabulu ka yi amfani da sabulu mai yawa, duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. |
19063 | JER 2:29 | “Me ya sa kuke tuhumana? Dukanku kun yi mini tawaye,” in ji Ubangiji. |
19081 | JER 3:10 | Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji. |
19085 | JER 3:14 | “Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. |
19087 | JER 3:16 | A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. |
19097 | JER 4:1 | “In za ka komo, ya Isra’ila, ka komo gare ni,” in ji Ubangiji. “In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana ba ka ƙara karkace ba, |
19105 | JER 4:9 | “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “sarki da shugabanni za su fid da zuciya, firistoci za su razana, annabawa kuma za su yi mamaki.” |
19145 | JER 5:18 | “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. |
19170 | JER 6:12 | Za a ba da gidajensu ga waɗansu, tare da gonakinsu da matansu, sa’ad da na miƙa hannuna gāba da waɗanda suke zama a ƙasar,” in ji Ubangiji. |
19173 | JER 6:15 | Suna jin kunyar halinsu na banƙyama? A’a, ba sa jin kunya sam; ba su ma san yadda za su soke kai ba. Saboda haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za a hamɓarar da su sa’ad da na hukunta su,” in ji Ubangiji. |
19198 | JER 7:10 | sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama? |
19230 | JER 8:8 | “ ‘Yaya za ku ce, “Muna da hikima, gama muna da dokar Ubangiji,” alhali alƙalamin ƙarya na magatakarda ya yi ƙarya? |
19233 | JER 8:11 | Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, “Lafiya, Lafiya,” alhali kuwa ba lafiya. |
19239 | JER 8:17 | “Duba, zan aika macizai masu dafi a cikinku, kāsā, waɗanda ba su da maƙari, za su kuwa sassare ku,” in ji Ubangiji. |